Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,223 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zub'e a kasa ta daga hannu tana "Ya Allah ka kareni daga sharrin Abba Allah ka dubi marainiyar ka da idon Rahama kar ka bashi ikon cutar dani" Ta mik'e ta saka hijabin ta tayi waje gabanta sai faduwa yake bata san Mai yasa take Jin fitar da zasu yi a tare Kabiru Yana da wani manufa a zuciyarsa. Koda ta fito Kabiru har yayi waje Yana jiran ta. Jiki a mace ta fita waje bayan Sajeeda ta Mata adduar dawowa lafiya Tana zuwa ta haye machine din Kabiru dan har lokacin Kabiru bai siyi mota ba saboda gudun zargin mutane. Sai da suka fara tafiya Kabiru ya fara magana yana "Ba kya Jin magana ko?sai kinyi abinda Zaki tona min asiri ko"? Jiki na rawa Yesmeen ta hau grigiza kai tana "Ba abinda nace Abba wlh ba abinda nayi" Kabiru girgiza kan sa yayi bai Kara magana ba dan Yesmeen ta zame Masa karfen kafa,Yesmeen na neman zame masa barazana ga cikar burin sa ya rasa yadda zai yi da ita kullum zuciyarsa cike take da fargaba duk da ya fesa Mata maganin mantuwa ko da ta gan shi amma sai yake jin kafin ya cimma burin sa zata iya aikata mishi komai. Gashi bai fi saura kwana hudu ya samu cikar burin nasa ba ko a yanzu so yake ya tsoratar da ita yadda ko da mutuwa ma yayi bata Isa fallasa sirrin sa ba. Bai zame da ita ko Ina ba sai gidan gonan Rabiu a bushen da yake Jin Zuciyarsa da tsanar da yayi wa yesmeen,ba dan gudun zargi ba tsaf zai shaketa ta mutu a binne ta. Yana tsayar da machine din ya sauko. Yesmeen da taji kirjinta kamar ya faso saboda tsoro dan ba kasuwan suka zo ba kamar ma daji ya kawota. Tsawan daya daka mata yasa ta sauko daga machine din a gigice ta zub'e a kasa tare da fasa ihu tana ruko kafarsa a gigice tana "Abba na hada da girman Allah karka kasheni dan darajar da Allah yayi wa Annabi karka cutar dani" "Rufe min baki kafin na yanka ki ni zaki Tarawa jama'a" Da sauri Yesmeen ta rufe bakin ta jikinta na wani irin rawa Kabiru ya fusgo hannun ta ya tura gate din Suka shige Yesmeen ta turje ta fara Neman ihu dan bilhakki da gaskiya zuciyar ta ta bata kasheta zai yi Kabiru kuwa ganin yadda take zunduma ihu yasa ya kwasheta da Marin da sai da ta ga taurari na gilma mata kafin ta dawo daidai. Kabiru ya tsugunna a gabanta ya daga rigar sa sama ya d'auko wuka. Yesmeen ta zaro ido. Cikin wani irin murya kabiru yace "Yesmeen kin takura min kina min barazana kasheki Zan yi kawai na huta" "Abba Dan Allah karka kasheni na rantse da Allah ban taba fadawa kowa ba,tunda ka min gargadi ban Kara leko ka ba" "Karya kike yi na gano take taken ki so kike ki tona min asiri so kike ki fallasa sirrina" "Wallahi Abba ba Wanda na gaya wa Kuma bazan tab'a fada wa kowa ba ka yarda dani" "Wallahi Yesmeen duk ranar da na kamaki kin Shiga abinda bai shafe ki ba kinsan Allah sai kasheki dan duk duniya ba wacce na tsana sama dake a larura nake zaune dake ki nisance ni Yesmeen wanan shine gargadi na karshe da zan miki domin duk takun da kike Ina sane komai kike Yi Ina kallon ki" "Ba Wanda zan fadawa Abba in Sha Allah na yarda ka kasheni idan har na fadawa kowa" Kabiru ido ya zuba mata daya ga yadda jikinta ke rawa dan ba karamin tsorata tayi ba. Mik'e wa yayi ya maida wukar ya daka mata tsawa akan ta tashi su tafi. Da sauri ta fice waje ya bita ya tada machine suka tafi kasuwar dan dama Sajeeda yaso ta tafi kasuwar ya tsorota ta a gidan amma ta tsaya Masa tambayoyi Koda ya gama siyan duk abinda zai siya. Sai da ya saka Yesmeen ta wanke fuskarta yaga ba Wanda zai gane tayi kuka ya loda kayan da ya siya mota ya biya kudin Yesmeen ta tafi gida. Yesmeen sai da ta isa gidan hankalin ta ya dan kwanta bata tab'a tsorata kamar yadda Kabiru ya tsorata ta ba,Sajeeda kuwa sai tambayoyi take mata akan Mai ya sameta ta ganta a firgice haka. Yesmeen tace ba komai gajiya kawai ta kwaso. Saboda Kar Sajeeda ta zargi wani abu ta dan saki jikinta ta tayata ayyukan gidan taci abincin Ana kiraye kirayen sallah magriba ta shige daki tacewa Sajeeda a gajiye take bacci take ji tana sallah zata kwanta. Ko da ta shiga d'akin jakar makarantar ta ta d'auko ta d'auko paper da biro ta hau rubutawa Sajeeda wasika tana kuka,dan ta yanke a ranta guduwa zata yi bazata iya cigaba da zama a gidan da rabon da ta samu bacci mai kyau a gidan ba har ta manta,jininta da zaa auna zaa ga yayi mugun Hawa saboda fargabar da take fama dashi,kalar tsanar da take hango Kabiru na mata wata rana zai iya kashe ta din" Kafin a Kai ga haka gwara ta tsira da ranta ta gudu ta bar gidan ta Shiga duniya bazaa rasa na Allah da zasu taimaka mata ba,dan bazata je wajen dangin mahaifiyar ta ko mahaifinta ba ballantana a Nemo ta. Tana rubuta wasikar tana kuka har sai da ta gama ta ninke takardar ta kwanta lamo tana jiran dare yayi ta fice daga gidan. A kwancen da take kuka kawai take tana tunanin Ina zata dosa ya Sajeeda zata ji idan ta ga wasikar. Tana nan a kwance bacci ya fara k'ok'arin sace ta sai k'ok'ari take ta hana kanta baccin har sai da baccin ya saceta ta k'arfi. Mafarki Shigowar Sajeeda d'akin ta da Sunan ta da ta Kira yasa ta bud'e idonta. Ganin Sajeeda a tsaye ta kura Mata ido hawaye na zubo Mata yasa ta mik'e zaune da sauri tana Umma "Kar ki tafi ki barni Yesmeen,Mai na miki da Zaki tafi ki taimaka min karki tafi Yesmeen"......... 2nd to the last free pages Biya 500 ta wanan acct din 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko katin mtn ta wanan lambar 08033719070 sai a turo da shaidar biya ta layin nan 08033719070 ko wanan layin 08068484400 Mutanen Niger Kuma ku tuntubi wanan lambar +227 96 82 89 84 karku yarda a Baku labari dan rufaffen sirri labarine mai Abubuwan ban mamaki da alajabi akwai Kuma darusa Mai yawa MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4k Mg's beauty

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});