Chapter 25
Chapter 25
Annabi SAW yayi gaskiya da yace a hadisi na hudu cikin arba'una na Annawawi wanda aka karbo daga Ibn Mas'ud yake cewa .. _......Hakika dayanku zaiyi ta aikata aiki irin na 'yan aljannah har sai ya kasance tsakaninsa da ita bai wuce zira'i ba sai littafinsa ya rinjaye shi sai ya aikata aiki irin na 'yan wuta sai ya shigeta...._ Qasim ya soma hawaye " in sha Allahu bazamu shiga wuta ba. Ka manta Allah Yayi alkawarin yafe zunubin masu tuba.?" Sai da suka sha kukansu sannan Abubakar ya bawa Qasim wayarsa ya karanta wasu cikin sakonnin text da Asmau ta turo masa. _Yaya Abubakar ka dubi girman Allah ka daga wayata. Kada ka gujeni a wannan lokacin_ _Idan ka rabu dani rayuwata bazata kara wani amfani ba. Me zan fadawa duniya nan gaba._ _Kai kadai ne zaka iya taimakona a wannan halin. Ka daure kada ka fasa aurena._ _Na amince ko washegarin aurenmu ne ka sakeni wallahi bazan yi korafi ba. Amma yanzu idan ka kini duk wanda ya aureni zai iya tona min asiri._ Kasa kara karatun Qasim yayi saboda tausayin Asmau da ya kama shi. Sun dauki wasu mintuna babu mai magana sai muryar malamin nan kawai suke ji yana kara tsorata mutane game da aikata zina. Qasim ya tashi tsaye yana kashe kayan wuta na dakin dake kunne "ka tashi mu tafi ka bawa yarinyar nan hakuri sannan mu san yadda zamuyi su Baba su amince a matso da bikin nan zuwa wata biyu tunda kace mai hayar naka har ya gama ginin da wuri." "Kana ganin zasu amince? Wata hudu ya rage da 'yan kwanaki yanzu nace a maido shi baya?" "A nawa ganin hakan ne zai kara kwantarwa Asmau da hankali tasan cewa da gaske bazaka gujeta ba. Wallahi Abubakar ban taba zaton zamu wayi gari mu ga rana irin wannan ba. Ba don da bakinka ka fada min ba Allah bazan taba yarda ba." Rufe dakin suka yi sannan suka fita zuwa motar Abubakar. Qasim ne zai tuka su. A hanya suka sami masallaci sukayi sallar juma'a sannan suka wuce Kano suna ta tattauna yadda zasu bullowa su Baba domin su yarda a dawo da bikin baya. Kafin su rabu sai da Abubakar yasa Qasim yayu masa alkawarin wannan zancen zai zama sirri a garesu har mutuwa. ***** Ko gida Abubakar bai shiga ba yana sauke Qasim ya tashar unguwar kabuga zai wuce Shanono, gidansu Asmau ya wuce kai tsaye. Lokacin Umma na wurin aiki ita kuma tana daki tana sana'ar kuka. Ta gama sawa ranta Abubakar ya gujeta kenan yanzu abinda ya faru matsalarta ce ita kadai. Jafar ne ya buga mata kofar daki ya sanar da ita zuwan Abubakar. A zabure ta tashi ta lulluba mayafi ya rufe mata rabin fuska ta fita ta same shi a wurin da Umma ke ajiye mota. Tana zuwa gabansa bata yi la'ari da cewa wani zai iya ganinsu ba ta zube gwiwoyinta a kasa tana kuka mai sauti. "Don Allah Yaya Abubakar kada kace kazo rabuwa dani. Gara na mutu da in ga ka juya min baya a wannan yanayin." Waigawa yayi ya tabbatar babu mai ganinsu sannan yayi mata alama da ta tashi. Shima hawayen yake shirin yi. "Asmy kiyi hakuri ki yafe min. Naci amanarki na cutar dake. Amma ina so kisan cewa bazan gujeki ba. Wannan tsautsayin ni ne na tilasta miki saboda haka tare zamu fuskance shi. Idan kin amince zanyi magana a gida a dawo da bikinmu nan da wata biyu". Wani hawayen ne ya sakko mata ga dariyar farinciki duk a lokaci daya. "Da gaske? Wallahi na amince. Na yarda. Nagode Yaya Abubakar." "Ki dena yimin godiya. Ni dake duk bamu fi karfin kaddara ba. Kuma kowane bawa akwai irin jarabawarsa a duniya. Dama Annabi SAW yace _Shaidan yana gudu a jikin mutum kamar yadda jini yake yi._ Kinga ashe bamu fi karfin fadawa tarkonsa ba. Sai dai Ubangijinmu mai rahma ne da gafara. Idan muka tuba sai kiga kamar ba'ayi ba." A sanyaye yake maganar ciki da nadama. Daga wannan lokacin suka fara azumi da tashi cikin dare neman gafarar Allah. Yaso samun matsala da su Baba amma daga baya sun amince an matso da auren. Tun daga lokacin Asmau take bashi girma fiye da na da, tsoro take yi kada ta kuskure yace ya fasa asirinta ya tonu. Haka lokaci ya tafi har zuwa bikinsu da abinda ya faru bayan nan. ***** *CIGABAN LABARI* Asmau ta share hawayenta bayan ta gama bawa Zubaida labarinta. Ita ma Zubaidan kukan take yi na tausayi ga bakuwar da kwanansu daya da haduwa amma jininsu ya hadu. "Tabbas kinga tashin hankali a rayuwarki Asmau. To amma abinda ya daure min kai shine yadda kuka tuba amma duk da haka kika tsinci kanki a irin wannan rayuwar". Dan murmushi Asmau tayi "Zubaida kenan, tubanmu ba shi zai hana faruwar kaddarar rayuwarmu ba. Komai da kika gani ya faru ga bawa rubutaccen al'amari ne tun kafin zuwansa duniya. Wani abin yana faruwa ne domin ya zama darasi ga wasu don su kiyaye. Ni bana bakinciki da ikon Allah. Nasan bazai barni na tabe ba albarkar Annabi SAW." Zubaida ta gyada kai ta gamsu da bayanin Asmau. "Allah Ya jikan Abubakar" Asmau tace "Amin " tana share kwalla. ABINDA AKE GUDU🙆🏽20 Batul Mamman💖 Wani mugun fitsari ne ya tashi Asmau daf da kiran assalatu. Ta fito zata je bandaki amma ko ruwan tsarki bata dashi. Haka ta koma daki tana ta matse shi da adduar Zubaida ta fito da wuri ko dan yaya ne ta sammata. Har aka idar da sallah a masallaci Zubaida bata fito ba. Zuwa lokacin Asmau sai gumi take yi tana cilla kafa. A hankali taji ya fara zubowa dole ta tafi bandakin da gudu tayi batare da tayi tsarki ba. Haka ta dawo dakinta ta shafi kura tayi taimama sannan tayi sallar asuba. Batun jin yunwa dama ba'a magana. Wannan yanayin da ta tsinci kanta a ciki hakurinta ya fara karewa. Ace tayi fitsari ko ruwan tsarki babu gashi tana gani amma gidan nafsi nafsi (kowa na ta kansa)kawai ake yi. Yau Zubaida bacci sosai take yi don har tara ta wuce bata farka ba. Asmau ta gaji da jiran tsammami ta duba hijabinta wanda yafi kowanne dauda ta saka ta fita bakin titi. Ga rana ta kwale haka ta daure zuciyarta ta zauna duk wanda yazo wucewa tace. _Sadaka fisabilillah_ Mutumin farko da ya bata naira goma yana yin gaba ta saka kuka. Wai ita da watanni kadan da suka wuce take cikin rayuwar jindadi tare da masoyinta da iyayenta, ita ce take bara tamkar mara galihu. Bara sana'ar da take tattare da kaskanci da mutuwar zuciya. A ranta addua take yi Allah Yasa mufi karfin zukatanmu Ya nesanta mu da kaddara mai muni irin wannan. Ita kenan ma da tayi nadama amma Allah Ya zabeta don gwada imaninta da kuma nuna aya ga sauran mutane. To ina masu aikata zinar duk da sun san laifine amma basu dauketa a bakin komai ba. A ganinsu suna da sauran lokaci. Ina masu bada muguwar shawara a baki ko a rubuce batare da yin la'akari da tasirin da hakan yake yi a zukata masu rauni ba. Da Abubakar bai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103