Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 95

Chapter 95

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,248 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kasa guduwa ta bar gidan,akan Sajeeda tayi karyar makanta,Wanda da batayi ba da yanzu tayi candy kila ma ta cigaba da makaranta,duk wahalar nan da ta Sha da rashin bacci da kwanan fargaba na kusan shekara fassarar da Nusrahh zata mata kenan har da mata Allah ya Isa,sosai taji ciwon abinda Nusrah tayi mata,Aisha ma bar Mata d'akin tayi kanta kamar ya rabe biyu saboda ciwon da yake,gashi batasan halin da Sajeeda ke ciki ba. Damuwa da kuka a daidai lokacin nan bazai kareta da komai ba dukufa agaban mai kowa mai komai shi yafiye mata a ayanzu dan tasan Kabiru bazai tab'a barinta ba zai iya komai dan yaga bayanta. Bandakin da ta gani ta shige bata damu da sanyin ruwan ba tayi wanka jikinta sai rawa yake saboda yunwar da take ji. Amma bazata iya cin abincin ba. Tana fitowa daga bandakin tayi wajen wadrobe din da ta gani,dan da alama Aishar bar Mata d'akin tayi dan ta kwana ita kadai, duk da baa Mata izinin tab'a Kaya ba doguwar rigar da ta gani a goge ta d'auko ta zura ya mata yawa sosai dan Aisha ta fita tsayi sosai har kafarta sai da ya rufe,a dube dubenta ta samo hijabi har kasa ta saka,ta rufe wadrobe din,a can gefen da taga a shimfida sallaya ta nufa dan har da Qur'ani a wajen. Sai da tayi addua ta samu nutsuwa ta tadda sallah tare da ayyanawa tana gaban A Rahman a Raheem yasan me a zuciyarta,yasan mai tazo nema a wajensa tana da yaqinin zai amsa mata dan shi Mai amsa adduar bayinsa ne,mai taimaka wa bayinsa ne a lokacin da suke cikin tsanani,sallah raka'a shidda tayi,ta sallame ta dauki carbin da ta gani ta hau Jan istigifari sai da tayi dubu,ta hau yiwa Annabi sallati tana Jan majina dan har lokacin hawaye bai yanke a fuskarta ba,sai da taji yatsunta na ciwo ta ajiye carbin ta d'auko Qur'ani ta fara karatu,sai da ta karanta iya yadda zata iya ta ajiye Qur'anin,ta koma tayi Sujadda tayiwa Annabi sallati goshinta a kasa ta karanto sunayen Allah 99 kafin ta dago da hawaye Shabe shabe ta daga hannunta ta fara Addu'a "Ya samiu dua ya rabbi Maliki ya quddusu ka bawa ummana lafiya ka tashi kafadunta, Alhamdulillah ya rabbi mungode maka da tarin niimomin ka a garemu wanan halin da muke ciki Kai ka jarrabcemu ya Allah ka yanke Mana ka sausauta ma na ba dan halinmu ba,ka tausayawa umma ka tashi kafadunta kai kake da iko akan kowa da komai,ya Rahimu ka gwada ikonka akan Abba ka bawa Umma lafiya ka bata ikon tashi akan kafafunta ka bude mata bakinta ta iya magana dan ta wanke zargin da Nusrah ke min,ya Allah ka kadai ne shaidata ba yadda za'ayi na cutar da umma ko na bari a cuceta Allah a yanzu banida yadda zan taimaka Mata ya Allah ka taimaka mata ka ara Mata tsawon rayuwa Allah ka nuna min ranar da zata warke kafin na koma gareka" Kuka kawai take rusawa jikinta na rawa sai da ta dade kafin ta cigaba da Addu'a mai tsayi,rawar da taga jikinta nayi har tana Jin jiri yasa ta rufe Addu'ar da amanar rasulu ta shafa ta kwanta akan sallayar ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita cike da mafarkin Sajeeda. 3am Sajeeda A hankali na bud'e idona sai na Kara maida idona na rufe,a rufewar da nayi bana so na yaudari kaina nayi tunanin Ina rayye,duk da ban tab'a mutuwa ba nasan duk Wanda ya mutu binne shi akeyi a Kai shi makwancinsa wato Kabari Wanda a yadda ake bamu labari ana dawo maka da ranka,sai dai banjini a Matse ba,banjini a dadaure ba,ba dai bayan na cire rai da rayuwa na jiyo kamshin mutuwa ba mutuwar nayi ba,a hankali na Kara bud'e idona sai na kurawa saman rufin d'akin ido na mintuna kafin na juya kaina na kalli gefena na Kara juyawa na kalli daya gefen,tuni tunanina ya bani inda nake wato asibti,daga b'arina na hagu nurse ce a kwance a daya gadon da ba kowa. A hankali na daga hannuna na dora akan kirjina naji Yana bugawa na mitsini kaina a daidai wajen da nake Jin bugun zuciyata sai naji tabbas ba mafarki nake ba Allah ya barni a raye bayan na fidda rai da rayuwa,Allah ya barni a raye bayan ciwon da naji a kirjina da na kwatanta shi da ciwon ajali,Ashe Ina da sauran kwana a gaba, Ashe cuta ba mutuwa bace ba,tuni hawaye ya hau zubo min Ina daga kwance wallahi ban taba tunanin Zan rayu ba,kuka na fara yi kasa kasa na fara motsa bakina dan nace Alhamdulillah. Ga mamakina sai naji sautin maganata a kunnena,sai na zaro idona na hau wuwurga idona naga ko dai wata ce a gefena take hamdala na dauka nice,sai dai banga kowa ba nurse ce dai dake bacci a daya gadon. Kirjina na dan bugawa da Kar na yaudari kaina na Kara cewa "Alhamdulillah ya rabbi" Sai na Kara Jin sautin muryata a kunnena. Sai na saki murmushi Ina tunanin yadda nake neman saka rai da magana bayan nasan da wuya. Sai na Kara gwada magana Ina "Yesmeen Kinga Zan yaudari kaina Ina Jin maganata a kunnena" Sautin maganar ya Kara tafiya kunnena daya saka jikina d'aukar rawa nasan abune da bazai yu nayi magana ba taya kunnena ke yaudarar kaina da Ina magana har maganar tawa na fitowa. Sai naja tsaki a zuciyata na fi minti goma a haka kafin na waiga wajen nurse ina bari na sake yaudarar kaina sai nace "Nurse ki bani ruwa in Sha" Sai naga ta bud'e idonta tana kallona,sai na zaro idona Ina Jin bugun kirjina da ido na bita naga ta sauko daga gadon ta nufo wajen da nake tana "Yanzu nan fa bacci ya daukeni ruwa zaki Sha" Jikina wani irin rawa yake hannuna da nake iya motsawa na Kai na damki hannunta Ina "Kina nufin kinji Mai nace"? Sai naga ta yamutsa fuska sai ta kawo hannunta ta tab'a kaina tana "Ko dai zazzabi ne a jikinki bangane naji mai ki ka ce ba ba ruwa kikace Zaki Sha ba"? A hankali na saki hannunta na maida idona na rufe bazan iya fassara halin da nake ciki ba,hakane kawai yasa na rushe da kuka na hau yiwa Allah godiya,Ina addua Allah yasa ba mafarkan da na Saba yi bane nayi akan Ina magana,Allah buwayi gaggara misali,Allah maji rokon bawansa,Allah mai amsa adduar bayinsa a lokacin da ya fidda rai,dan wallahi na fidda rai da rayuwa ko iya maganar Allah ya bani ikon yi alhamdulillah bani da bakin gode masa,Ina ma zan ga Yesmeen Ina ma tana kusa dani,Ina ma itace ta fara jin muryata,nasan bazan iya fassalta farinciki da zata yi ba ,ta Sha cewa tayi kewar murya ta,ganin nurse din ta fice waje yasa na fara magana a fili dan na tabbatar "Alhamdulillah ya Allah Alhamdulillah Allah da ka nuna min Wanan ranar da zan iya magana, Kabiru asirinka ya tonu" Wallahi naji sautin maganata ta tafi kunnena dan da k'arfi nayi, Kukan farinciki kawai nake,tunanin da ya fado min yasa na gwada daga daya hannun nawa sai naga na daga sai na zaro idona, bana iya

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});