Chapter 74
Chapter 74
wanda Allah SWT Ya umarcemu da mu nisanta kawunanmu da ita. Allah Ya kara shige mana gaba. ***** Bayan sati biyu kamar yadda suka yi alkawari kawunnan Col. Ishaq suka zo daga Jikamshi. Haj Lubabatu ta shirya musu tarba mai kyau sai da suka ci suka koshi sannan sauran kannensa maza suka yi musu jagora zuwa gidan Umma. A nan din ma tun safe ake shirin zuwan nasu. 'Yan uwa da abokan arziki sun taro. Alh Adamu ma da tasa gayyar duk don a taru a rufawa juna asiri. Baki kam sun ga karamci kuma sun yaba. Matsalar dai itace haihuwar Asmau kafin aure. Amma tunda dan nasu yace yaji ya gani dole su bi yarima su sha kida. Dubu dari suka bada wanda yasa su Baba nuna a rage. Wani cikinsu dan tsoho yace ko kwandala bazasu rage ba. Dansu yace lallai abinda zaa bayar kenan ko sama da haka. Kawu Garzali sai murna yake. Allah Yayi Asmau zatayi aure kuma zata auri wanda yake matukar sonta. Adduarsu Allah Yasa soyayyar ta zarce har gidan aure. Taro ya tashi cikin mutunta juna aka yi sallama suka tafi. ***** Asmau kuwa da wuri ta fita amma ta bar Amatullah a gida. Hankalinta a kwance wannan karon kana ganinta zaka san amarya ce mai murna da dokin lokacin aurenta. Da kwatance saboda sababbin gine gine ta isa gidansu Walida tsohuwar aminiyarta. Har kofar gidan adaidaita ya kawota. Tana sauka a kofar gidan Walida ta fito daga makotansu. Hada ido suka yi sai suka tsaya kallon kallo kowacce tana zubar da hawaye. Duk su biyun abubuwa da dama suke tunawa wanda suka wargaza musu rayuwa. Asmau ce ta fara yunkurawa kafin ta karasa itama Walida ta taho cikin sauri suka rungume juna. A bakin kofar gidan suka fashe da kuka sosai suka rike da juna. Mutane kuwa sai kallonsu suke yi. Sai da suka dan nutsu Walida ta ja hannunta suka shiga ciki. Antin Walida matar babansu na zaune tana yankan farce suka shigo. Murna ganin juna suke sosai. A firgice ta tashi tana nuna Asmau. "Wa nake gani kamar Asmau?" Walida tace "ita ce Anti" Ta karewa Asmau kallo sannan ta tabe baki "to ina abinda kika haifa. Ai na jima da jin labarin kin dawo Kano da dane ko 'ya ni ban rike ba. An gama yawon ta zubar an dawo gida." Murmushi Asmau tayi, irin wadannan maganganun 'yan uwa da yawa da Jikamshinta sun fada mata dole ko taki ko taso sai tayi hakuri dasu. Kuma sanin halin Antin na kwarewa wurin rashin mutunci yasa bata dauki abin da zafi ba. Walida ma da a da tasan cewa bata shiru, idan matar nan tayi mata ramawa take suyi ta cacar baki kamar kishiyoyi shiru Asmau taga tayi. Ta kama hannunta suka shiga dakinta. Kan wata kujera suka zauna Walida tace "Ashe rai kan ga rai 'yar uwa? Na fidda rai da sake haduwa dake wallahi" "Kiyi hakuri Walida. Na dan jima da dawowa amma na rasa me zamu cewa juna idan muka hadu. Har ga Allah abinda ya faru dani shekarun baya kika gujeni yasa ban kara nemanki ba" Walida ta share kwalla "ki yafe min Asmau, na cutar dake da na zama sanadiyar koya miki dabi'un da ba naki ba. Ba haka kawai na gujeki ba amma..." Asmau tace "kada ki damu. Yaya Qasim ya fada min kema duk abinda ya faru dake. Mu kuma haka Allah Ya rubutu mana tama jarabawar" da kuka ta karashe maganar. Suka taru su biyu suna yi babu mai rarrashi. Asmau na tuna rasuwar Abubakar da cikin da aka gane tare da ita a ranar da ya rasu. Ita kuma Walida tana tuno ranar da mahaifinta ya kamata da saurayi ya zura hannuwansa cikin rigarta. Wa'iyazu billah wadannan 'yan mata bazasu manta da sharrin social media ba. Da suka gama kukan ne suka bawa juna labarin irin gwagwarmayar da suka sha. Walida tayi murna da jin zancen auren Asmau sannan tayi ta kallon hotunan Amatullah a waya tana mita ba'a zo mata da ita ba. Itama ta bawa Asmau labarin irin takunkunmin da babanta ya saka mata saboda jin labarin cikin Asmau. Karshe ma ko karatun jami'ar bai bari ta kammala ba yace sai tayi aure. To gashi shekaru shida babu auren babu karatun sai zaman gida da zuwa islamiyya. Matar gidan ta sami yadda take so wurin fadawa Walida maganganu sai dai ta dena ramawa saboda yanzu babanta bai damu da lamarinta ba. Indai ba aure tayi ba shi baiga amfaninta ba. A wannan zaman gidan kannenta biyu 'ya'yan Anti sunyi aure har sun haihu. Bata yawo daga islamiyya sai gida sai kuma abinda ya zama dole. Samari kuwa kamar anyi ruwa an dauke. Babu mai zuwa yanzu. Asmau tace "dukkanmu munga irin abinda ake gudu a waya da social media. Allah kara rufa mana asiri duniya da lahira." "Amin Asmau, amma ai kinfini ganin tashin hankali. Kullum ina miki addua Allah Yasa kada rayuwarki ta lalace da kika bar gida. Da farko a social media na fara watsa hotunanki cigiya kafin Baba ya karbe wayar. Rabona da wayar arziki na manta" Yini suka yi suna hira sai bayan laasar lokacin da Asmau ta tabbatar an gama taron gidansu tayi haramar tafiya. Jikamshi yayi mata waya yace to ta fara shiri sauran kadan fa ta karasa zama matarsa yana fatan za tayi shiri mai kyau kafin zuwan lokacin. Yaso zuwa daukarta ma da kansa amma kamar yadda suka faro da bin komai yadda ya kamata sai ya hakura. Wani lokacin ko babu social media idan budurwa da saurayi suka kebe su kadai a mota sanyin AC yana dan ratsasu sai shaidan ya fara kawo musu hari. Ko kadan babu burgewa kice wai duk inda zaki saurayinki shine yake kaiki ya dauko ki. Ki duba da kyau kiyiwa kanki adalci watarana ko dan yaya sai anyi abinda bai dace ba ko da kuwa taba hannu ne. Yau da gobe ai tafi karfin wasa. ****** A cikin wata daya Col. Ishaq ya dage sosai ana ta gyaran gidansa. Duk inda yake bukatar canji kamar kayan cikin toilet irinsu baho da sink an canza an saka komai sabo. Haka ma a kitchen da su kofa. Ga fenti sai da ya kira Asmau ta fadi irin kalar da take so. A bangarensu ma Umma ta tashi tsaye sosai. Daga Asmau yanzu babu kowa a gabanta sai Yassar. Su Shemau ne suka je suka gano gidan aka zo aka fara siyayya. Dole ita ma ta dage ta fito da 'yarta ta. Gado ma ready made ta siya guda biyu tare da sauran kayan gida. Shemau, Jafar, Kawu Garzali da gidan Mama duk ba'a barsu a baya ba. Kowa akwai abinda ya dauki nauyi don ganin cewa Asmau ta sami nutsuwa a rayuwarta. Ita kam sai son barka da yi musu addua. Saura kwanaki biyar su tafi Zaria bikin Dijah. Umma da Anti Bintu basa zama kullum sai an fita siyayya saboda ana gama na Dijah da sati hudu za'ayi na Asmau. Jikamshi yazo yiwa Asmau sallama tafiya ta kamashi Warri zaiyi sati uku. Zaune yake ya dora hannuwansa akan cinyarsa sannan ya tallabi fuskarsa dasu yana kallon Asmau. Kallon ya takurata tace "Jikamshina zan tashi fa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103