Chapter 59
Chapter 59
ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84* *PAGE 20-25* Yesmeen Motsin mutum da taji yasa tayi saurin Mai da idonta sama tana cigaba da kurba shayin da Yaya Abu ta bata dan abincin karyawar da suka hada har da ita,yunwar da ta kwana dashi yasa suna fita ta fara ci,tana adduar Allah yasa Kabiru ya fita yanzu ta leka Sajeedan. Tana Jin fitar su Yaya abu motsin da taji kamar an taho d'akin yasa tayi saurin mai da idon ta sama tana cigaba da cin abincinta. Ganin Kabiru ne ya shigo ya tsaya a bakin kofa Yana Kare mata kallo yasa taji kirjinta ya buga da k'arfi,tasan indai Kabiru ya rabo Inda take ba alheri a tare da shi sai sharri tuni ta fara addua a zuciyarta, idonta na sama tana wuwurga ido amma tana iya ganin kabirun Da ya shigo d'akin ya nufo wajen da take a hankali,tuni taji hankalin ta ya Kara tashi, zuciyarta ta fara rayya mata da kila shaketa yake so yayi tunda yaga ba kowa a gidan,kila ma Sajeeda ta fada Masa, ta gaya mata sirrin sa shi yasa ya shigo dan ya kasheta,hannun ta dake rik'e da kofin shayi rawa kawai yake tana kallon sama. Kabiru kuwa ya tsugunna a gabanta Yana Kare mata kallo, ganin sama take kallo kamar dai makauniyar yasa ya mik'a hannun sa wajen idon ta kamar zai tsone mata ido, Yesmeen kuwa cikin mugun bugun zuciya ta dake bata kifta idon ta ba dan tuni ta gano so yake ya tabbatar da tana gani ko bata gani,addua kawai take Allah ya kareta daga sharrin sa dan tasan ba kowa a gidan idan har cutar da ita zai yi ya zama dole ta mai da kallon ta kasa ta nuna Masa tana gani,tana kallon lokacin da ya mik'e a hankali cikin sand'a yayi gaba Yana kallon ta,ya Kara dawowa baya,duk asan yaga ko zata bi shi da ido,amma haka ta daure tana wuwurga ido sama, Kabiru kuwa ganin duk yadda yaso ya gano ko tana gani duk da yayi gaba ya dawo baya, idonta dai a sama yake tana wuwurga wa,sai ya matsa kusa da ita ya sunkuya Kamar zai mata kiss yasan indai tana gani yadda zai yi din dole ko yayane ta motsa, Yesmeen da taga ya matso da ita daf kamar zai hau kanta cikin dakiya da rawar jiki da dabarar daya fado mata ta fara magana tana " Waye anan wanene? Kabiru cak ya tsaya Yana kallon ta dan sai yake ganin kamar tana gani, Yesmeen kuwa kofin shayi ta saki ta hau wuwurga hannu tana cigaba da ihun magana da "Waye anan"? So take Sajeeda ta jiyo ta ta kawo mata agaji,tunda take bata tab'a Jin ta a cikin irin wanan tashin hankalin ba,da dukan alamu Kabiru so yake ya cutar da ita dan ya d'auka bata gani. Kabiru kuwa ganin tana magana da k'arfi tana wuwurga hannu tana shafa iska yasa yayi waje cikin sand'a yaje bakin k'ofar Sajeeda dan yaji ko zai jiyo motsin ta,shi ba Yaro bane daga yadda yesmeen ta jike da gumi,da alama tana gani raina masa hankali kawai take. Numfarfashin Sajeeda kawai yake jiyo wa a d'akin. Bai tsaya bata lokaci ba ya koma dakinsa ya d'auko garin maganin daya nemo tun jiya daddare ya fito ya koma d'akin Yesmeen Yesmeen kuwa tana ganin fitarsa ta mik'e da sauri ta fara yarfa hannu tana tunanin abinda zata yi dan tasan dole zai dawo,ba yadda za'ayi da hankalin ta ta zauna Kabiru ya cutar da ita hakane yasa ta yanke guduwa,tana zuwa bakin kofa taji takun tafiyar sa ya nufo d'akin tuni ta Kara rikicewa tana adduar Allah ya kawo mata agaji,idan har ta bari ya gano bata gani,tasan sai yaga bayanta,dab da isowarsa d'akin ta mai da idonta sama cikin zafin nama ta fara lallubar iska tana "umma kina Ina kece"? Kabiru kuwa ya kauce daga gabanta da sauri daya ga tana lalubar iska dan saura kiris ta tab'a shi,sai yaji kansa ya daure dan daga yadda take yi kamar bata gani,dan Yana kaucewa ta gwaru da bango,ta saki sallati da k'arfi tana "Umma kina ina?Ba kowa ne"? Kabiru gyaran murya yayi dan baya so Sajeeda ta jiyota,Yesmeen kuwa tana lalluban iska tace "Abba Kaine"? "Lafiya kike kwallawa umman Kira ?mai zata Miki"? "Abba motsi nake ji a dakina Kuma nasan ba kowa tunda su mama sun fita" "Sai ki juya ki koma ba kowa nima yanzu Zan fita aiki Umman ku bacci take karki takura Mata" "Abba bari naje wajen Umma bana so na zauna ni kadai tunda fita zaka yi" Yesmeen tace tana kikifta ido,duk abinda yake tana kallon sa har bakin ledar dake dukunkune a hannun sa kallon ta kawai Ganin ya nufo wajen ta a hankali yasa ta daga murya tana cigaba da lallubar iska da "Kaji Abba zanje wajen Umma na zauna da ita dan Allah" Dab da ita ya tsaya jikinta ya kwashi wani irin rawa numfashin ta kuwa ya fara barazanar d'aukewa a lokacin da ya kaiwa wuyan ta shaka da k'arfi kafin tayi tunanin ihu ya matse bakin ta fuskarsa dab da nata ya fara magana daidai kunnenta "Na rantse da Allah duk ranar da Kika bud'i bakin ki kika fitar da sirrina Yesmeen sai na kashe ki,duk wani motsin ki duk wani abu da kike yi Ina kallon ki Yesmeen wanan ya Zama rufaffen sirrin da zaki binne a zuciyarki har ki koma ga mahallincinki, Yesmeen idan har zan iya sadaukar da abubuwa masu mahimmanci dan na kawo wanan matsayin kau dake tamkar kashe kuda ne a wajena Yesmeen Yesmeen ki iya bakinki ko tari kikayi Ina kallonki, kinji mai nace ko bakiji ba"? Yesmeen da taji numfashi na mata wahalar shaka Kai kawai take gyadawa dan ba karamin shaka ya mata ba idan banda rawa ba abinda jikinta ke yi,yana sakinta ta zub'e a kasa ya ja da baya Yana kallon ta,dan a yanzu ya tabbatar wa kansa bata gani dan da tana gani,da ko yayane zata nuna alama a lokacin da ya Kai Mata shaka wuya,amfani da maganin bazai masa wani amfani ba kila a gaba,yasan ya gama tsoratar da ita da ko wuka aka saka Mata a wuya bata Isa ta tona Masa asiri ba,duk da ko bata tona ba bazai samu irin kwanciyar hankalin da yake so ba tunda har akwai wacce tasan sirrinsa sannu a hankali zai kau da Yesmeen cikin ruwan sanyi yanzu abinda zai saka a gaba shine yadda zai samu Kan Sajeeda sai yadda yayi da ita,dan wadanan surutan da take masa na Neman daga Masa hankali gani yake yau da gobe zata iya jefa zargi a zuciyar su Yaya Abun. Da wanan ya juya ya bar d'akin Yesmeen din har zai wuce
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111