Chapter 73
Chapter 73
damuna, istigari na fara yi a zuciyata dan zuciyata a kuntace take nasan Ina fara istigifari zan ji sanyi a zuciyata, nasan yanzu da wuya ya iya hana Gwaggo tafiya dani, ko yak'i yarda babba yalwa ba bari zatayi ba da kunya ya kalli kakata yace bazai barsu. Su tafi dani ba. Gwaggo Sai da ta fito daga d'akin Sajeedan hankalinta ya dawo jikinta ta fara karewa gidan kallo,jiki a mace suka karasa d'akin da Yaya Abu take Kamar tunanin da takeyi irinsa baba yalwa keyi dan suna Shiga d'akin babba yalwa tace "Wai wane irin aiki mijin Sajeeda ya samu haka yayi irin wanan kudin"?ba Sanaar gyare gyare yake bane"? "Babba nima kaina ya kulle bansan ya akayi Kabiru yayi kudi lokaci daya haka ba Kinga katon gidan daya Gina wancan shekarar ma ai bashi da komai" Babba yalwa bata kara magana ba zuciyarta ya hau mata sake sake Kamar yadda na Gwaggo ke mata. Shiru d'akin ya d'auka kowace da tunanin da take ko abincin da Sajeeda ta ajiye musu ba Wanda yayi yunkurin tabawa, Gwaggo yalwa kuwa tunanin yadda Kabiru yayi kudi lokaci guda kawai take Sajeeda ba baki ba ballantana ta tambayeta aikin Mai Kabiru ya samu haka. Shigowar Kabiru d'akin ya katse musu tunanin da suke. Kabiru ya zube a gabansu ya hau gaishe su,sai da suka gama gaisawa Kabiru ya fara magana cikin faraa Yana "Gwaggo kin k'i kwantar da hankalin ki har sai da Kika d'auko hanya ai da baki wahalar da kanki ba Gwaggo wallahi zata samu sauki yanzu haka ma Shirin da nayi asibitt zanje ganin likita dan Ina tunanin kasar waje zamu fita da Sajeeda likitan yace zamu dace da magani idan har muka je" "Ai Ina ga Kabiru ba sai ka wahalar da kanka ba tafiya kawai zamuyi da Sajeeda a ganin da nayi Mata a gaskiya larurarta bata asibiti bace zamu je mu gwada na gargajiya da Addu'a in Sha Allahu zamu dace dan da nasan haka larurarta take da tuni nasa an Kai ta can" Cewar babba yalwa Kabiru da yaji hankalinsa ya fara tashi da maganar tafiya da Sajeeda yafara magana Yana "babba yalwa larurar Sajeeda ba maganin gargajiya ne zai warkar da ita ba,dan kwarone ya cijeta yanzu haka fa asibiti zanje" "Karka damu tafiya zamuyi da ita zaa dace acan in Sha Allahu" "Karka sake ka tab'a yarda a kaita wani wajen da Sunan za'a mata magani idan har ka bari aka kaita wani wajen aikin ka na iya warwarewa idan aka hadu da kwararre"....... Mg's skincare Kunji takennan kunsake jinshi shin yar'uwa nace wai haryanzu baki jaraba products dinsu ba😵💫yar'uwa mace fa yar ado da kwalliyace koda kina dakyau akace kikara da wanka😍sufa kayan mg's basa bleaching duka kayansu 💯 natural ne sannan organic zasu gyara sukuma goge Miki jikine kawai yakara bayya ar da ainihin zallar Madarar kyawun halittar da Allah yayimiki🥰 Wai kinafama da pimples da spot afuska amma haryau baki nemi mg's ba🤔duk Mai tantama akan kayan gyaranjiki yacire mg's domin babu shakka sudin na dabanne indai problem dinki matsalan fatane yar'uwa kijaraba koda soap dinsu bi'iznillah zaki godemin👯♀️kayansu ga kamshi inkinjaraba kinga yanda suke na tabbatar bazakiso su Yanke Miki ba🤩08062991549 anatayi Baku sisters kusamu kugwada koda b duka kit din na gyaranjiki ba zakuga sauyin da fatarku zata samu cikin lokaci kalilan🥳jikin yazama so fresh ko Ina kikashiga kita glowing fatarki na walwali kamar madubi😘keda kanki zakina burge kanki balle wasu🤗08062991549 Adade anayi sai gaskiya sannan siyan nagari Maida kudi gida ❤️ Duk Mai bukatar products din mg's kutuntubi wadannan numbers din domin tasune kawai zaku samesu🙏 Chat 08062991549 07046881166,07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Team glow🧖♀️ *WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84* *PAGE 55* Maganar shugaba da Kabiru ya tuna yasa yaji hankalin sa ya Kara tashi da yaga babba yalwa ta dage,dan a yanzu ma so yake yayi ta nuna musu magani yake nema mata Saboda ya d'auke musu hankali daga kanta sai gashi su babba yalwa na neman jika Masa aiki,yasan ma da wuya su iya Sama Mata maganin warakar amma Yana tsoron a dace da samun maganin asirinsa ya tonu, Ganin suna kallonsa suna jiran suji mai zai ce yasa ya kirkiro murmushi Yana "Babba bance Zan hana a Kai ta a nema Mata magani ba,Amma inaso ki gane cutar Sajeeda baya bukatar maganin gargajiya,dan idan aka ma hada da na gargajiya wallahi jikinta sai yafi haka rikicewa dan Bata magana ne da kin tambayeta kinji duk Sai da muka gwada na hausar baa dace ba a yanzu Kuma na samo kwararren likitan daya san Kan cutar ta inaso na Kai ta ya mata magani idan har muka je baa dace ba sai ki Kai ta Inda kike so ki Kai ta din" "Inda kuka je Ina ganin basu san Kan magani ba shi yasa da kuka jarraba na gargajiyar baku dace ba,amma nasan indai na samu na kaita wajen mai sallati da ikon rabbi zata warke" "Tom shikenan babba abinda za'ayi kibari na kaita mu dawo dan na riga na biya kudi mai yawa idan muka dawo sai ki kaita inda kikeso a Kai ta din" Duk yadda babba yalwa taso Kabiru ya bari su tafi da ita Kabiru k'i yayi ya kalamance su da maganganu Gwaggo Sam baa san ranta ba Suka bar shi akan sai sun dawo din inda ya nuna zasu tafi nan da kwana biyar masu zuwa,sai da yazo fita Gwaggo ta tsayar dashi tana "Anan Zan bar babba Ina ganin sai tafi Abu kula da Sajeeda idan na tashi tafiya gobe sai mu koma da Abu dan zamanta anan din ba tsari. "Gwaggo ai babba yalwa Kamar zamu dora mata wahala Kuma ta tsufa Yaya abun ce dai nake ganin zata iya hidimar Sajeeda da gidanan" "Zan zauna nima zan iya kula dasu tunda Allah ya hore min lafiya ba abinda nake so sama da na bawa Sajeeda kulawa mai kyau" "Toh shikenan babba Allah ya saka da alheri ya Kara Miki lafiya" Daga haka ya fice daga d'akin, Gwaggo ta saki ajiyar zuciya dan Sam ba haka taso ba,amma ganin babba yalwa zata zauna yasa ta dan ji hankalin ta ya kwanta balain tausayin Sajeeda take taso Kabiru ya barta ta tafi da ita,duk da Sajeeda bata iya magana tasan zata so ta tafi da ita din amma ba yadda zata yi tunda ya dage,sai ta tafi tunanin kasar wajen da yace zai Kai Sajeeda har wane irin kudine da Kabiru haka da zai iya fita da Sajeeda kasar waje,?abin na daure mata Kai zata so ta ji irin aikin da yake da ya samu kudi haka. Sajeeda Tunda Abban Nusrah ya fita nake jiran
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111