Chapter 3
Chapter 3
saurin dakatar dashi yana "Rabiu Ina kaunar matata tunda na yarda zan yi harkar nan zuciyata take cike da fargaba da tsoro ko bacci bana iya yi dan Allah muje wajen shugaba ka fada masa ya duba min ko zan iya yi da wata na samu biyan bukatata ba sai Sajeeda ba. "Ikon Allah toh wa zaka samo"? "Akwai yar kanwarta da nake rike da ita da ita nake so na samu biyan bukatar tawa" "Bani da ta cewa muje daga can muji ko zai yu...... Hmmm *RUFAFFEN SIRRI* *NA SADNAF* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *Page 2* Kabiru har suka je Suka dawo bai iya magana ba sabida kasan zuciyarsa cike take da tsoro,ji yake Kamar ba zai iya ba dokokin da Abubuwan da akace yayi sun masa yawa da tsauri,a hankali ya Kai dubansa wajen Alhaji Rabiu da ya kasance abokinsa tun primary da a lokacin ya fi shi k'ok'ari nesa ba kusa ba dan shi yake zuwa na karshe ma a ajinsu da kuwa suka gama primary bai Kara saka shi a idonsa ba,bai Kara jin labarin sa ba sai a shekara biyu da suka wuce ya had'u dashi,sai da yayi da gaske ya gane shi sabida yanda ya dawo fari kal sabida yadda hutu da Jin dadi suka zauna masa tashin farko,kyautar dubu dari ya Masa,ya hada da bashi lambarsa,duk kalar rayuwar da yaso tun Yana karami na rayuwar Jin dadi shi yake gani a wajen Rabiu. Gashi ya girma zai iya cewa ya d'auko tsufa tunda Yana dab da aurar da 'yar cikin sa duk bai samu cikar burin nasa ba. Tuni yaji ya kwadaitu da san yayi kudin fiye ma da da hakane yasa ya makalewa Alhaji Rabiu ko zai taimaka Masa ya sama mi shi aiki irin nashi da shi ma zai samu kudin. A haka Alhaji Rabiu ya ringa masa yawo da hankali Yana kasuwanci yake yi sai da yayi dagaske Rabiu ya fito ya nuna masa ta hanyar da ya samu kudin sa,idan har yaga zai iya. Tsayuwar motar Alhaji Rabiu a wani tamfatsatsen gidansa da matarsa ta uku take ciki ya katse tunanin da Kabiru ya tafi. Yayi horn Mai gadi ya bud'e masa. Tun da suka shiga gidan Kabiru ya saki baki da hanci Yana kallon Aljannar duniya,maganar shugaba na dawo Masa a kunne,"zaka yi kudi, idan nace ma kudi,Ina nufin kazamin kudin da zai saka duniya ta san ka zaka ji dadin rayuwar ka zaka bar wa yayanka tarin dukiya ka tabbata baka tsallake duk sharuddan da aka gindaya ma ba daga yanzu kafin wata ukun zaka fara dandana arziki amma ka iya takun ka" "Sauko mu Shiga daga ciki ka gaisa da Aseeya" Muryar Alhaji Rabiu ya katse Masa tunanin da yake. "Rabiu anya zan iya wlh bansan mai yasa nake Jin bazan iya ba gani nake za'a iya gano ni da wuri bazan iya yiwa Sajeeda haka ba" Murmushi Alhaji Rabiu ya saki Yana "Tunda na iya yiwa Sakeena Yar uwata haka Kai ma zaka iya bafa kasheta zaka yi ba,a cikin kankanin lokaci Kai ma zaka zama kamar ni,kayi amfani da abinda kake dashi ka samu cikar burin ka,kar ka karaya abokina muje dai daga ciki indai Muka bi komai a yanda Muka tsara wlh baza'a samu matsala ba" Kabiru gyada Kai yayi duk da a kasan zuciyarsa gani yake bazai iya ba. Yabi bayan Alhaji Rabiu yana karewa gidan kallo,hararo kansa kawai yake a matsayin Rabiun ya mallaki irin wanan gidan,ya ginawa su Saifullahi manya manyan gida daidai da Nusrah ma sai ya mallaka Mata gida da mota, tuni yaji ya Kara kwadaituwa da ya samu kudin,a lokacin da suka Shiga palon da Kamar a kasar waje suke da suka shiga. A lokacin kuwa daya zauna kalle kalle ya cigaba da yi Alhaji Rabiu ya haye Sama minti biyar a tsakani sai gashi ya sauko ya zauna. Kafin kace me masu aiki sun cika gabansu da kayan ciye ciye. Alhaji Rabiu kuwa sai murmushi yake dayaga yanda Kabiru ke hadiyar yawu. Takun takalmin Aseeya matar Alhaji Rabiu dake saukowa daga saman benen yasa Kabiru maida hankalin sa wajen benen. Yarinya ce bata fi saar Nusrah Yar sa ba ko zata girmi Nusrah bazai fi da shekara biyu ba,kyakyawa ce ta ajin karshe tamkar ita tayi kanta fuskarta d'auke da murmushi,har ta karaso gefen Alhaji Rabiu ta zauna ta fara gaida Kabiru da ya hau washe baki kasan ransa Yana ta mamakin yanda yarinya karama ta yarda ta auri sa'an mahaifinta. Bayan sun gama gaisawa ta mik'e ta koma sama, "Rabiu yanzu Wanan Yar yarinyar ka Aura"? Murmushi Alhaji Rabiu ya saki ya zuba Lemo a kofi sai da ya kurba ya ajiye ya kalli Kabiru Yana "Shekara uku kenan da Auren mu Kuma ta wajen nan da matarka ta hana ka ta wajen nake neman ta" Ido Kabiru ya zaro waje Yana "Kuma sai ta yarda"? "Kwarai kuwa ba Ina da kudi ba,a yanzu da kake ganin ta bama tasan Inda zata Kai kudi ba kaga kuwa ko dan su dole ta yarda da bukatata dan sai da na tabbata Iyayenta irin talakawan nan ne sosai,dan a garin talla ma na hadu da ita,na cikata da kudi na cika Iyayenta da kudi, basu da gidan kansu kafin na aureta yanzu kuwa har yayyenta maza ba Wanda ban siyawa gida ba tana morata a zahiri Ina morarta a badini" Sai yayi kasa da murya "Tana samun ciki take b'ari na riga na bada mahaifarta" Ni kuwa Ina nan da yayana bakwai suna jin dadin su a waje" Kabiru mamaki ya sa ya kasa ma magana dan sai a yanzu ya gane da rabon amaryar kudin sa ke Kara hab'aka uwar yayan sa kuma ta masa silar kudin. "Rabiu dama nima na auri wata ta zama silar kudin bana so na tab'a uwar Yayana da mu ka Sha wahala tare da ya Kamata ace a yanzu taji dadina shugaba ya bani wata uku ya bani Abubuwan da zanyi har zuwa matakin karshe,tunda Muka baro wajensa wlh jikina a sanyaye yake gani nake bazan iya ba" Wani irin mugun kallo Rabiu yabi Kabiru da shi yana "Ka ga idan baza ka iya ba ka tashi ka bar min gida ka Kuma dawomin da kudadena da na baka,kudin nan idan kayi ni zaka bawa ko me ana ta nuna ma hanyar arziki kana baudewa,duk uban wahalar nan da ka ringa bani dama baka tsayar da zuciyar ka ba abu kad'an sai kace baza ka iya ba dalla tashi ka bar min gida kasan Kuma baa yiwa kungiya haka indai ka fasa wlh sai an tab'a ka" "Ba abinda nake nufi ba kenan Rabiu ba fasawa zanyi ba sharrudan yanzu sunfi bani tsoro ina tsoron na kuskure a samu matsala" "Ka kwantar da hankalin ka kasa a ran ka zaka iya Sajeeda da kake ta fadi ba fa kasheta zaka yi ba balle,dadin ma da ita za'aji gefe guda Kuma idan an kwana biyu zaka iya auren Mata uku kayi ta more rayuwar ka abokina kana Jin dadi,yayanka ka gan su fes,ni kasan gabad'aya yarana suna kasar waje,shawara daya dai Zan baka duk yanda muka tsara ka bi zaka Sha mamaki kila.ma.ka fini himma wajen bada abin arziki kudi suyi ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111