Chapter 19
Chapter 19
kit 14k Herbal whitening soap Body cream Face cream Scrub Cleanser Glow oil Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Team glow😍 *RUFAFFEN SIRRI* *NA SADNAF* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *Page 9* "Yesmeen Kar ki tafi ki barni Yesmeen" Sajeeda ke ta maimaitawa a mafarkin ta har sai da ta tashi a firgice bakin ta d'auke da sallati. Dan sai taga kamar a gaske ba mafarki ba. Sai da ta ga k'ofar d'akin ta a rufe yake ta tabbatar da mafarki take tabi ta hada gumi,ta kalli hannun ta da ta rik'e wasikar da ta rubutawa Sajeeda,ta dago ta kalli agogo taga karfe Sha biyu na dare ta mik'e tsaye da sauri dan har ga Allah so take ta gudu ta bar gidan,dan rayuwarta a cikin hatsari take tunda har Kabiru ya fara mata Barazana akan zai kasheta idan bata gudu ba watarana zai kasheta din. Jakar da ta zuba kayan ta ta d'auko bayan ta ajiye takardar a karkarshin pillo a hankali ta fara karewa dakin kallo hawaye na zubo mata hakika Sajeeda ta rik'e ta tamkar Yar cikin ta bata tab'a barin ta tayi maraici ba duk da dangin mahaifinta sun watsar da ita,mahaifinta ma gani take ya manta da Yana da ita dan bai tab'a Neman ta ba. A yanzu bata san hannun wa zata fada ba Tafi minti talatin a tsaye tana zubar da hawaye tana tunanin halin da ta tsinci kanta a ciki tayi matukar nadamar leka Kabiru,dan da bata leka shi ba da duk haka bata faru ba. A hankali ta murda k'ofar d'akin ta fita palo kirjinta na dukan uku uku fitilar palon ma a kashe take ko Ina shiru sai karar fanka. Cikin Sand'a ta nufi k'ofar fita daga palon ta murda a hankali ta fice tare da rufo k'ofar duk abinda take yi jikin ta rawa kawai yake. Taku uku tayi taji motsin bud'e k'ofa. Cikin zafin nama ta shige cikin fulawowi dake kewaye da jikin bangon runtse idon ta tayi da k'arfi dan ji tayi abu ya soketa a baya ta d'auke numfashin ta a lokacin da Kabiru ya fito Yana dube dube. Ganin bai ga kowa ba yasa yayi bayan gidan dan ya duba lafiyar karen sa kasan dan Kamar motsi yaji Yana yin bayan gidan Yesmeen ta fito daga fulawowi ta shige cikin gidan da gudu ta bud'e kofar ta ta shige tana sauke ajiyar zuciya dan ta balain tsorata ta d'auka Kabiru zai ganta. Ba haka taso ba taso ta gudu a yau dan ta balain tsorata da Kabiru amma ko bata gudu yau ba sai ta gudu gobe. Tana Jin motsin sa a bayan gidan sai da ya jima kafin ya koma ciki. Sajeeda A firgice ta tashi daga baccin da take ta hau kalle kalle,ganin Kabiru a gefen ta yasa ta hau tashin sa tana cigaba da kallon bakin k'ofar jikinta na rawa Karen da Kabiru ya kawo cikin gidan tayi mafarki ya shigo Yana kokawa da ita Yana jan zanin ta tana ja Kabiru bude idonsa yayi yana "Sajeeda zan bar Miki d'akin nan na koma dakina kawai dan bakya barina nayi bacci na gaji" Kuka Sajeeda ta fashe dashi tana "Kabiru dan girman Allah ka fitar da Karen nan da ga gidanan rabon da nayi bacci cikin dadin rai har na manta tun muna tsohon gida rabona da samun bacci Mai nustuwa kullum sai nayi mafarki da Karen nan na gaji Wallahi na gaji Kabiru idan har ba za ka fitar da Karen nan daga gidanan ba wlh zan bar gidanan kullum cikin fargaba nake dare yayi ban da mugayen mafarkai da nake fama dasu. Ido Kabiru ya zuba mata cikin mamaki dan ya d'auka aikin da shugaba yayi a kanta zai saka duk abinda ta gani bazata iya magana ba. Ya za'ayi ya barta ta bar gidan bayan yazo dab da cimma burinsa Dole yasan dabarar da zai mata nan da kwana uku yasan ya samu cikar burin sa tashi yayi ya zauna Yana "Ya isa Sajeeda tsaya ki saurareni" Sajeeda tsagaita kukan da take tayi Kabiru ya fara magana Yana "Ki kwantar da hankalin ki zan maida karen wajen Wanda ya bani amma baya gari sai ranar alhamis zai dawo na Miki alkawari Yana dawowa zan maida karen akwai barayi sosai a unguwar nan shi ya sa na karbo Karen dan na san idan barayi najin haushinsa zasu ji tsoron shigowa amma tunda kin saka tsoro a ranki ran alhamis zan maida Karen shikenan"? Gyada Kai Sajeeda tayi Kabiru ya saki murmushi Yana ta koma ta kwanta. Sajeeda tashi tayi tana bari tayi sallah raka'a biyu. Kamar kullum dai tana raka'a biyu bacci ya kwasheta akan sallaya. Kabiru kuwa na ganin haka ya fito daga d'akin yayi waje. Yesmeen tuni ta ajiye batun guduwa a gefe dan sau uku tana mafarkin idan zata gudu sai Sajeeda tazo tayi ta rokonta Bata san Mai yasa take yawan mafarkin ba. Yau har suka gama karyawa bata ga Sajeeda ta fito daga daki ba taga dai Kabiru ya fita ganin har Sha daya Sajeeda bata fito daga d'akin ba yasa ta nufi d'akin Sajeedan dan ta dubata. Koda ta tura k'ofar d'akin Sajeedan a kwance ta ganta tana ta mutsu mutsu tana girgiza ita kadai idon ta a rufe ta hada gumi,. Da sauri ta Isa bakin gadon ta fara girgiza ta tana "Umma umma ki tashi" Sai dai bata bude idon ta ba ta cigaba girgiza hakan kuwa ya Kara dagawa Sajeeda hankali tayi waje da sauri taga ko su Saifullahi na nan" Ganin su Saifullahi basa nan da ta duba dakinsu yasa tayi d'akin ta dan ta d'auko wayarta ta Kira Kabiru ta fada Masa halin da Sajeeda ke ciki. Jikinta rawa kawai yake a lokacin da ta d'auko wayarta akan gado ta d'auko wayar kenan kamar ance ta kalli windon dakinta taga Karen a kwance Yana girgiza Kuma a ringingine Yana wani gurnani Sakin baki tayi tana kallon Karen dan bata tab'a ganin Kare a kwance kamar mutum ba sai wanan,kamar an mitsineta tayi d'akin Sajeeda da gudu,Koda ta Shiga girgiza da mutsu mutsun ta cigaba da yi ta Kara fitowa da gudu tayi dakin ta ta tsaya a bakin windo shima mutsu mutsun taga Karen nayi,sai ta fara k'ok'arin ta hada tunanin ta waje daya tunanin daya darsan mata a zuciya yasa tayi waje da gudu zuciyarta cike da tsoro da fargaba tayi bayan gidan ta tsaya nesa da wajen da Karen yake har lokacin Yana ta girgiza dube dube ta fara yi idon ta ya sauka akan wani katon dutse bata tsaya bata lokaci ba ta d'auki dutsen ta jefa wa Karen ya kuwa mirgina ya fara haushi Yayo kanta ta kwasa da gudu ta koma ciki tare da rufo k'ofar Jikinta karkarwa kawai yake dan saura kiris ya kawowa kafarta Cafka. D'akin Sajeeda ta koma ta kuwa ganta a zaune tana sauke ajiyar zuciya ta bi ta hada gumi yesmeen kuwa tuni ta daskare a tsaye dan a yanzu abinda take zargi ya tabbata. Sajeeda kawai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111