Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 100

Chapter 100

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,247 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ganin yarana a tare dani da suke murnar warkewa ta yafi komai faranta min,ni nasan karshen Kabiru yazo tunda asirinsa ya tonu,alkadarinsa ya karye tunda har muka warke nida Annur. Yanzu Kuma Yesmeen ce a Raina tunda Gwaggo tace bata je ba,Yaya Asmau itama sai maganarta take muna Kan hanya tana Kara daga min hankalin maganganun da taji Kabiru nayi da Yan kungiya a kanta,akan zasu kasheta Tuni na fara kuka wiwi dan zan iya d'aukar komai, matakin da zan dauka akan Kabiru na rabuwa ne,Zan rufe sirrinsa ga mutane saboda yarana bana so laifin mahaifin su ha shafe su,amma indai Kabiru ya tab'a Yesmeen wallahi sai Inda Karfina ya kare har kashe shi zan iya yi, Yesmeen bani na haifeta ba amma kaunar ta a zuciyata take,matsalar ba wani sanin wajen dangin mahaifinta tayi ba,gashi bata fadamin Inda zata gudu taje ba. Har muka iso Tasha Hankalina baa jikina yake ba, Mahaifina ya fara laluba Mana motar da zai Kai mu har can,muka samu waje muka zauna. Ina Jin Gwaggo da Yaya Asmau nata hirar Kabiru Nusrah na kuka,Hamza da Annur sunyi jingum jingum,amma ni zuciyata na wajen Yesmeen. Wani bakin mota ne ya shigo ya wuce ta gabanmu nabi motar da kallo,dan gaba da mu naga motar ta tsaya,Kamar wacce ake bawa umarni na zubawa motar ido, wani kyakyawan saurayi ya fara fitowa daga motar kafin a bud'e daya bangaren wata sanye da farin hijabi ta saka nikaf itama ta sauko daga motar, Haka kawai naji kirjina ya buga,sai na zubawa mai nikaf din ido, da ta bamu baya. Saurayin ya zagayo ta wajen da take tsaye ya hau magana Yana wuwurga hannu Yana nuna motocin,dake zube a Tasha. Ni dai ido na zuba musu bansan dalili ba naga saurayin ya nufi wajen da aka jera motocin katsina Dan akan motar na gane motar katsina ce dan an rubuta a jikin wani katako an dora akai. Mai niqaf din Kuma ta jinjina a jikin motar,ni kaina bansan Mai yasa na zuba Mata ido ba har saurayin ya dawo ya mata magana yayi gaba ta fara bin shi a baya a hankali kamar wacce bata so,har Suka isa wajen motar kallon su kawai nake saurayin kuwa sai magana yake Yana leka fuskarta,haka kawai nake hango Yesmeen a tare da mai niqaf din,irin tsayuwar Yesmeen da tsayinta,bansani ba ko dan Ina tunaninta yasa na fara hango yanayinta a wajen mai niqaf din,suna tsaye idona akanta,da alama a takure take dan saurayin ya dage sai zuba yake idan tayi hanyar motar sai ya sha gabanta sai mika Mata wayar hannun sa yake,nidai ido na zuba musu suna tsaye na Kuma kasa d'auke idona akansu har sai da babana ya dawo Yana mu tashi ga mota can,a hankali na mike Ina k'ok'arin d'auke kaina daga kansu naga ta daga niqaf din ta sama,naga Yesmeen dita ce idan har ba gizo idona ke min ba,Yaya Asmau ce a gefena hakane yasa na damko ta Ina "Yaya Asmau duba min can Kamar Yesmeen nake gani ko idona ne? Da sauri ta waiga sai ji nayi ta kwalla mata Kira da "Yesmeen"!!! Yesmeen ta juyo da sauri tare da kallon Inda taji sunanta. Tabbas Yesmeen ce ba gizo idona ke min ba,a daidai lokacin da ta kwaso da mugun gudu tana isowa gabanmu kamar wacce wuta ya jata ta daskare a tsaye tana kallona bakinta a bud'e. Ni kuwa hawayen farinciki ya hau wanke min fuska nima Ina kallonta, Kamar Mai koyon magana tace "Umma kece ko mafarki nake yi? "Nice Yesmeen ba mafarki kike ba" Wani Irin cafka ta kawomin ta rungumeni ta fashe da kuka tana "Umma Ashe akwai ranar da zan Kara Jin muryarki,umma ashe akwai ranar da zan ga kin tsaya akan kafafunki,dan Allah karku tasheni idan mafarki nake. Nima kankameta nayi cikin kuka Ina "Ba mafarki kike ba yesmeen Allah ya warkar dani,Allah yayi ikonsa akaina Allah ya amsa adduar da kike Dade kina min" Cikani naga tayi ta zub'e akasa tare da yin Sujadda sai kuka take tana "Alhamdulillah ya Allah Alhamdulillah Alhamdulillah Allah nagode maka" Sai da ta dade a haka daidai da mahaifina sai da idonsa ya ciko da kwalla, Tana dagowa tana "Umma a yanzu da Kika fara magana Zaki wankeni a wajen Nusrah,tace ni muguwa ce saboda ba ke Kika haifeni ba shiyasa naki fadawa kowa halin da kike ciki,umma ke zaki wankeni a wajensu" Har ga Allah ji nayi raina ya b'aci na kalli Nusrah dake zare ido na fara magana Ina "Au haka kikace dan bani na haifeta ba shi yasa bata fada muku ba, kunsan abinda Yesmeen tayi min kuwa?so kuke ta fada muku mahaifinku ya kasheta" "Umma dole naji haushinta kema kinsan yadda nake da ita,idan ta fadamin bazan nunawa Abba nasan komai ba iyakaci na Kira Gwaggo a waya na fada mata da kila baki dade haka ba umma ace duk tsawon lokacin nan Yesmeen tasan abinda ke faruwa sai ta ja bakinta tayi shiru umma dole naji haushinta" Ina k'ok'arin magana mahaifin mu ya dakatar dani Yana ya isa haka mu wuce ana jiranmu. Yesmeen kuwa tana ganowa Annur na magana ta Kara fasa ihu tana hamdala tama kasa tsayawa waje daya. Kuka hade da farinciki haka muka ringayi har Haka muka je Shiga mota Ina godewa Allah da ban wahala wajen Neman Yesmeen ba,ko Wanda ya kawota tashar bata kara kallon wajen da take tsaye ba har muka tafi. ta rik'e hannuna Tama kasa cikani sai tambayoyi take min akan ya akayi na warke?Ina Abba ya akayi su Gwaggo Suka zo? Ta hau bani labarin yadda ta fito taga su Kabiru da yadda ta gudu wasu bayin Allah suka taimaka Mata,ta kwana a yanzu ma dan mai gidan ne ya kawota tashan dan karya ta musu. Murmushi kawai nake dan da alama Yar tawa tayi saurayi Sosai nake k'ok'arin danne zuciyata dake san tuna min Yaya Abu da ta cutar da kanta akan kudin,da zaa mutu a bari a gidan duniya,yau akansa ta kassara rayuwarta,tsigar jikina sai tashi yake da na tuna irin wahalar da na Sha. KABIRU Yana fita daga gidan ya hau neman Rabiu a karamar wayarsa sai ihu yake Yana "Ka cuceni Rabiu ribar Mai na samu a Shiga kungiya,yau gashi asirina ya tonu,tun ban mori kudina ba,duk wahalar nan da na Sha ko shekara biyu banyi ba,Sajeeda ta gano sirrina,iyayenta sun gano sirrina yarana sun gano sirrina mai ya rage min kuma" Kuka kawai yake yana cigaba da Kiran Rabiu da bai San adadin miscal din da ya Masa ba. Yana k'ok'arin ajiye wayar yaji an dauki wayar hayaniyar da yake ji yasa ya kasa Jin Mai ake cewa ya kashe wayar ya sake Kiran wayar. A madadin yaji muryar Rabiu sai muryar wani yaji Yana "Mai wayar nan yanzu nan wani tirela ya murkushe motarsa ko shurawa baiyi ba,dan trilar ta tsatse shi" Wani irin ihu Kabiru ya saki tare da taka birki da k'arfi Yana "Rabiun ne ya mutu yanzu kana nufin ya rasu" Kashe wayar yayi ya fito daga motar a kidime kamar sabon mahaukaci haka ya ringa zunduma ihu dan ko a yau haka Suka ringa waya dashi,yana fada masa ya samo tsalalliyar yarinya zai je ya kwashe arzikin ta.

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});