Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mu." Hankalin Hajjo ya kara tashi. Rabe yaji dadin hakan. Bashi da burin da ya wuce asa dan uwansa ya saki Bara'atu shi kuma ya aura. Tun farkon haduwarsu yaji yana sonta. Duk wasu alamu ya nuna mata inda tayi masa tatas shine ya koma zuga Hajjo suna muzguna mata. A dalilin bata son hadashi da dan uwansa ne yasa bata tona masa asiri ba tunda dama babu mai kaunarta sai mijinta. Ko ta fada kila bazasu yarda ba. A fusace Hajjo tace "Bara'atu fito nan muguwa mai mugun nufi". Bara'atu tana kitchen ta fito da sauri ta durkusa. Lokacin bacci ya fara daukar Baba amma hayaniyar Hajjo tasa ya farka. Sai da ta gama harararta sannan ta dubi Rabe "fita ka nemo min abokanka majiya karfi koda biyu ne" Murmushin mugunta yayiwa Bara'atu sannan ya fita. Ba jimawa suka dawo su uku. Hajjo ta tashi ta nuna musu Bara'atu da Bintu "gasu nan, so nake ku sa su tsallake Malam sau bakwai ko na samu su saki kurwarsa. Bari naje na debo garwashi na kunna turaren mayu." Bara'atu tayi matukar razana ta soma rokon Hajjo tayi hakuri. Ko kallonsu bata sake yi ba tayi gaba abinta tana masifa. Ganin haka yasa ta kama hannun Bintu zasu shiga daki su rufe Rabe ya fizgota. Suna ihu da kuka ya rike Bara'atu wani kato ya daga Bintu yana tsallaka Malam Yahaya da ita a kafadarsa. Mal Yahaya jiki babu kwari ya kasa tashi sai daga kwance yake kokarin yi musu magana amma babu mai sauraronsa. Bayan sun gama da Bintu suka ajiyeta sannan Rabe da dayan suka kama hannu da kafafun Bara'atu suna shillata ta saman Malam. Kuka dai tayi har muryarta ta dashe. A karo na biyar da shilla ta da suke yi Shu'aibu yayi sallama ya shigo. Abinda da ya ga kaninsa yana yiwa matarsa yasa yaji wani mugun daci a wuya. Shi kanshi Rabe ba karamin tsorata yayi ba suka yar da Bara'atu yayi ciki inda Hajjo take tahowa da kasko fal garwashi. Ko tunanin daga Bara'atu, Shu'aibu baiyi ba. Kan Rabe yayi da gudu ya damko shi. Dukansa yake kamar ba jininsa ba yana zaginsa. Hajjo tayi iya kokarinta amma bai sake shi ba sai da ya gaji don kansa ya koma ya daga matarsa yana haki. Hajjo ta durkusa ta daga Rabe. Baki da hancinsa duk jini. Rai a bace tace " yanzu saboda wannan yarinyar kayiwa dan uwanka irin wannan dukan? Meye laifinsa don yana son ceto rayuwar mahaifinsa. Kuma ni na saka shi". "Yanzu saboda Allah Hajjo ko Bara'atu ba matata bace abinda akayi mata yayi daidai kenan? Duk abinda akeyi ina dauke kai darajar Baba amma na rantse duk wanda ya sake shiga sabgar iyalina sai hukuma ce zata raba mu." Da hannu Mal Yahaya yayi masa alama ya durkusa a gabansa. Hakuri baban nasu ya sake bashi da alkawarin idan yaji sauki zai dauki mataki. Bayan kwana uku ciwonsa ya kara tsanani suka je wani asibitin aka ce typoid ce taci hanjinsa ma. Dama irin abinda ake gudu kenan. A kai mutum asibiti babu gwaji su hau dirka masa magani. Washegari Malam Yahaya ya cika. Iyalinsa sun sha kuka sosai. Bayan wata daya Shu'aibu ya hada nasa iyalin suka koma Zaria. Hajjo dai ta kullaci Bara'atu don ta yarda dari bisa dari su suka kama Malam. Tunda suka koma Zaria suke samun budi. Bara'atu har kiba ta soma yi kuma ya samar mata gurbin karatu a ABU Zaria tana karanta Public Administration. Duk sati Shu'aibu yake zuwa Kano amma baya tafiya dasu. Da tayi magana yace babu amfani tunda ba kaunarta sukeyi ba. Itama Hajjon don neman magana ta tambayeshi yace hakan ya fiye musu kwanciyar hankali. A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah. Shekara bata zagayo ba Bara'atu ta haifi Shema'u. Danginsu na Wushishi sun zo sosai tunda mijinta yana bari taje ganin gida. Daga Kano ma su Yaya Abu sun zo sai dai ba'a rabu lafiya ba. Bayan shekara daya da rabi ta haifi Jafar sannan Asmau. Shu'aibu yana kula dasu sosai. A lokacin Bintu ta gama secondary akayi bikinta. Haka suke zamansu lafiya ga jari ya bawa Bara'atu tana sayar da kayan sawa na mata a cikin gida. Sai lokacin sallah kawai suke zuwa Kano ko idan wani abu ya faru. Basu da wata matsala a lokacin. Asmau nada shekara hudu aka haifi Yassar. Wata rana da yamma Shu'aibu yana zaune a falo tare da iyalinsa Rabe ya zo. Shi da matarsa ne Laraba da yaransa biyu. Baraatu bata nuna wata damuwa ba tayi musu tarba mai kyau. Laraba mace ce mai mutumci shiyasa basu dauki lokaci ba suka saba a dan zuwan da suke yi Kano. A can falo kuma Rabe yake sanar da yayansa yazo ne zasu dan kwana biyu shi da iyalinsa. Ko kadan Shu'aibu bai so hakan ba sai dai ya kyale yaga iya gudun ruwansa. Shiru basu da niyar tafiya ita kanta Laraba har kunya take ji. A sati na uku Shu'aibu ya dawo daga makaranta zai shiga dakinsa yaji muryar Rabe yana rokon Bara'atu da ta amince masa wannan zuwan ma duk nata ne. Daga murya tayi tana fada tace cikin kuka "idan baka fita ba sai nayi maka tonon asirin da bazaka kara mutumci ba a duniya. Matarka fa tana gidan nan. Ko don kaga tuntuni ina rufa maka asiri?" Murya kasa kasa yace "ki amince Bara ko ba a gidan nan ba. Ni sau daya ma kawai ya isheni. Ki taimaka." Ihu ta kurma a tsorace ganin yayo kanta Shu'aibu ya bude kofar ya shigo. Yau ma iya karfinsa yasa yana duka Rabe. Abu yayi tsanani har Laraba ta jiyo su ta fito. Korarsu yayi a yamman yace ya fice masa daga gida. Laraba na fahimtar abinda ke faruwa ta tattara ko jiransa batayi ba ta kwashi yaranta suka tafi. Shu'aibu yayi kukan bakinciki sosai sannan yayi mata fadan rashin sanar dashi da wuri. Washegari da safe yace mata zai je Kano ayi maganar a gaban Hajjo don yasan Rabe yanzu yanzu zai juya zance. Haka kuwa akayi Hajjo tace sai ya saki Bara'atu ko ta tsine masa. Jiya Rabe ya dawo gidan jina-jina saboda sharrin data kulla masa. Duk yadda Shu'aibu yayi Hajjo taki yarda. Laraba ma data bada shaida akan Rabe a take Hajjo tasa ya saketa. A kan hanyarsa ta komawa ne Shu'aibu yayi hatsari. Bacin rai ne ke damunsa saboda Hajjo tace idan har bai saki Bara'atu ba sai dai ya sake wata uwar. ABINDA AKE GUDU🙆🏽10 Batul Mamman💖 www.fikrahwriters.blogspot.com Bara'atu ta gama girkinta tayi wanka sannan tayiwa yaranta. Albishir gareta ga maigidanta idan ya dawo wanda take tunanin zai rage masa bacin rai. Ciki ne da ita har wata biyu. Dayake ranar babu islamiyya su Jafar sai wasansu suke yi a gida. Sallamar maza taji a kofar gidan ta dauki mayafi ta fita. Ga mamakinta har da 'yan sanda biyu. A tsorace ta gaisa da su sannan guda cikin 'yan sandan ya miko mata ID card ko ta gane wanda yake jiki. Tana ganin hoton jikinta ya fara rawa "ku fada min abinda ya same shi" Wani mutum a gefe yace "Hajiya sai dai hakuri a hanyar shiga gari muka ga motarsa yayi hatsari.

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});