Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 63

Chapter 63

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ishaq ya kara murmusawa "to ai babu damuwa Mami ga kannenki nan sai kibi daya daga cikinsu ki kwana a gidansa" Mami ta saki baki don batayi tunanin haka zai ce ba. Tayi zaton zaije ya bawa Hajiya hakuri. Duk sun san bacin ranta yafi karfi akan gorin haihuwar da aka yi masa ne. "saboda Allah ya zaayi naje gidan kannena na kwana da girmana" "To bari mu dawo daga masallaci sai na baki key din gidana. Babu datti sosai saboda karshen sati maigadi yana min shara. Sai ki tafi da taki 'yar Bilkisu ta tayaki kwana" yana gama magana yayi gaba kamar bashi ya fada ba. Sun san sun tabo soja yau sai yadda ta yiwu kuma. Bayan fitarsu masallaci Mami da Safiyya suka zauna suna ta magana akan lamarin auren Asmau da kuma karin laifin da Ismail ya janyo musu. Bilkisu dai shiryawa tayi a daki ta fito ta zauna jiran zuwa asibiti don tasan dole aje da ita tunda mai aikinsu bata nan. Tare suka dawo daga masallacin su Dahiru suna ta bashi hakuri ya nuna musu komai ya wuce. Wurin Hajiya ya je ta shirya ita ma tace motarsa zata shiga su tafi. Suka fito falo Bilkisu tabi bayansu suma sauran suka fito. Bilkisu na gaban motarsa Hajiya a baya Safiyya tazo ta kama daya kofar zata bude ya juyo ya watsa mata harara ba shiri ta saki kofar. "Ki koma kibi motar 'yan uwanki masu haihuwa. Ni Hajiya zan dauka da 'yata." Tayi saroro tana kallonsa. Dahiru da yaji ya dan matso wurin motar "Yaya don Allah kayi hakuri ka manta da zancen nan. Kuma ka yarda ta biku ko Mami ta shigo. Kaga sai ayi saving din mai mu tafi da mota biyu" Col. Ishaq ya wani kankance ido ya kalli Bilkisu "toshe kunnenki kinji mai gadon zinare" ta kuwa tura yatsu a kunne tare da sunkuyar da kanta. Hajiya tasan karshenta wata maganar mara dadi zai yabawa kaninsa tace "a gaban 'yarku zaku nuna min hali ko, kai kuma Dahiru kusan yadda zakuyi ku taho" Col. Ishaq ya mayar da kansa ciki albarkacin Hajiya suka ci. Dole mota biyu suka yi don daya zata matsesu saboda Dahiru da Safiyya duk akwai jiki. Yana soma tuki Hajiya tace "kai" "Naam" "Kayi hakuri da abinda suka yi maka don Allah kada kuyi min gaba. Aure kuma da kaina zan sami kakar Asmau muyi magana in sha Allahu. Tun farko na fada maka dole zaka fuskanci kalubale ta ko'ina saboda wannan abu fa ba wanda ake iya saurin kawar da kai bane a kansa. Ni dai ina sonta kuma na baka goyon baya ka nemi aurenta. Allah mai yawan gafara ne da jinkai. Idan bama iya kawar da kai ga kuskuren mutane to bamu san da wane laifi mu kuma Allah zai kamamu ba" Allah Sarki Hajuyarsa akwai zurfin tunani. "Hajiya nagode sosai amma ki bar maganar auren. Asmau bata cancanci ta kare rayuwarta bata haihuwa ba. Nima daga yanzu bana fatan kara neman aure. Mu bari kawai tabi shawarar iyayenta a zauna lafiya." Sosai Haj Lubabatu taji tausayin Ishaq. Duk sallah bata fasa yi masa adduar samun rabo saboda yadda yake son yara. Da suna kanana har goya masa kannensa tana yi saboda yadda yake mata nacin zaiyi raino. Sai ayi goyon ya zauna a falo ko baki tayi baya jin kunya. "Dole kayi aure shine cikar dan Adam. Kayi addua kamar yadda nake maka. Allah Ya kawo maka mace tagari" ya amsa da amin amma ba don yana tunanin zai kara son wata bayan Asmau ba. Shi fa bashi da raayin auren da babu soyayya. Kuma soyayyarsa ta kare a wurin Matar Jikamshi. Ya kai hannu kan giya zai canja yaji Bilkisu ta dora nata a saman nasa ta kankame. Ya dan kalleta ya kula kuka take yi a hankali. Yace "nine ko, nasa Maminki kuka" Muryarta na rawa tace "a'a Uncle don Allah kada kaki auren Ummin Amatullah" Murmushi kawai yayi yana kwanar shiga asibitin motar Musaddiq tana bayansa. "Allah Yayi miki albarka kinji. Ki cire duk abinda kika ji dazu daga ranki.... Wai ma wa ya koya miki labe? Bari mu dawo yau sai kinyi tsallen kwado" Da guntun hawayenta tayi murmushi. Hajiya ma murmushin tayi. Taji dadi da fushinsa bai shafi 'ya'ya ba. Boot dinsa ya bude ya fito da ledoji biyu cike da tarkacen kayan kwadayi na yara sai katon din ziza. Yana tasowa daga office ya siyo kafin ya wuce gida. Bilkisu tazo taya shi dauka sai ga su Ismail da sauri kowa ya dauki abu daya cikin su mazan. Ya kawar da kansa gefe don yasan suna neman shiri ne. Abinda bazasu samu kenan a nan kusa ba. ***** Shi da Hajiya ne a gaba sai Bilkisu da ta jero tare da Mami da Safiyya tana tambayar Mamin kannenta. Sun kusa zuwa dakin suka ga wata mace ta fito daga wani daki da hijab dinta har gwiwa tana kuka. Col. Ishaq bai san lokacin da ya isa gabanta ba da sauri ba hankali a tashe yace "Matar Jikamshi menene?" Asmau kuka take yi kawai "Amatullah ce ta sake samun attack. Likita zan kira" Shima a rude yake yace "koma wurinta bari na kira likitan" Kasa komawa dakin tayi tabi bayanshi da gudu tana ta zubar da hawaye. Duk sunji tausayin Asmau da yadda ta gigice. Dakin da suka ga ta fito Hajiya tace "mu shiga mu jirasu" Mami ta bude kofar suka shiga da sallama. Mama Yalwa ce a tsaye kan Amatullah tana ta kakari. Safiyya na jin yadda take kakarin ta matsa kusa da gadon da sauri tace "wannan ba attack din asthma bane. Ba kuji yadda take numfashin ba, majina ce a kirjinta" Mama Yalwa tana jin haka ta saka bakinta a hancin Amatullah ko kyama babu ta rinka zuke mata tana tofarwa. Tana kaunar Safina fiye da sauran jikokinta sosai saboda yarinya ce mai tattare da tabo mai muni a rayuwarta. Bayan zina mace aka fi gani da nason zunubin duk da cewa dole idan anyi akwai namijin da suka yi tare. To amma namijin sai ya tsira daga aibatawar mutane saboda shi ba'a ganewa a jikinsa. Idan ya karyata babu yadda za'ayi dashi. Sharrin zuciya ya cutar da Abubakar wanda yayi sanadin cutar da Asmau. Gashi a karshe Safina ita ce abin ya kare a kanta. Mama ta dan share hawayenta sai ga Amatullah ta ware saboda hancinta ya bude. Sai a lokacin suka gaisa dasu Haj Lubabatu. Mama tace "Hajiya duk wadannan yaranki ne? Masha Allah" Hajiya ta dan murmusa "ya mai jikin?" Mama tace " gata nan duk ta ruda mu." Ta kalli Safiyya "nagode miki kinji. Ya sunanki ne?" Safiyya ta fadi sunanta kenan su Asmau suka shigo tare da likita. Ga mamakinsu a zaune Amatullah take ta jingina da pillow. Asmau taji wani sanyi a ranta sannan ta matsa kusa da Amatullah tana mata sannu. Likitan ya dubata ya tabbatar harda mura tayi mata mugun kamu. Magunguna yace zai turo nurse ta kawo musu. Bayan fitar likitan Asmau ta gaishe da su Mami. Cikin su babu sa'anta duk sun girmeta. Sun amsa mata fuskokinsu babu yabo babu fallasa. Col. Ishaq yana tsaye daga wurin kofa. Idonsa kyam akan Asmau har

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});