Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 102

Chapter 102

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

don tasan akwai wurin sati uku kafin lokacin haihuwarta. Cikin dare suna bacci taji ciwon ba mai daukewa bane ta tashi ta fita a hankali. Ita kadai take ta kai kawo a falo ciwo yana ta gaba gaba har taji tafiya tana neman gagararta. Da jan kafa ta dawo dakin ta zauna a bakin gado. Sai da ta zauna ta fara cewa "Jikamshina" ta kira sau uku yana baccinsa. Wani ciwo taji sosai bata san lokacin da tace "ISHAQ" da karfi ba. Tashi yayi ya rasa daga ina take kiransa. Ciwo yayi ciwo ta sake cewa Ishaq, fitila ya kunna ya ganta a bakin gado sai gumi take. Ya rude sosai yace me kike yi a nan. Tambayar ma haushi ta bata ta cije dai tace "nakuda nake" Rigarsa ya nema ya saka ya fara neman mukullin mota. Ciwo na cinta tace "Jikamshina bazan iya tashi ba. Haihuwar ta matso. Ka dauko sabuwar reza a waccan drawer din" Ya zaro idanu a tsorace "inyi me da reza?" Tana wash wash tace "yanke cibiya" A take jikinsa ya fara rawa. "Kiyi hakuri na kaiki asibiti don Allah kada ki haihu a gabana wallahi bazan iya gani ba suma zanyi. Ko ta awaki bana son gani" yadda yake maganar kasan a tsorace yake sosai. Durkushe yake a gabanta ta daure ta rike masa hannu "Jikamshina kafin muje asibiti ko wani yazo zan iya haihuwa. Ka daure ka duba min ko baka son baby din" Jikinsa a sanyaye yace "ina so" Wani nishin ciwon ta gama sannan tace ya dauko rezar. Yaje ya dauko ya dawo gabanta ya zauna tare da mike kafafu. Yana zama yaga ruwa yana fito mata ya dago kai a razane. "Ruwan jikinki zai kare don Allah ki bari na kira ko Hussaini ne" Jin bata amsa ba ya dan dago "Asmau kina jina" Idonta a rufe ta gyada kai "faya ce ta fashe kada ka damu" Yana kallon yadda take famam cije lebe tausayinta ya kama shi. Babu inda baya rawa a jikinsa idonsa a rufe yake ya fito da reza sai kyalli take amma bai san me ma zaiyi da ita ba. Sai da tace ya bude idonsa ya rinka gani ta kusa haihuwa. Budewar yayi ya juya gefe tare da rike mata kafa yana ta faman cewa "push Matar Jikamshi, push, yauwa gashi nan kin kusa ko? Push, push nasan zaki iya" Ji tayi kamar ta haure shi da kafarta don takaici. Wai push ga uban ciwo gashi ya kasa yi mata abin kirki. Sake cewa push yayi ta ce cikin bacin rai "Idan ka sake cewa push wallahi zan haureka" "Au toh, bansan ba'a fada ba. Naji haka akeyi a tv. Yanzu me kike so?" Gumin fuskarta ya goge mata sannan tace "addua zaka rinka yi min kuma *ka bude ido ka kalli yadda baby zai fito* kada a sami matsala" Ya rinka gyada kai tana magana. Ita ke fama da ciwon kuma ita ke fada masa yadda zaiyi. Daga lokacin addua ya rinka karanto mata itama tana yi. Can yaji ta fara nishi ya sake cewa push ai kuwa ta kai masa hauri da kafa. Ji tayi ta tsani kalmar gabadaya. Yana kallo kan baby ya fara fitowa sai ji tayi ya fara kiran sallah. A yanayin da take ciki babu halin dariya. Da yaga abin na gaske ne yace "na shiga uku in hade miki kafarki kada kiji ciwo." "Kashemu zakayi ne? Ka tara hannu kada ya fado a kasa" Ta fada da kyar. Yace "toh, ita rezar ina zan yanka miki?" Tunani tayi kada yayi mata karin da bata shirya masa ba tace "ajiyeta a gefe tukunna" wai tana wannan yanayin yake damunta haka. Ya ajiye ya mika hannu ya cigaba da kiran sallah tana nishi har Allah Ya taimaketa baby ya fito tare da mahaifa sai kukansa taji. Da jinin da komai Col. Ishaq ya rungume dansa yana hawayen farinciki. Asmau nuna masa yadda zai yanke cibiya sannan ta mayar da kai ta dan kwanta tana mayar da numfashi. Da dan rungume a jikinsa ya zagayo ya rungumeta sunyi kace kace dasu. "Allah Yayi miki albarka Asmau. Allah Ya sakawa iyayenmu da alkhairi" Baby din ya bata yana ta canyara kuka ya dauki wayarsa lokacin biyar da rabi ya kira Hajiyarsa. Cikin bacci ta farka ganin mai wayar ta tashi a gigice. Tana dauka ta jiyo kukan jariri. Col. Ishaq yace "Hajiya mun haihu" Bakinta ya kasa rufuwa don murna tace "kun haihu ko ta haihu" Yana ta murmushi yana kallon Asmau da dansu yace "wallahi tare muka yi komai muna gida. Saura wankan ne ban iya ba" Hajiya ko tambayar me aka haifa bata yi ba ta tashi cikin sauri ta tafi dakin Bilkisu ta tayar da ita tace ta kira mata Dahiru shine gidansa yafi kusa da nata yazo ya kaita gidansu Asmau. Da yazo suna hanya tana addua Allah Yasa haihuwar babu matsala. Ai kuwa sun sha kallo don da dansa a kafada yazo ya bude musu kofa lokacin an fara kiran asuba. Hajiya tayi saurin karbar baby din tace maza yaje yayi wanka. Ko da ta shiga kitchen ya dora ruwa a manyan tukwane biyu akan gas cooker. Wurin da Asmau ta haihu ya gyara shi tas ya dauke kafet din ya fito dashi waje. Hajiya ta yaba masa duk da bata fada ba. Asmau ta gani tana dauko robar wankan baby. Tana jin muryar Hajiya kunya ta kamata. Hajiya tace Bilkisu ta juyo mata ruwan tayi wanka ita kuma zata yiwa baby. Anjima kuma da kanta zata yiwa maijego. Kafin takwas na safe Asmau maijego da jaririnta sunyi fes. Col. Ishaq kuwa baki har kunne. Tare da Hajiya suka je asibiti aka yi mata allurai aka basu magani suka dawo gida. Lokacin su Umma suka zo gida ya cika da yan uwa. Col. Ishaq shima jegon yake don kuwa daki ya shige yana baccin gajiya saboda irin aikin karbar haihuwa da yayi. Shi da 'yan uwansa sun nunawa Asmau gata sosai. Amatullah an dawo gida sai murna tayi kani. Kayan barka lodi guda su Mami suka kai gidansu Asmau. Ranar suna aka shirya walima gagaruma aka ci aka sha yaro yaci suna Abdallah. Su Zulaiha, Rashida, Zubaida, Walida da Ma'u matar Qasim sun sha hidima. Daren ranar Asmau tayi wanka ta fito ta sami su Ainau suna ta hade mata kayan barkan da ta samu. Hawaye ne ya ciko mata Shemau tace " zaki fara ko." "Amatullah nake tunani, lokacin da na haifeta babu mai kaunarta. Ita nata uban ma bai san da ita ba har ya koma ga Allah. Ko pant bata dashi sai da Allah Ya hadamu da Zulaiha ta bata kayan Ali. Bazan taba mantawa da bambancin dan zina da dan aure ba. Allah Ya yafe mana" sai kuka yaci karfinta. Su Shemau sunji tausayinsa suka rinka bata baki. Washegari Col. Ishaw yace tazo ta ga wani abu a waje. Mota ce mai kyau ya siya mata. Bata san lokacin da ta rungumeshi a wurin ba don murna. ***** Duk abinda miji zaiyiwa mata Col. Ishaq yana wadata Asmau dashi. Ta bangaren yara kuwa duk yadda yake matukar son Abdallah hakan bai hana shi cigaba da nuna tsantsar kulawa ga Amatullah ba. Asmau

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});