Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,225 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

alheri a wajen aikin sa Yana tunanin ma zai fara gini A Abuja" Ni dai Jin sa kawai nake dan ni kadai nasan me nake ji a jikina a yanzu ma kaikaiyi nake ji sama sama sai naji kamar abu ya zubo. A haka na kwanta ni ba bacci ba ni ba Ido biyu ba,wajen uku dai bacci ya daukeni sai na hau mafarki Abban Nusrah ya Kai mu wani gidan bene wai gidansa ne nazo shiga na fada wani Rami dake gaban gidan,sai na hau ihu Ina mikawa Abban Nusrah hannu akan ya taimaka min na fito,a madadin ya taimaka min sai ya hau watso min kasa. Ihu nake da iya karfina amma ba mai jina sai da ya kusa gama rufeni da kasa na farka a gigice Ina sallati nabi na hada zufa,a hankali na kalli wajen da Abban Nusrah ke kwance naga baccin sa kawai yake har da munshari,a hankali na Kara tuno mafarkin da nayi Ina wane irin mafarki ne wanan Jina da nayi a jike kamar wacce tayi fitsarin kwance yasa na Kai hannu na shafa wajen da nake kwancen naji a jike,cikin mamaki na fara k'ok'arin mik'ewa tsaye Dan kamar dai fitsarin nayi,yadda naga zanin jikina a jike. Koda na cire zanin na Kai hannu jikina na shafa ruwan na Kai hancina dan na shinshina naji ko dai fitsarin nayi kasan zuciyata kuwa sallati kawai nake ko da na Kai hannu hancina wani irin wari naji nayi saurin cire hannuna hankalina a balain tashe "Wanan ruwan daga ina"? Na tambayi kaina Ina cire wandon jikina gabad'aya na Kara Kai wandon hancina naji wani irin wari Kamar gurbatacen kwai ya daki hancina na wurgar da wandon jikina na d'aukar rawa mai ke Shirin faruwa dani haka?wane irin ruwa ne wanan yake fitowa a jikina. Kuka na rushe dashi daya saka Abban Nusrah tashi a firgice Yana "Sajeedaa lafiya Mai ya faru"? "Abban Nusrah na Shiga uku na lalace kaga ruwa mai doyi ke fita a jikina innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Na Kara rushewa da ihun kuka Ya taso daga kwancen da yake ya zagayo wajen da nake tsaye Yana "wane irin ruwa Kuma Sajeeda"? "Farkawa nayi daga bacci najini a jike,kaga wajen da na kwanta Abban Nusrah kaga zanina mai ke Shirin faruwa dani Abban Nusrah tunda jiya nake Jin wani iri a jikina Abban Nusrah,tun jiya da ka kusanceni ban Kara jina daidai ba" "Bangane baki Kara jinki daidai ba Mai kike nufi?watakila infection ne dake ki kwantar da hankalin ki gobe da safe sai mu koma asibiti kije bandakin ki gyara jikinki" "A Ina zan samo infection Abban Nusrah idan ba kai ne ka saka min infection ba a ina zan samo" "Ta Ina Zan saka miki nima ki daina kukan nan kije bandaki ki gyara jikin ki gobe idan muka je asibiti sai muji Mai ya kawo Miki farin ruwan" Kuka kawai nake da iya karfina Gwara kowane rashin lafiya da wanan masifar dake neman Samuna,Taya ruwa zai ringa zubo min Mai wari, tunda nake a rayuwa ko discharge ban taba ba,amma dare daya na tashi ruwa na zubomin mai wari,nan ko maganin Mata indai na matsi ne bana amfani dashi saboda tsoro. Idan har ba Abban Nusrah ne ya kwaso wani abun yazo ya saka min ba Kuma iya sanina ba maneman Mata bane sai dai idan Wanan tsinanne abokin nasa ne zai dora shi a hanya mara kyau. Baccin da ban koma ba kenan na Shiga bandaki na wanke jikina da ruwan dumi da Dettol na samo sabon pant na saka,wanan tashin hankalin da na tsinci Kaina a ciki ya d'auke min tunanin mafarkin da nayi. Sai da nayi Sallah Asuba bacci ya daukeni. Yesmeen Bata wani samu baccin kirki ba dan gani take tana kwanciya Kabiru zai iya shigowa d'akin,a duniya ba Wanda take tsoro sama da Kabiru,a jiya sau uku tana taka abu dan ta cire glass din fitilar d'akin ta tsoro na hanata tasan akwai abu a cikin fitilar, mafarkin da tayi da ta kunna wutar d'akin ta hau ihun idonta ya tsaya Mata a zuciya,sai ta tafi tunanin yadda Annur ya kurmance tasan ita Kabiru ya so ta kurmance Allah ya tsallakar da ita,shine ya Kara biyo wa ta wanan hanyar dan ya makantar da ita tunda tasan sirrinsa sau uku tana mafarki iri daya ta kunna fitilar ta makance,bata mafarki a banza dan Sajeeda ma hanata take ta Fadi mafarkin da tayi,dan Haka ma mahaifiyar ta take indai tayi mafarki sai ya tabbata saboda ance tana da Aljannu,shiyasa da aka gano itama in tayi mafarkin tabbata yake aka hanata fadar mafarki saboda Kar a fassarata. Tasan da akwai matsala indai ta kunna fitilar d'akin Koda ta iddar da Sallah asuba bata koma bacci ba azkar kawai ta ringa yi zuciyarta na wajen Sajeeda rabin adduata akan Sajeeda ne, Karfe shidda ta fito daga daki dan ta fara aikace aikacen da ta saba dan su koma hutun makaranta tana ss2 a yanzu. Yau gabadaya bata ji motsin Kabiru ba. Koda ta Gama share ko'ina Dustin bin din kitchen daya cika da shara ta d'auka dan taje ta zubar a a katon Dustin din dake wajen hanyar fita. Tana zuwa ta zubar da sharan muryar Kabiru da taji Yana magana a waje yasa ta tsaya cak kirjinta na bugawa da Jin ya ambaci sunanta. Hakane yasa ta Kara gyara tsayuwarta tana Jin Mai yake cewa,abinda taji yasa ta zaro ido jikinta na d'aukar rawa sallati kawai take a zuciyarta hankali a tashe ta koma cikin gidan ya shige daki ta hau safa da marwa in ta zauna bata tsira ba in ta gudu ma bata tsira ba dole tasan nayi kafin Kabiru ya samu cikar burinsa a kanta tuni taji bama zata iya zuwa makarantar ba. Tana Jin motsin Hamza da Annur Amma ta kasa fitowa. Jikinta rawa kawai yake har taji Kabiru ya shigo Yana tambayar su Hamza inda take ya hau kwalla mata Kira ta fito a guje. Ya daka mata tsawa akan ta hada wa su Hamza tea su Sha shayi su tafi makaranta. Jiki na rawa ta shige kitchen ta hau hada breakfast. Sajeeda Ban farka ba sai wajen goma da rabi na safe Koda na farka ba kowa a d'akin,Ina k'ok'arin mik'ewa tsaye naji wani irin kaikaiyi a gabana tuni na saka hannu na fara susa da na tuna ruwan daya zubo min jiya mai wari sai naji hankalina ya Kara tashi Ina cikin susa Abban Nusrah ya shigo da faranti a hannun sa. "Kin tashi"? Ban iya bashi amsa ba har ya zauna Hannuna a cikin zani Ina susa,wai jikin naki ne har yanzu" Tun dazu nake so na tashe ki ki karya na Kai ki asibiti a duba ki bansan Mai ya kawo Miki wanan ruwan ba" Karbi shayi ki sha da magungunan ki idan kin gama sai mu tafi. Bata abinci nake ba hakane yasa na girgiza Masa Kai akan bazan ci ba ya dage min akan sai na karya Koda na karya na shirya dan muje asibitin yayata Abu ce ta kirani akan suna hanya ita da yar kanwar babarmu Asmau sun kusa isowa. Hakane yasa na cire hijabina na koma na kwanta nace masa ya bari

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});