Chapter 21
Chapter 21
wanan da zaiyi yafi kowane wuya da hatsari Ganin Karen ya daina cin abincin ya sa ya daina shafa shi yaraf Karen ya zub'e a kasa bakinsa na fitar da kumfaa hankali a tashe Kabiru ya mik'e tsaye Yana kallon Karen tun Karen na motsi har sai da ya daina. Hankalinsa a mugun tashe ya girgiza Karen Yaga ko motsi baya yi babu ma alamar rai a jikinsa wani irin ja da baya yi cikin azabar tashin hankali ko baa fada Masa ba Karen dai mutuwa yayi. Wani irin ihuuu ya saka yana "Yesmeen kin kashenii............. Hmmm Yanzu aka fara labari ku biya 500 zuwa acct dinan 2029764071 ko katin mtn zuwa lambar Nan 08033719070 ku turo da shaidar biya ta layin Nan 08033719070 ko wanan layin 08064484400 Mutanen Niger ku tuntubi lambar Nan +227 96 82 89 84 Dan kuyi payment ku more karatu.. MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4k Mg's beauty kit 14k Herbal whitening soap Body cream Face cream Scrub Cleanser Glow oil Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Team glow😍 *RUFAFFEN SIRRI* *NA SADNAF* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *Page 10* A haukace Kabiru ya ringa girgia Karen Yana kuka wiwi,shi kadai yasan wahalar da ya sha kafin a iya hada masa abinda zaiyi ya samu cikar burin sa,sai a yau da zai samu cikar burin sa Yesmeen ta kashe masa arzikin sa. Ya dauki abincin ya kurawa plate din ido, zuciyarsa kamar tayi bindiga saboda bakin ciki,ba Mai Masa aika aikan nan sai Yesmeen ba wacce ta saka masa ido sai ita daga fita yayi fitsari shine ta Shiga kitchen taje ta masa wanan aika aikan. Shikenan duk burikan sa da wahalar da ya Sha ya tashi a banza, Yesmeen ta jawo mai Asara A wani irin haukace yayi cikin gidan jikinsa na wani irin rawa ba abinda zai hana ya raba Yesmeen da ranta a yau. Bugun da yayi wa k'ofar palon yasa Sajeeeda mik'ewa a tsorace tana "Abban Nusrah lafiya"? Ko kallon ta bai yi ba yayi hanyar d'akin yesmen Yesmeen kuwa tunda taga yayi waje ta shige d'akin ta ta kulle wani irin tsoro ne ya shigeta a lokacin da Suka hadu a k'ofar kitchen sai taji ta fara nadamar ma zuba shinkafar beran dan tasan indai Karen ya mutu atake dole Kabiru ya zargeta tunda yaci karo da ita a lokacin da take fitowa daga kitchen, kirjinta kamar ya fado saboda fargaba ta tsaya a window tana kallonsu. A lokacin da Karen ya zub'e a kasa taji Kabiru ya Kira sunanta bandaki tayi a guje dan tasan yau kashinta ya bushe kuka kawai take a jiya tayi mafarkin Karen na ta cizon Sajeeda har sai da Sajeeda ta daina motsi,sau biyu tana mafarki a jere hakane yasa ko da ta tashi,sai taji gabadaya ta kasa samun nutsuwa zuciyarta tayi ta rayya mata da ta zuba wa Karen maganin b'era dan daga mafarkin da take tasan karen su Kabiru ke so ya cutar da Sajeeda,bazata iya zuba ido tana kallo ba, dole tayi wani Abu. Bugun da Kabiru ya fara yiwa kofarta yasa ta saki ihu dan ba k'aramin bugu yake yiwa k'ofar ba ta tuna yadda ya ringa rantsuwar zai kasheta idan ta Kara masa shishigi. Sajeeda kuwa hankalin ta ba karamin tashi yayi ba da ta ga yadda Kabiru ke k'ok'arin balle k'ofar d'akin Yesmeen Yana rantsuwar sai ya kasheta. Cikin tashin hankali ta fara magana tana "Abban Nusrah Mai Yesmeen din ta maka haka dan girman Allah kayi hakuri karka manta marainiya ce ka rufa min asiri mai ta maka haka dan Allah" Cikin jajjayen idonsa ya kalli Sajeeda Yana "Kinsan Allah yarinya nan sai na kasheta sai dai duk abinda zai faru ya faru" ido Sajeeda ta zaro cikin tashin hankali tana " A hayyacin ka kake kuwa Kabiru Mai ta maka da zaka kasheta innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Tace cikin ihu a daidai lokacin da ya buga k'ofar da balain k'arfi ya balle,ya shige yana hucci kamar wani zaki bai yi wata wata ba ya fara buga k'ofar bandakin da karfinsa. Sajeeda ta saki ihu Kamar yadda Yesmeen dake cikin bandakin ke zunduma ihu tana azo a taimaka mata. Sajeeda kuwa ganin da gaske idon Kabiru ya rufe idan har ta bar shi ya shiga bandakin shaidan na iya cin galaba a kansa ya kashe mata Yesmeen. Jan kabirun ta farayi da karfinta tana rokon sa shi kuwa iya karfinsa yake tura k'ofar dan ya balla kofar ita kuwa Sajeeda ta Kankame shi duk yadda yaso ya tureta ya kasa dan ba karamin kankama ta masa tana ihu ba. Kabiru ya runtse idonsa jikinsa na cigaba da rawa hawaye sai zubo masa yake na asarar da Yesmeen ta jawo Masa yanzu duk mafarkin sa na yin kudi ya tafi a banza dan dak'yar idan shugaban zai Kara sauraransa dan Yana ta basu wahala a duk abinda aka ce yayi bai yi ba Sajeeda da zai samu komai yazo masa cikin sauki,ta bijire masa hanyar da ya rage Masa Yesmeen ta ruguje masa Anya Yesmeen dinan mutum ce kuwa"?ko dai tasan dalilin daya saka ya kawo Karen cikin gidan. Hucci kawai yake Sajeeda kuwa har lokacin tana Kankame dashi tana bashi hakuri kamar yadda yesmeen dake bandakin ke aukin bashi hakuri tana sharrin shaidan ne ya yafe mata. Baya Jin kwarin jikin sa saboda irin bugun da yayi wa k'ofar d'akin nata murya can kasa da tunanin daya darsar Masa na idan har ya dage zai yiwa Yesmeen wani abu,asirinsa na iya tonuwa a gaban Sajeeda dan Yesmeen na iya fadar wani Abu ko shi zuciya tasa ya Fadi wani abu asirin sa ya tonu. Ki cikani Sajeeda na fasa yi Mata komai Karen da na ce Miki ba nawa bane na abokina ne Yesmeen ta sakawa shinkafar bera baki ga yadda abokina ke ji da Karen nan ba dazu ma sai da muka yi waya na jadadda Masa zan maida Masa gobe yarinyar nan da ta tashi ta zubawa Karen shinkafar bera" Kabiru yace cikin dacin zuciya idonsa na Kara cikowa da ruwa dan dauriya kawai yake shi kadai yasan tashin hankalin da yake ciki da sai da komai yazo masa karshe Yesmeen ta Masa haka, duk saboda cikar burin sa yak'i sallah har tsawon sati daya,yayi wanka da jini,ya Sha jini yaje makabarta karfe biyun dare ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111