Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 72

Chapter 72

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fara ji kafin idanunta su sauka akan Jikamshi. Shadda ce ruwan kasa a jikinsa ga hula tayi masa kyau. Ganinsa tayi kamar an kara masa girma, ya gyara sajensa da gashin baki. Shima din ita yake kallo sai da suka hada ido tayi saurin sauke kanta a kunyace. Ko kadan bata yi tsammanin ganinsa a gidansu ba. Balle da taji shiru bai amsa sakonninta ta hanyar waya ko text ba. Dan gyaran murya taji sannan aka ce "muna kusa fa" ta kalli wurin da sautin ya fito. Subhanallah... Umma, Hajjo da Ismail ne zaune a wurin. Daburcewa tayi gabadaya tace "uhmm sauri nake banyi sallar magariba ba." Bata jira amsar kowa ba ta shige ciki gabanta na tsananta bugu. Tana jiyo dariyar Ismail din yana tsokanar yayansa. ***** Bandaki ta fada ta watsa ruwa da sauri tayi alwala. Sai da tayi sallah sannan ta koma gaban madubi ta shafa mai da gyara fuska. Ba kwalliya ta tsananta ba amma tayi kyau. Ta rasa kayan da zata saka kada su Umma suce kwalliya tayi saboda ganin Jikamshi. Sannan kuma bata son mayar da na jikinta don a gaskiya tayi suyar nama dasu. Karshe wata jallabiya ta dauko baka mai adon duwatsu pink. Tana son rigar sosai, Anti Bintu ce ta siya mata da taje Zaria. Mayafin rigar tasa tayi nadi sannan ta sami wuri ta zauna tana tunanin yadda zatayi ta fita. Umma da kanta ta shigo ta danyi murmushi ganin Asmau na kallon kasa. Allah mai iko, sai Ya sanya musu son juna duk da lalaurar dake tattare da kowanensu. Wannan ma kadai ya ishi bawa aya. "Asmau kije ku gaisa mana kin barmu da baki kuma kinsan naki ne" A kunyace tace "ni bansan zasu zo ba." "Bari na sallame su to. Ina jin gaishemu suka zo gara su tafi tunda mun gaisa." Dago kai tayi da sauri amma bata ce komai ba. Umma tayi murmushi kawai ta godewa Allah. Cikin ikonSa 'yarta ta sami farinciki a rayuwarta. "Gulma to tashi kada waccan akun ta cika su da surutu" Sai da Asmau ta jira Umma ta bar dakin sannan ta fito falon. Da sallama ta shiga. Ai kuwa Amatullah ta gani tana ta zuba zance tana bawa Ismail labari yana biye mata suna dariya. Hajjo kuma da Jikamshi suke tasu hirar. Tana shiga Ismail yace "yauwa ga amaryar tamu. Hajjo ke fa an sallameki. Daga yanzu duk abinda zaki fada ba ganewa zaiyi ba" Wayyo Allah, ji tayi kamar ta juya da gudu. Ismail na tsokanarta shi kuma gogan ya wani zubo mata idanu yana kallonta yana lumshe ido kamar mai jin bacci. "Babu inda zani, ni har akwai masu nuna min soyayya ne. Allah Ya jikan Malam amma muma a zamaninmu fa ba'a cewa komai" Ismail yace "Allah Hajjo?" "Hmmm kaidai bari dannan." Ta fada tana jinjina kai. Yau fa tunda ta tuno Malam to wanda bai sanshi ba zai sha labari. Allah Sarki Malam Yahya. Hajjo baki shi kuma shiru shiru. Shiyasa akayi zaman lafiya duk da rigimarta. Daurewa Asmau tayi ta gaishe su. Ismail ne kawai ya amsa, Jikamshi tashi yayi yana dubanta. "Muje na baki amsa ko" Hajjo tace "'yan nema kuyi a gabana mana." Da muryarar nan tasa me sa Asmau jin tafi kowa dace yace "ga Ismail nan ya fini iya hira da tsofaffi. Ni ga tawa nan." Ya nuna Asmau. Amatullah ta taso tana kumburi "Babana kace fa yau da ni zaka yi wasa banda Ummi" "Duk yau taki ce. Yanzu ma sako zan bata kinji princess. Zauna a wurin sabon Baba kafin na dawo" Asmau na kallonsa ya fita. Ismail yayi mata alama da hannu tabi bayansa. Sai da tayi dariya a hankali sannan ta fita. Hajjo tace "oh, yaran zamani baku da ta ido. Wannan yayan naka Sama'ila yana wani mici mici da ido sai kafirin iya saye zuciya." Ismail sai dariya "ko dai za'a koma da ne ki zabe shi ki bar Malam" "A'a fa, Malam yafi kowa. Wannan alakoro ne Asmau ta samu. Ni kuwa nawa shine gangariya" ***** Wurin motar Ismail da suka zo da ita ya kaita. Barin dreba ya bude ya nuna mata kujerar yace "zauna" Zata tambaye shi ina zai zauna ta ga ya tafi hanyar kofa inda wasu kujerun roba suke farare ya dauko daya. Sai a lokacin ta zauna kafafunta a waje shi kuma ya dasa kujerar daga gabanta ya zauna kafarsa daya kan daya. Ji tayi kamar wadda aka rufe a cikin keji duk ya cike wurin. Ta kasa kwakkwaran motsi. Wayarsa taga ya dan turo gabanta ta karanta abinda ke rubuce a ciki. Text dinta ne na biyun da ta tura masa kafin su iso gida. "Ina sonki Matar Jikamshi, don Allah kada kiyi kuka. Hawayenki yana da tsada. Ba a gaban kowa zaki zubar dashi ba. Amsar ta gamsar dake ko na kara wata?" Murmushin da yake so daga gareta take yi amma ta kasa dago kanta. Kunyarsa ke karuwa sosai a zuciyarta. Ga wani nishadi da take ji kamshin turaren Jikamshinta ya baibaye wurin gabadaya. Dama yasan irin wannan kalamai sai a text. Tana ganinsa take komawa bebiya. Ranakun da take ajiye kunyarta kuwa sai taga alamun zata rasa shi ne. "Dago kanki na baki amsar sakonki na farko. Shine babban dalilin zuwana" Dan kadan ta iya daga kan tana sauraronsa. "Matar Jikamshi Allah Yayi miki albarka. Bani da wata kalma da zan iya nuna miki matsayinki a zuciyata. Sakonki ya shigo a lokacin da komai ya rikice min. Haduwata dake zuwa yau hadi ne daga Allah. Har abada nasan cewa kinyi min abinda mata da yawa bazasu yi ba. Ni kuma saboda son kai na amince maimakon na dage na rabu dake ki auri wanda zaki haihu dashi..." Bude baki tayi zata yi magana ya sanya yatsansa a saman lebensa "shhhh, kada kiyi magana. Text dinki yace komai. Ki barni nima na fadi nawa. Banyi miki alkawarin cewa idan munyi aure shikenan duk wani bacin rai da damuwar da kike dasu zasu kau dari bisa dari ba. Amma Matar Jikamshi zanyi kokari naga na kare hakkinki kuma na kyautata rayuwarki har karshen rayuwata. Abinda kike gudu tun farkon da na gabatar miki da soyayyata bance bazai taba faruwa ba. Kowane mutum yana da damar fadin son ransa duk da kiyaye bakin shi yafi akan fadar magana mara alkhairi. Ki sani a dangina ko naki, makota ko abokan arziki dole watarana sai anyi miki gori a gabanki ko bayan idonki wannan bani da haufi akansa. To ina so duk lokacin da aka fada miki maganar da ta shafi rayuwarki ta baya kuma bana wurin bare na kare miki ki sani cewa Ishaq yana son Asmau. Ki sakawa ranki akwai wanda zaki zo kiyi kuka a gabansa ya rarrasheki, akwai wanda yake kaunarki saboda Allah yake fatan kasancewa abokin rayuwarki har a aljannah." Ba sai na fada ba Asmau kuka take yi sosai saboda yadda kalaman Jikamshi ke ratsata. Shi kanshi a raunane yake idan ya tuna cewa duk su biyun suna da abin fada a rayuwarsu. "Abu na karshe Matar Jikamshi ina so don Allah kiyi hakurin zama dani. A duk lokacin da kika ji anyi haihuwa zuciyarki ta kwadaitu da son ina ma kece maijegon to ki

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});