Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 67

Chapter 67

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,244 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bakin Hali ba,dan lokacin da muke Yara indai na samu Abu ko nuratu haka zatayi ta fushi tana bakin ciki,akwai ranar da naci na biyu a islamiya mahaifinmu ya bani kyautar sabon littafi da fensir,daddare duk muna kwance ba bacci nake ba a kwance nake dan ba wuta da wuri Mu ke kwanciya Ina kwance da Nuratu a katifar dake kasa sai naga ta sauko daga kan gadon ta nufi wajen kayana har zan tashi zauna na fasa sai gashi ta bude akwatin karfen da kayana yake ciki,ta d'auko littafin ta yaga ta karya fensir din ta maida min akwati,har na girma na kasa manta abinda tamin da sai da na girma na gane bakin ciki yasa tamun haka, Haka idan muka samo kyautar abu ni da Nuratu sai ta yaga,ko auren Abban Nusrah da nayi murna take saboda tasan ba Mai kudi bane mijinta yafi shi hali, maganar Abban Nusrah ya katse min tunanin da na tafi,Sajeeda ki sha kunun Mana" "Tun dazu nake fama da ita ta Sha tak'i sha Kuma saboda ita na dama kunun nan" "Ko dai zafine da kunun"? Girgiza kai Yaya Abu ta hau yi tana "Ina fa kunun yaga zafi" Sai ta Kai cokalin bakinta ta fito da harshenta ta dandana tana ba zafi" Sai a lokacin ta tuna dandana kunun tayi ta Kuma hadiye,ta mike da azabar sauri ta fara sallati tana tari da k'arfi tana kakalo amai tayi waje da gudu, Lumshe idona kawai nayi Ina yiwa Annabi sallati,da kanta ta dandana kunun da take so ta kasheni dash,sai Kuma na fashe da kuka dana tabbatar da kasheni dai Yaya Abu ke San yi Abban nusrah kuwa ya bita bakin kofa Yana mata sannu ya dawo wajen da ta zauna ya Kara d'aukar kunun Yana "Ina ga tsarkewa tayi tashi ki Sha kunun Sajeeda ko wani abun kikeso kici"? Ido na zuba Masa Ina Addu'a Allah yasa shi ma ya Sha kunun wallahi da zan ga abinda zai kashe Abban Nusrah Dadi zanji,kunun ya kawo bakina yaga na Kara kau da kaina sai ya ajiye kunun Yana "ko Tea Zaki sha,Wai bakya gajiya da kuka ne Sajeeda dan Allah ki bar kukan nan karki jawowa kanki wani matsala bari na hada miki shayi Ina ga kunun ne bakya so. Ya mik'e yayi waje. Kabiru. Yana fita yayi hanyar kitchen Yana Shiga yaga Yaya Abu nata kakarin amai, gefen ta Kuma ga gwangwanin Madara ta bud'e ta lafta a kofi, Shi kuwa cikin mamaki ya karasa wajen ta Yana "Yaya Abu lafiya kuwa mai ya kawo Miki amai Kuma"? Yaya Abu kuwa hannu kawai take turawa bakinta tana kakarin amai,gudun Kar Kabiru ya zargeta yasa ta zuba ruwa a madarar ta kafa Kai ta shanye. Sai da ta shanye ta kalli Kabiru dake ta jera Mata sannu tana "Wallahi bana San kazanta wari na shaka shine naji zuciyata na tashi" "A cikin kunun warin yake"? "Aaa Ina Kai kunun bakina na shako warin" "Ai da kin fara gyarata kafin ki bata abincin naga yau ma ai warin da sauki Sannu bari na dama mata shayi Kamar kunun ne bata so" Yaya Abu bata iya magana ba saboda cikin ta da taji Yana murda mata da ciwo, Ta Kara dama wani madarar a daddafe tayi d'akin ta dan d'akin ta daban aka ware Mata,Yesmeen ma na da nata d'akin. Tana shigewa daki ta daga Kai ta kwankwade madarar ta kwanta rub da ciki tana "da kaina nake neman kashe kaina banda rashin hankali da b'atar basira mai ya kaini dandana kunun duk wanan kabirun ne ma ya rudani naje na dandana Ta Kara cije lebbenta saboda sosai taji cikinta na karta mata duk da sai da tayi amai,bata tab'a tunanin haka maganin ke da mugun karfi ba,ai wanan da Sajeedan ta sha da asirin ta ya tonu an gano ita ta saka mata magani a kunu,ya zama Dole ma ta Nemo Wanda bai Kai wanan k'arfi ba,ta dade tana Addu'a Sajeeda ta saukaka mata ta tafi da kanta batare da ta karasa ta ba,tunda ta gano irin arzikin da Kabiru yake dashi ta fara kwadaituwa da san itama ta dandana arzikin,ganin Kuma Sajeeda na fama da rashin lafiya yasa ta fara tunanin idan har Sajeeda ta mutu zata iya auren Kabirun ta mori arzikin sa sai ta fake da ta aure shi ne dan ta kula da yaran da wanan kudurin nata ta fara yiwa Sajeeda fatan mutuwa,har mamaki take yadda take ganin Sajeeda na raye dan ba karamin jin jiki sajeedan ke ba,daya hannun kuma ta ringa dan shishigewa kabirun tana caba ado,Sajeeda sam bata dace ma da arzikin Kabiru ba ita ta dace da arzikin, sai dai duk kwalliya da girkin da take yi bata ga alamar Kabiru na ganewa ba watakila dan Yana ganin Sajeeda shi yasa bazai tab'a kawo tunanin aurenta a zuciyarsa hakane yasa ta fara tunanin hanyar da zata bi ta karasa Sajeedan da kafar ta daya ke duniya daya a lahira,tana tsaka da tunanin abun yi Kabiru ya tareta da zancen zai Kara Aure,a ranar ko bacci bata yi ba idan har ta bari yayi auren hakan na nufin bazai tab'a aurenta ba idan kuwa tayi gaggawan kau da Sajeeda dole ma yayi tunanin auren ta,sai gashi Sajeeda bata Sha maganin ba ta Kare a dandana maganin da bata San Yana da mugun karfi ba,dan Mai gadin gidan tasa ya siyo mata maganin,dole ta Kara siyo wani,dan wanan yayi k'arfi da yawa tunda har a yanzu cikinta ciwo yake. Tasan indai ta kau da Sajeeda ba mai kawo zargin ba mutuwar Allah da Annabi tayi ba,tunda dama ta dade tana fama,Kiran da ya shigo wayarta ne ya katse mata tunanin da take tana d'auko wayar ta ga Gwaggo ce ke kiranta,mai da wayar tayi ta ajiye dan yanzu Gwaggo ta fara matsa Mata da waya akan Sajeeda kusan kullum sai ta kirata ta tambayeta ya jikin Sajeeda. Sajeeda Abban Nusrah bai Dade da fita ba sai gashi ya dawo da kofin shayi a hannun sa har lokacin kuka nake,wa zai yarda wai uban yayana ne ya maidani haka saboda yayi kudi,wa zai yarda yayata da ta saki nono ta bani itace ke san ganin ta kasheni saboda kawai ta auri mijina da take ganin yayi kudin da bata san ta hanyar da ya samu kudin ba, duk na jikina ke san cutar dani wane irin zamani ne wanan da Allah ya kawo mu,wai yayata ita take San ta kasheni,nata a yanzu sai naji yafi tsaya min a rai,na Abban Nusrah bai girgizani kamar yadda na Yaya Abu ya girgizani ba,dan dama shi namiji bashi da tabbas,ita Kuma Yaya Abu fa Yar uwata ce ta jini,da yanzu mutuwa tayi,auren Abban Nusrah zatayi ba tare da taji komai a zuciyarta ba,nasan shi ma Abban Nusrah tsaf zai aureta tunda da sauranta,waya sani ma ko ma suna soyayyar yanzu,bansani ba tunda nasan Abban Nusrah Yana cikin maza masu karfin shaawa. Muryar Abban Nusrah ya katse min maganar zucin da nake Yana "ki bude bakin ki na Baki shayin Sajeeda Ina saurine zan fita ana jirana idan na dawo akwai maganar da zamu yi" Kau da kaina nayi dan shi ma yanzu ba yarda nayi dashi ba, kila shi ma

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});