Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 45

Chapter 45

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,229 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na zubo mata na halin da Sajeeda ke ciki cikin ihun ta ringa lalube da hannu tana "Mai ya samu ummana ku fada min dan Allah mai ya sameta"? "Dalla ki rufewa mutane baki kin cika mutane da ihu duk ke kika jawo ma ta sume,haka kawai zaki daina gani ga idonki tarr a bud'e" Yaya Abu tace a tsawace a daidai lokacin da Kabiru ya kawo ruwa aka hau watsawa Sajeeda dogon numfashi kawai taja,hakane yasa Yaya asmau tace "Ina ganin mu kaita asibiti tunda har yanzu tana numfashi,a hada da Yesmeen din kawai muji mai ya samu idonta,da wanan Kabiru ya fara k'ok'arin kinkimar Sajeeda da taimakon Yaya Abu. Asmau Kuma ta saka saka hijabinta ta ruko hannun Yesmeen dake ta kuka tana kallon sama,tasan saboda ita Sajeeda ta yanke Jiki ta Fadi tana tsoron wani abu ya samu Sajeeda Kamar bata gani ta ringa hada hanya har suka isa bakin motar Kabiru,suka shige, Kabiru yaja motar a guje. Suna isa asibiti akayi emergency da Sajeeda Yesmeen Kuma Yaya Asmau tayi bangaren da likitan ido, yake, Kabiru sam bata Yesmeen yake ba dan yasan likita bai isa ya gano silar makancewar ta ba yau ranar farinciki ce a gare shi Amma Sajeeda na neman daga masa hankali ya rasa wane irin kauna take yiwa Yesmeen haka,ko Annur daya kurmance bata daga hankalin ta kamar haka ba. Yana tsaye a kanta da Yaya Abu likita na duba ta dan private ya Kai su. Yesmeen Jikinta rawa kawai yake tana Jin kamar ta zura da gudu tana tsoron likita ya dubata ya gano tana gani,bata San ya zatayi ba. Har kinkina take wajen amsa tambayoyin da likita ya ringa mata akan idon nata Mai ya fara samun idon nata kafin ta daina gani,haka ta ringa bashi Amsa Yaya asmau na tayata da ya taimaka ya dubata taya tashi daya zata daina gani. Likita gadon dake can gefe yace Yaya Asmau ta Kai Yesmeen ta kwantar da ita zai haska idon nata. Da wanan Yaya Asmau ta rik'e hannun Yesmeen ta kaita Kan gadon Yesmeen ta kwanta idonta a sama tana hawaye, addua take Allah yasa Yaya Asmau ta fita daga office din ta roki likita ya rufa mata asiri" Yaya Asmau na tsaye a kanta. Likitan ya iso wajen gadon ya samu wani cocilan ya dallarewa Yesmeen Ido,Yesmeen ta rufe idonta da sauri,cikin mamaki likitan ya Kara gyara tsayuwar sa dan daga yanda ta rufe idonta na nufin tana gani,dan da bata ganin ko motsa idon ba za ta yi ba. Ya Kara kure duk hasken cocilan din ya haske idonta ta Kara rufe idonta dan ji tayi hasken na ci mata ido, Likitan kuwa cikin mamaki ya kalli Asmau ya maida kallon sa kan Yesmeen yana "Ai tana gani baa abinda ya samu idonta gaskiya" Yaya Asmau ta saki baki tana kallon likitar Yesmeen hankali a tashe ta fara girgiza kai tana "Bana gani likita dagaske bana gani ka yarda dani bana ganin komai sai duhu" Likitan a dan rikice yace "Bakya gani fa ki ka ce idan ba kya gani ai ba za ki rufe idon ki da na haska da cocilan ba,gaskiya a dubawar da nayi kina gani" "Likita anya tana gani kuwa ya za'ayi tana gani tace maka bata gani"? Tom bansani Mai yasa bata gani ba,amma indai bata gani yadda na haska idon ta ko motsi baza tayi da idon ba" Amma bari na Kara duba idon nata. Ya d'auko wani Abu kamar glass ya sawa Yesmeen dogon igiyar ya jona da wani Abu Mai Kama da computer dake saman wajen gadon ya fara duba idon yesmeen,sai da ya duba komai daya shafi idon ta amma bai ga wani matsalar da zata saka Yesmeen taki gani ba" Koda ya gama dubawa cire glass din yayi daga idon yesmeen yace Yaya Asmau ta sauko da ita,ya koma wajen zaman sa ya hau rubuce rubuce sai da ya gama ya kalli Yaya Asmau yana "Ni dai duk binciken da nayi gaskiya ba abinda ya samu idon ta idan dai har bata ganin Ina ga larurar tata bata asibiti bace" Yaya Asmau kuwa cikin mamaki tace "Abin nan da da ban mamaki ga idonta a bud'e dai amma Wai bata gani Kai ma ka duba baka ga komai ba" Yaya Asmau tace tana Kai hannu wajen fuskar Yesmeen ta ringa juya hannun Kamar zata tsone mata Ido Amma Yesmeen ko motsawa bata yi ba ta ringa kallon sama, likita ya mik'a wa Yaya Asmau takarda akan ga magungunan dai a siya mata. Haka Yaya Asmau ta ruko hannun Yesmeen suka fito daga office din Suka nufi d'akin da aka kwantar da Sajeeda. Suna Shiga suka ga Sajeeda a zaune duk da ruwa a jikinta kuka kawai take sharba Yaya Abu na masifar tayi shiru ita fa ba yarinya bace Mai haka zata cika asibitin da kuka, Kabiru kuwa shiru kawai yayi dan tana farfadowa ta fara kuka. Sajeeda kuwa Yesmeen data ga tana kallon sama hannun ta na lalube sun shigo d'akin yasa ta Kara rushewa da wani kukan tana "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha "Yaya Asmau mai likita yace ya samu idon yesmeen dan Allah karki ce min dagaske ne Yesmeen ta daina gani" Yaya Asmau na k'ok'arin magana Yaya Abu ta Kara dakawa Sajeeda tsawa tana "Wai ke Mai hakane Sajeeda ke fa ba yarinya bace ke idan kina irin wanan kukan Mai kikeso ita Yesmeen din tayi"? "Ki barni Yaya Abu dole nayi kuka dan tunda Abban Nusrah ya hadu da wanan abokin nasa ya shigo rayuwar mu da Sunan taimako nake ganin masifa kala kala,wlh rabona da kwanciyar hankali tun kafin Abban Nusrah ya had'u da abokin nan nasa,tunda kuwa suka hadu,daga wanan sai wanan,daga komawar mu gidan daya bamu Annur ya kurmance,nima kaina ba lafiya ce dani ba,Wai yanzu tashi daya Yesmeen ta wayi gari tace bata gani,sai nayi magana Abban Nusrah yace ba haka ba wlh bazan iya cigaba da zama a gidanan ba idan har Abban Nusrah bazai maida Masa dukiyar sa ba wlh gida Zan koma,ko shekara daya bamu yi ba masifar yau daban na gobe daban" "Ikon Allah Sajeeda a hayyacin ki kike kuwa,Mai ya hada kurmancewar Annur da makancewar Yesmeen da abokin mijinki, Mai laifin Wanda ya taimakawa mijinki ya tsamo shi daga talauci dan ya dandana arziki kina nufin kin fi karfin Allah ya jarrabce ki"? "Haka nake fama da ita Yaya Abu ban taba sanin Sajeeda makiyata bace sai yanzu,tunda ta bud'e ido taga Allah ya amsa adduata na samu mai taimaka min ta dorawa kanta masifa Bata tab'a zaton alheri kullum sai sharri da zargin abokina take, ta dage bata hanyar halal abokina ke samun kudi ba, Bayan abokina Yana da balain kudi,shikenan duk wani Mai kudi ba ta hanyar halal yake neman kudinsa ba,yanzu sai ace dangote ma ba ta hanyar halal yake samun kudinsa ba,Sajeeda burinta taga na Kare rayuwata a talauci Ina yawo gida gida Ina gyara Allah ya kawo min wanan bawan Allah dan ya taimaka min Sajeeda tace ba haka ba tsabar masifa ko tuntub'e tayi sai tace tana zargin ba ta hanyar halal abokina ke samun kudi ba" "Nasan mai nake

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});