Chapter 92
Chapter 92
sai ka rantse min ba wallahi ko duk duniya zasu taru su ce kudinka ba na halal bane sai Inda karfina ya kare wajen Kare maka mutuncinka ni nasan ba yadda zaka tab'a haka,shi yasa na cewa Nusrah Kar ta sake ta fadawa kowa wanan maganar abinda za'ayi yanzu zan koma na Kara kwantar mata da hankali gobe da sassafe zan dawo kawai na cigaba da kula da Sajeeda dazu Gwaggo ta kirani Wai Asmau tazo Abuja wai har yanzu bata iso ba"? "Banganta ba da yake kinsan na fita da na dawo Kuma banganta ba yanzu ma Tasha zanje na dubata,gashi Yesmeen yanzu ta kara kunna min wani wutan" "Karka damu fa wallahi yanzu nan zan tsara Nusrah na gwada mata sharrin Yesmeen ta maka dan ta maka sata ka Kamata shine ta zuba maka wanan sharrin" "Ki taimaka min Yaya Abu ki koma Kar Nusrah ta sake Kiran wani ta fada Masa kinsan Yara ne su zasu iya yarda" "Ba matsala in Sha Allah ka taimaka ka Nemo Mana yarinya nan nasan tana cikin Abuja ba inda ta sani ba Kuma tasan hanya ba ka nemota ka daure Mana ita" "Zan nemota Yaya Abu ngd da Kika yarda dani, zan miki gaggarumin kyauta in Sha Allah da wata ce ba lailai ta yarda dani ba" "Kai haba wallahi na yarda da Kai karka damu bari na koma gidan,yanzu dai dole na taho gobe tunda akwai su larai a gidan,sai su cigaba da kula da Nusrah idan anyi suna sai su dawo gabad'aya" "Toh Yaya Abu ngd dan Allah duk yadda kika yi da Nusrah sai ki kirani ki fada min" Daga haka Kabiru ya kashe wayar ya dora kansa akan steering Yana "Rabiu ban Shiga kungiyar nan a saa ba,tunda na Shiga nake cikin tashin hankali yanzu idan Nusrah ta kira wani fa ta fada masa"? Kaja motar nan mu tafi wajen shugaba ya mana aikin da zaa rufe bakin yesmeen din a rufe bakin koma waye,duk matsalar nan Kai ka jefa kanka a ciki,da ka yarda ka bada wadatacen jini da yanzu duk baka tsinci kanka a wanan halin ba har yaushe ka Shiga kungiya da zaka fara nadama,kasan Allah ka bada jinin wanan matar ka huta yanzu shugaba duk zai kau ma da matsalar ka,Kai wallahi ko da duk duniya sun gano abinda kake ciki,zai maka aikin da zaa rufe bakin kowa,yanzu amfanin mai take maka ka bada jininta idan an kwana biyu sai ka samo matashiya ka aura,idan ka kwashe arzikin ta sai ka saketa ka Kara auren wata kamar dai yadda nake yi" " Bazan iya ba Rabiu wallahi bazan iya kashe Sajeeda ba,ko amfani da nayi da ita wallahi ba'a san raina bane Amma muje ya dubo min inda yarinya nan ta Shiga wallahi ita zan bayar idan ma da kaina yake so nayi ferfesun ta yi zanyi,Sajeeda ma ba sai na kaita can ba tunda ba magana take ba ko Yesmeen ta fada mata ba bakin da zata fadawa kowa, asibti zamu fara kaita inyaso idan an fara dubata sai mu wuce wajen shugaban" Kabiru kenan da barin ta da kayi a raye tana Shan wanan wahalar ba gwara kawai ka karasata ba" "Bazan iya ba Rabiu Kai karasa Ateeka kayi ba adaki ka killace ta ba mai ya hana kai ka karasata ko ba amfanin da take min inaso na ganta a raye" Daga haka Kabiru ya tada motar a madadin yayi hanyar wajen shugaban ya d'auki hanyar asibiti,dan tsoro ma yake ji shugaba yaga Sajeeda yace ya kawo jininta, yafi so ya bada jinin Yesmeen. Nusrah Tunda Yaya Abu ta fita ta kwanta tana ta kuka,sai a yanzu komai ya ringa dawo mata,dan yadda Kabiru yayi arzikin dare daya dole a dasa Masa ayar tambaya,sai a yanzu ta tuna kalmar Sajeeda da tace mata "Nusrah Abban ku ya kasheni" Ashe maganar da take so tayi mata kenan inama ma ta matsa mata a lokacin ta fada Mata,dama duk tsawon lokacin nan Yesmeen tasan irin wanan maganar amma ta boye mata,ko dan Sajeeda ba mahaifiyar ta bace shi yasa taki fadawa kowa Kabiru ya cigaba cutar musu da uwa, Mik'ewa tayi Kamar an tsikareta ta d'auko wayarta da taji Yana ta ringing ganin lambar da Yesmeen ta kirata dashi ne yasa ta dauka cikin ihun kuka ta fara magana tana "Allah ya isa tsakanin mu dake Yesmeen,duk tsawon lokacin nan kinsan dama abinda yake damun Umma baki tab'a fadawa kowa ba,ko bazaki fada wa kowa ba ai ya Kamata ki fadamin ko dan umma ba mahaifiyar ki bace, shi yasa Kika barta duk tsawon lokacin nan a kwance Muka rasa sanin wane irin cuta ne yake damunta, tun kafin ku bar garin nan Yesmeen kinsan Abba ya cutar da umma a madadin ki fada da wuri,mu ceto umma amma kikayi shiru Yesmeen wallahi idan Abba ya Kara cutar da Umma bazan tab'a yafe Miki ba wallahi kinfi abba mugunta har kuka koma Abuja su Saifullahi sun dade kafin su tafi baki fada musu ba yesmeen kece ma kika kashe umma ba Abba ba,kina tunanin da ace yau mahaifiyar ki na raye naga abinda zai cutar da ita bazan taimaka Mata ta hanyar fadawa mutane su Kai Mata agaji ba" "Ya isa haka Nusrah ki barni nayi miki magana Mana ki saurareni mana, Abba ya wuce duk Inda kike tunani yanzu ba lokacin da zaki Tsaya ganin laifina bane,ki kirawo Gwaggo ki fada mata halin da ake ciki,mama bakinta daya da Abba wallahi itama so take ta kashe umma sau uku tana gwada saka wa umma guba a abinci,idan kika fada Mata wallahi ba abinda zatayi akai kiyi sauri ki kira Gwaggo Nusrah" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Yesmeen Allah ya tsine Miki albarka duk kinsan wanan masifar baki fadamin ba sai da na tura mama wajen Umma idan har wani abu ya samu umma wallahi bazan yafe miki ba muguwa azzaluma" Nusrah da jikinta ke balain rawa ta kashe wayar tana jin numfashinta na neman d'aukewa. Hannunta rawa kawai yake ta nemo lambar Saifullahi na waje da yake yawan kiranta dashi,sai da ta Masa miscall uku a na hudu ya dauka,tana Jin muryarsa ta saka ihu tana "Saifullahi Abba ya kashe umma, Ashe Abba kudinsa bana halal bane ashe Abba shine silar jefa umma a halin da take ciki" "Bangane ba Aunty Nusrah mai ke faruwa ne kimin bayani yadda Zan gane" Nusrah labarin da Yesmeen ta bata duk ta kwashe ta fada masa ta Kara da "wanan wane irin balai ne, akan kudi Abba ya kassara rayuwar Umma,ga itama yayarta itama farautar ranta take mai umma ta musu da zafi haka Yesmeen ta cucemu wallahi idan har mama ko Abba Suka cutar da ita bazan tab'a yafe Mata ba Saifullahi yanzu mai abin yi banida lafiya ya za'ayi mu ceto umma bana so mijina yasan halin da ake ciki" "Zan kiraki yanzu Ina zuwa" Kiit taji Saifullahi ya kashe wayar a daidai lokacin da Yaya Abu ta turo k'ofar ta shigo ta zuba mata ido tana kallonta ta kasa yarda wai yayar mahaifiyar ta ke san kashe ta" Yaya Abu kuwa jakar hannunta ta fara k'ok'arin ajiyewa tana "Nusrah wai kuka kike har yanzu ki daina kuka haka wallahi karyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111