Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,232 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tafi gidan abokin na sa na masa godiya na so ya bari zuwa gobe ya dage mu tafi. Haka na shirya cikin dogon hijabina na haye machine din sa mu ka dau hanya. Ni dai ban san wajen da mu kayi ba kalle kalle kawai nake har mu ka iso wani wawakekken gida da aka masa ado da fitilu masu haske kamar ba dare ba. Haka kawai na ji tsoro ya Kara rufe ni na hau sallati a daidai lokacin da ya kashe machine d'in na sauko yayi parking a gefe ya hau buga gate d'in. Wani ne ya bud'e yana ganin Abban Nusrah ya washe baki Ya rusuna ya bashi hanya tare da masa sannu da zuwa, nidai tsayawa nayi daga baya Ina mamakin yanda Mai gadin yasan Abban Nusrah har yake wani rusunawa. Sai da Abban Nusrah ya juyo ya nuna min hanya na Shiga gidan da bismillah dan sai naji Ina karkarwa har Ina Jin sanyi na Shiga na. Abban Nusrah kuwa kamar yasan gidan yayi gaba nayi saurin ruk'o hannun sa ya juyo Yana kallo na. "Abban Nusrah tsoro nake ji ka ga girman gidan fa" Nace Ina kalle kalle Ya janye hannun sa Yana "mai abin tsoro ke dai kawai ki biyoni" Kirjina na dukan uku uku na cigaba da bin sa a baya har Muka karaso wani k'ofar da gabad'ayansa glass ne. Abban Nusrah ya danna wani waje k'ofar ta bud'e da kan ta,ya shige nima nabi bayan sa Ina zare ido,dan tunda nake a rayuwa ta ban tab'a ganin irin Wanan gidan ba. Ba kowa a palon Abban Nusrah kuwa ya samawa kansa wajen Zama ya nuna min kujera akan na zauna. Ni kuwa rawar da jikina yake yasa na zauna a kasa. Abban Nusrah ya d'auko wayar sa daga Aljihu Yana "gamu nan mun zo" Daga haka ya mai da wayar cikin jaka. Ni dai Sam ban ji hankalina ya kwanta ba dan Addu'a kawai nake a zuciya ta. Takun da na jiyo yasa na daga kaina Ina kallon sama. Wata mata ce mai kib'a fuskarta d'auke da murmushi bayan ta Kuma wani ne shi ma da kib'ar sa da Alama shi ne Abokin Abban Nusrah da matar sa sai naji hankalina ya dan kwanta har suka karaso wajen da mu ke. Matar tace "Haba ya zaki zauna a kasa ki zauna a sama mana" "Aaa nan ma yayi" Duk yanda naso ta barni a kasa ki tayi har sai da na hau saman kujerun na hau gai da abokin Abban Nusrah da ya kura min ido ya na Kare min kallo. Ku sha ruwa Mana"? Matar sa tace dan suna Zama aka cika gaban mu da kayan ciye ciye ni dai tunda na zauna na rasa nutsuwa ta buri na kawai mu bar gidan. Kaina a sunkuye naji Abban Nusrah na fada mi shi kawoni yayi na masa godiyar alherin da ya Masa. A lokacin matar ta koma sama haka ne yasa na sauko daga Kan kujeran na hau Masa godiya cikin murmushi daya bayyana hakoran makkar sa yace "ba komai uwargida baxan iya biyan Kabiru alherin sa a gareni ba dan ya taimaka min sosai sabida ni maraya ne,abincinsa haka zai kawo mu raba dan na taimaka Masa ba wani Abu bane". Godiya na Kara Masa yace ba komai ya Kara da "akwai wani gida da nake so na bar masa kyauta dan yace min gidan da kuke ciki ba naku bane haya ne,dan haka a satin nan ku fara shirye shiryen komawa na bar muku gidan halak malak,sannan zan d'auke shi aiki a company na zaa na biyan sa albashi miliyan daya kowane wata" Tunda ya fara magana na saki baki Ina kallon sa dan gabad'aya ji nayi na girgiza da Abubuwan da yace zai yi mana. Kamar an like min baki haka na ringa kallon sa Abban Nusrah kuwa sai godiya yake zuba Masa Yana ba komai. Sai da Abban Nusrah ya kalleni na iya bud'e bakina Nima na hau masa godiya. Ko da mu ka zo tafiya kudi ya d'auko Mai yawa ya miko min nak'i karba dan wlh wani irin tsoro naji ya Kara rufeni Kuma gabana bai bar fad'uwa ba idan dai na hada ido dashi. Sai da muka fito na daga palon na fara samun nutsuwa nayi gaba na bar su a baya. Kabiru Yana ganin Sajeeda tayi gaba ya kalli Alhaji Rabiu yana "Kasan idan ba haka muka yi ba wlh haka zata tayi min tambayoyi" "Nasan fa irin su haka sakeena ke da wanan taurin Kan,yanzu abinda za'ayi kayi k'ok'ari jibi ku koma gidan sabida ka fara aiwatar da abinda aka saka ka" "Ba zamu wuce jibi ba" Daga haka su ka yi sallama. Sajeeda Har muka isa gida Sam ban ji zuciyata ta kwanta da wanan sauyin rayuwar da muke neman samu ba hakane yasa sai da muka zo kwanciya nace "Abban Nusrah bansan Mai yasa hankali na bai kwanta da wanan canjin da muke neman samu ba,taya haka kawai zai d'auko gida sukutum guda ya mallaka ma dan kawai ka taimaka Masa Kuna Yara Anya mutumin nan ba dan yankan Kai bane?wane irin aiki zaka Masa da zai d'auko har miliyan daya ya baka a wata"a gaskiya!! Wani irin tsawa ya daka min daya tilasta min yin shiru"Sajeeda dama bakya san na cigaba a rayuwata? kinfi so na dawwama a haka a talauci kina jinki kamar mai gidan tunda ke kike yin komai a gidan,kinfi so na zama kamar yaron ki ko? bakya so kiga na samu na kaina Toh bari kiji na fada Miki da hannu biyu Zan karbi arzikin da ya tunkaroni idan Kinga bazaki iya ba sai kisan nayi" Daga haka yaja dogon tsaki ya juya min baya. Ko da na hau bashi hakuri inaso na fahimtar dashi nufina ko ta kaina bai bi ba. A haka na kwanta a gefen sa ina sake sake da bacci barawo kuwa ya daukeni na hau Mafarki da Kabiru da abokin sa Mafarki........ MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4k Mg's beauty kit 14k Herbal whitening soap Body cream Face cream Scrub Cleanser Glow oil Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Team glow😍 *RUFAFFEN SIRRI* *NA SADNAF* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *Page 4* Mafarki A kwancen da nake naji motsin bud'e k'ofar dakina hakane yasa na bud'e idona sai naga abokin Abban

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});