Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

*Page 5* Hankalin sa a tashe ya kashe kyandir din ya rarumo rigar sa ya saka hankalin sa idan yayi dubu ya tashi dan a sharadun da aka bashi har da Kar ya sake ya yarda a gan shi idan har aka gan shi da matsala. Tukunyar kasar ya d'auka yaje ya ajiye a d'akin da ya ajiye duka Abubuwan da aka bashi akan yayi amfani dasu,dan kafin su dawo gidan duk Suka kawo Abubuwan su musamman Suka ware d'akin ta bayan gidan. Yana rufo k'ofar d'akin. Ya nufo wajen window cikin sand'a addua kawai yake Allah yasa ba ganin sa Yesmeen tayi ba dan kamar daga dakin ta ya jiyo karar faduwar abu. Fuskar sa ya Kara a window ya hau lek'a d'akin sai dai ba abinda yake iya hango wa. Jiki a sanyaye ya koma ciki sai daya je har k'ofar d'akin Yesmeen ya Kara kunnensa yaji ko zai ji motsin ta sai dai har ya karaci tsayuwar sa bai ji motsin komai ba. Addua kawai yake Allah yasa ba ganin sa akayi ba dan yasan da matsala. Jiki ba kwari ya nufi d'akin su Yana tura k'ofar d'akin yaci Karo da Sajeeda tana ganin shi ta Kankame shi tana sauke numfashi. Ture ta yayi daga jikin sa dan yasan yanzu zata ce mafarki tayi Kara ruko shi tayi jikinta na rawa ta fara kuka tana "Abban Nusrah akwai matsala wanan mafarkin da nake ba haka kawai bane Mafarki iri daya sau uku Abban Nusrah wlh wanan abokin naka bana Jin mutumin arziki ne" Wani irin tsawa ya daka mata idon sa jawur dan yanzu sam ba'a hayyacin sa yake ba abinda aka ce yayi a yau har da wankan bai samu yayi ba fada ya rufeta dashi akan daga yau Kar ta Kara fada masa tayi mafarki ya gaji da halin ta idan ba za ta zauna dashi ta bar masa gida. Yaja dogon tsaki ya kwanta ya bar Sajeeda da jikin ta ke Karkarwa saboda tsoron mafarkin da tayi na yau ya da tayi ya munana dan har yanzu zafi take ji a gaban ta kamar a gaske,dan mafarki tayi abokin Abban Nusrah ya zura mata hannu a gabanta ya Ciro abu tana ta ihu, tsoro yasa ta kwanta a bayan Kabiru ta Kankame jikinta tare da rufe fuskarta. Allah yasan Kabiru fin karfin ta kawai yayi amma jikin ta na gaya Mata akwai wani abu game da Abokin nan nasa ba abanza take mafarki dashi ba daga ranar da ta fara zuwa gidan sa ta ga Yana ta kura Mata ido ya zama dole ta tashi tsaye da Addu'a. A haka tayi zuru har aka Kira sallah Asuba da yake tana fashin sallah sai ta Shiga bandaki ta gyara jikinta ta canja pad dinta ta saka Wanda ta cire a leda da zumar idan gari ya waye sai ta Kai bola dan haka take yi daga lokacin da take flushing din pad ya toshe pipe din ruwa ya daina tafiya ta daina sakawa a toilet. Ko da ta fito daga bandakin kwanciyarta tayi Dan tasan sai Abban Nusrah yaga gari ya kusa wayewa yake tafiya massallaci abin na matukar bata mamaki. Tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita dan baccin take ji. Duk abinda take yi Kabiru na sane rufe idonsa kawai yayi sai da ya tabbatar da tayi nisa a bacci ya mik'e ya Shiga bandakin ya d'auke pad din dan Yana ta addua ta cire dan zai Kai ayi amfani dashi Yana d'auka yayi waje da sauri dan so yake yaje ya samu Rabiu,suje yaji ya ko aikin da aka sa shi yayi. Yesmeen Rik'e numfashin ta kawai tayi da rarrafe ta kwanta ta Kankame jikinta dake ta karkarwa ba abinda take gani a idon ta sai Kabiru da ta hango Zigidir Yana zagaye wuta,gani take kamar a mafarki tana jin takun tafiyar sa har zuwa lokacin da taji karar bud'e k'ofar da yayi Wanda hakan ke alamunta Mata da shigowa yayi,Jin motsin sa a bakin k'ofar d'akinta yasa taji Kamar ta saki fitsari saboda tsananin tsoro,ita dai tasan ba tabin hankali ta samu ba Wanda take yiwa kallon mahaifinta taga yayi tsirara Yana zagaye wuta,mai hakan nufi?Mai yake yi da tsakar dare da kowa ke bacci,duk yadda ta so ta gano ma'anar abinda yake yi kwakwalwar ta tak'i bata had'in kai, dan a iya sanin ta a film take ganin irin wanan tashin hankalin ta Kuma san Abban ba boka bane ba maye bane. Baccin da bata koma kenan ba ta Kankame jikinta tana Addu'a a zuciyarta sai take ganin kamar ma dai idon ta ne ya gane mata Abba amma bashi bane. Umman ta zata fadawa taga Abba da tsakar dare tsirara ko Saifullahi Ko dai Aljani ne da siffar Abban,amma dai taji motsin shigowar sa cikin gidan. Haka ta kwanta bata motsa ba sai da aka Kira sallah Asuba ta mik'e ta daura alwala duk ba'a nutse tayi sallahr ba sabida tunanin abinda ta gani. KABIRU Yana fitowa daga gidan ya hango motar Alhaji Rabiu a nesa da gidan dan dama sun yi akan za su hadu da sassafe dan shi ma zai je can wajen shugaban nasu. Yana Shiga cikin motar Rabiu yace "dafatan ka yi abinda shugaba ya saka Kuma ba'a samu kuskure ba"? "Jiya na fara yi na ji Kamar motsi ina tsoron ace ganina aka yi ko wankan ban samu nayi ba" "Ya za'ayi a gan ka ba karfe biyun ka tashi ba"? "Karfe biyu na tashi wlh motsi naji Wai dole a gida zan yi Abubuwan nan ba zan iya yi a wani wajen ba"? "Aikuwa dole a gida zaka yi Kuma indai an gan ka wallahi da matsala ka samo jinin nata"? "Eee gashi nan a Aljihu na" "Tom bari mu karasa,tunda tak'i bamu hadin kai ayi ta baya kaga kuwa Dole a biyo mata ta bayan gida" "Kasan me ke damuna wai tana yawan mafarki dakai abin na damuna dan har ta fara nuna min Kamar kudin da kake bani bana halal bane tana da saurin gano abu fa Ina tsoro asirina ya tonu da Wanan mafarkin da take" "Ni mai hadina da ita da za ta yi mafarki dani ai da Kai ya Kamata tayi mafarki bani ba" A haka suka cigaba da hira har Suka karasa wajen. Ta baya Suka Shiga d'akin da shugaban nasu ke zaune kafin su karasa su zauna shugaban ya daka musu tsawa Yana "ku dakata!! Cak suka tsaya Cikin wani irin murya shugaban nasu ya taso da kana masa kallo daya sai gaban ka ya Fadi a d'akin da yake har da kwarangwal din kawunan mutane cikin wani irin murya yace "Rabiu abokin ka jiya ya bata min aiki dan ya bari an gan shi" Ido Kabiru ya zaro ba dama yayi sallati cikin tashin hankali yace "Shugaba waye ya gani" Akwai yarinyar da ta gan ka Kuma kasan ka'idan aikinmu indai wani ya ganmu sai mun d'au mataki dan bazamu so ta tonawa wani sirrin mu ba" Gaban Kabiru ne ya yanke ya Fadi dan Yana tsoron matakin da zaa d'auka akan Yesmeen dan ya gano itace ta gan shi dan ita kadai ce mace a gidan. "A cikin abu uku dole ayi daya

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});