Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Nusrah ya shigo da Jan zani daure a kugun sa hannun sa rik'e da tukunyar kasa,sai na Mik'e da sauri cikin tsananin tsoro na fara kwallawa Abban Nusrah Kira akan ya tashi,dan ba iya abokin nasa ne ya shigo ba har da wasu a bayan sa suma da tukunyar kasa a hannun su,ihu nake iya karfina na kasa d'auke idona daga kansu na Kai hannu na dan na tashi Abban Nusrah sai na ji baya gefe na har suka zagaye gadon da na ke kwance na cigaba da ihu Abokin Abban Nusrah ya fusgoni da k'arfi ya Kai hannun sa wajen zani na, na saka ihu!" A daidai lokacin da naji an rik'e ni ana girgiza ni na bud'e ido na da sauri tare da mik'ewa zaune kirjina na dukan uku uku a lokacin da na farka na ga ashe mafarki nake duk na jike da gumi,na Kankame Abban Nusrah da ya rik'e ni gam yana "lafiyarki kuwa"? "Mafarki nayi Abban Nusrah innalillahi wa Inna ilaihi rajiun innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Na cigaba da sallati Ina kallon k'ofar dakin mu dake rufe dan sai nake ganin kamar ba mafarki nake ba "Kiyi Addu'a ki koma ki kwanta" "Abban Nusrah mafarkin abokin ka nayi" "Gwara da ki ka ce mafarki ba gaske ba ki koma bacci dan Allah" Ya fara k'ok'arin cire ni daga jikin sa na Kara Kankame shi mu ka kwanta ahaka. Mafarkin da nayi na nan daram a idona,ko kad'an ban runtsa ba dan gani nake ko Yaya na rufe ido zan ga sun shigo bansan Mai yasa nayi mafarki da abokin Abban Nusrah ba,Mai ma'anar wanan mafarkin da nayi. Idona biyu har aka Kira sallah Asuba na tashi na daura alwala Abban Nusrah kuwa sai sakin munshari yake,a yanzu baya sallah akan lokaci sai nayi ta tashin sa kafin ya tafi massallaci. Duk tashin da na masa bai tashi ba da na dame shi ma tsawa ya daka min hakane yasa na rabu dashi nayi Sallah ta ina ta mamakin canjin da nake gani a tare dashi,sai Kuma na tuna wai abokinsa yace zamu bar gidanan take naji wani irin tsoro da fargaba ya rufeni da na tuna mafarkin da nayi dashi,jikina na gaya min mutumin nan baa a banza zai taimake mu ba bansan mai yasa jinina bai d'auke shi ba ko dan na saka shi a raina shi ya sa nayi irin wanan mafarkin dashi. Har na fito Muka hada abincin karyawa da Yesmeen zuciyata cike take da tunani har sai da Yesmeen tayi ta tambaya ta mai ke damuna nace mata ba komai. Karfe tara da rabi su Saifullahi suka shigo dan su karya fuskar su a washe,Annur kuwa ya zauna a gefe na bayan duk sun gaisheni yace "Umma nifa yanzu kullum sai nayi mafarki Abba yayi kudi" Da sauri na daga masa hannu Ina "ka ringa mana Addu'ar idan alheri ne kudin Allah ya tabbatar mana" "Ai yama tabbatar in Sha Allah yaro babban ka ya zama Mai kudi,Umman ka ke so mu cigaba da zama a talauce ba cigaba" Naji maganar Abban Nusrah a baya na na waiga Ina kallon sa a daidai lokacin da ya iso gefena ya zauna fuskar sa d'auke da murmushi Yana amsa gaisuwar da suke Masa. Ya janyo faranti ya fara zuba dankali yana cigaba da magana "Saifullahi Kai da Faisal yanzu idan muka gama karyawa zamu je ku rakani gidan da abokina ya bar min kyauta nasan zaku ga kwana biyu na dan samu kudi,wani aminina ne tun muna primary Allah ya hada ni dashi Mai kudine sosai hakane yasa yace zai taimaka min yanzu haka jiya nida mahaifiyar ku mun je jiya ta masa godiya ba iya kyautar gida kawai yace zai min ba har aiki zai bani a companyn sa zaa ringa biyana miliyan daya duk wata" Ihu Suka saka gabad'aya suka hau murna har da tsalle Yesmeen itama sai murna take "Abba yanzu kana nufin sabon gida zamu koma Wanda yafi wanan"? Saifullahi yace cikin tsananin murna da farinciki "Sabon gida zamu koma ai zamuje kuga gidan daga nan ma sai muje ku masa godiya" Murna kawai suke Yesmeen kuwa jiki na rawa ta d'auko wayarta ta Kira Nusrah ta hau labarta mata naji itama ta saki ihu ta cikin waya tana zata zo gidan. Nidai da ido kawai na ringa bin su banji Ina murna ba na rasa dalili hakika cigaba ne yazo mana Wanda ban tab'a tunani ko mafarkin sa ba amma na rasa mai yasa naji a madadin naji ni cikin Farin ciki nake Jin akasin haka har ga Allah bana san mu bar gidanan abokin Abban Nusrah sam bai kwanta min ba Ina addua Allah yasa tarayyar su ya zame Mana alheri. Yaran ko ta kaina basu Kara bi ba suka yi waje duuu dan Abban Nusrah ma cewa yayi duk suzo su tafi suga gidan. Basu dawo gidan ba sai wajen laasar bakin su Kamar gonar auduga sai labarta mun kyaun gidan suke da haduwar sa ,suka d'auko Dubu hamsin suka bani akan abokin Abban su ne ya basu kyauta,sai fadar kirkin shi suke suna murna wai Abban su ya zama Mai kudi nidai ban iya ce komai ba sai dai sake sake a zuciya dan ban samu fuskar ma da zanyi wata magana ba. Sai da muka zo kwanciya Naga na kasa jurewa dan Abban Nusrah cemin yayi a gobe goben nan zamu tashi mu bar gidan Kuma baza mu dau komai ba dan akwai komai a gidan Duk da nasan magana ta zata b'ata masa rai haka na daure na fara magana Ina "Abban Nusrah daga haduwar ka da abokin nan naka ina ga ko sati ba'ayi ba har a cikin Yan kwanakin nan ya maka irin wanan alherin har dasu kyautar gida Abban Nusrah Kar idon mu ya rufe ya Kamata muyi bincike a kansa kafin mu koma gidan da ya bamu,ya Kamata mu tabbatar da irin sana'ar da yake yi saboda mu samu kwanciyar hankali wlh zuciyata bata dauki wanan abokin naka ba tsoro nake ji Kar ya zama bata hanyar halak yake samun kudin sa ba Abban Nusrah" "Ya isa haka Sajeeda na fada miki Mai kudine Yana harkar Mai Kuma babban dan kasuwane bansan sau nawa kike so na fada Miki ba, ya za'ayi cigaba ya zo mana har gida ki tsaya kina wani kananan zance an gaya Miki banyi bincike akan sa ba Mai kudine na fada miki dan haka idan Zaki saki jikinki mu ci arziki toh idan bazaki saki ba wanan matsalar ki ce" Yaja dogon tsaki ya kwanta tare da juya min baya "Allah ya baka hakuri Abban Nusrah ai bansan kayi bincike akan sa ba Allah yasa mu koma gidan a saa" "Ameen" Kawai yace ya Kara Jan bargon saman kansa. Wlh a ranar sai naji na kasa bacci kallon dakina dana kwashe shekaru a ciki kawai nake sau uku Abban Nusrah na farkawa ya leka fuskata idan yaga idona biyu sai ya koma ya kwanta yaja tsaki ana hud'u da ya leka fuskata muka hada ido sai ya Kara Jan tsaki Yana "Wai me kike yi baki yi bacci ba"? "Bana Jin baccin ne Abban Nusrah Ina ta jimamin yadda zamu tashi mu bar

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});