Chapter 82
Chapter 82
kashe Sajeeda ne?akan me zan kasheta,ka fito kace ka gaji da zamana a gidanka ba sai ka hada damin sharri ba dan wani ne ya shigo yake san cutar da ita ka Kuma leka kasan gadon kagani dan wallahi an ja kafata bari na leka kagani" Kabiru kallonta kawai yake a lokacin da ta fara k'ok'arin tsugunnawa dan ta leka kasan gadon. Yesmeen hankalinta idan yayi Dubu sai da ya tashi da taji abinda Yaya Abu tace d'auke numfashinta tayi ta cire hannunta dake cikin ledar da ta nannade jikinta dashi a hankali,ta mik'a hannun Yaya Abu na lekawa ta kwasheta da mari, Yaya Abu ta saki ihu tayi waje da balain gudu. Kabiru kuwa ya mik'e tsaye da sauri ya ja da baya Yana kallon kasan gadon dan yaji karar saukar Marin. Tabbas da mutum a kasan gadon dan kamar motsi ma yake ji a kasan gadon. Har lokacin ihu Abu ke tsallawa tana Aljanine a kasan gadon Kabiru kuwa da shi ma jikinsa ya fara rawa ya fara neman abunda zai haska kasan gadon da kuma sandar da zai bugawa koma waye ganin bai ga komai a d'akin ba yasa yayi kasa da murya Yana "Sajeeda da gaskiya Abu akwai mutum a kasan gadon nan bari na dauko wayata na haska na d'auko sanda ta watakila barawone Ina zuwa"? Yayi hanyar waje da sauri,Yesmeen kuwa ta fito daga kasan gadon da ledar a nannade a jikinta ta shige zif din Sajeeda cikin zafin nama tana hada wani irin gumi,k'yarma kawai take saboda tsoro. Kabiru na fita ya ci Karo da yaya Abu da ta dafe kumatunta tana cigaba da ihun "ka leka kagani Kabiru wallahi akwai mutum ko aljan a kasan gadon,motsin da najiyo daga d'akina yasa ni fitowa dan na dubata wallahi ka leka kagani" "Shhhh to ki bar ihu mana haka Ina zuwa" Ya haye sama da sauri ba jimawa ya sauko da wayarsa da ya Kunna tocilan daya hannun sa rik'e da sandar labule yayi d'akin Sajeedan a hankali Yaya Abu da jinta bai dawo sosai ba tabi bayansa itama. Nesa da gadon ya tsugunna ya hau haska gadon sai dai bai ga alamar komai ba. Yaya Abu kuwa ta gwallo ido tana "baka ga komai ba"? Kabiru bai kulata ba ya cigaba da haskawa ganin bai ga komai ba yasa ya mik'e tsaye ya ajiye wayarsa a gaban mudubi da sandar hannun sa ya nufi Kan gadon ya d'auki Sajeeda da har lokacin take kuka ya ajiyeta a Kan 2 Seater dake cikin d'akin ya daga katifar sama. Yaya Abu dake bakin kofa ta saki ihu tana "Wallahi Aljanine ya rike min kafa ya taska min mari innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Kabiru kuwa shi kansa sai da kansa ya daure da mamaki dan tabbas yaji karar Marin da aka yiwa Yaya Abu ta kasan gadon ya Kuma ji motsi amma sai gashi ba kowa a kasan gadon. Yadda yaga Yaya Abu na cigaba da ihu a tsorace har su Annur dake d'akin su sai da suka fito yasa yacewa Yaya abu "Dan Allah ki bar ihun nan haka Kinga dai ba kowa a kasan gadon kila Aljanine ya ga zaki yi ba daidai ba ya cafo kafarki ya waska Miki mari, daga yau Sajeeda bazata Kara kwana a d'akin nan ba sama zan maidata dan Kamar zamanta a d'akin nan hatsarine" Daga haka ya saki gadon ya nufi wajen Sajeeda da ta zaro ido tana gurnani Yaya Abu da ta mugun tsorota dan ta gama yarda Aljanine ya ja kafarta ya waska mata mari ta shige dakinta da sauri ta kulle ta zauna a gefen gado jikinta na wani irin rawa ta yarda yadda Nuratu ke da Aljannu Sajeeda ma na dashi,dan tunda ta kuduri niyyar kashe Sajeeda ta daina cin abincinta idan har ba Aljannun ta ne suka fada mata ta saka magani a abincin ba ba yadda za'ayi tak'i ci,yau da ta so amfani da pillo Kuma Aljanin ya ruko mata kafa, tsoronta ma kar Aljanin ya biyota daki ya kasheta tunda ya b'ace daga kasan gadon. Wani irin zabura tayi ta nufi kofarta ta bude tana kalle kalle,har zata doshi d'akin Yesmeen ta fasa dan dakin Yesmeen ma ya mata nisa nasu Annur ne a gefenta. Ta fada dakinsu da sauri ta rufo k'ofar duk suna zaune da Alama basu koma bacci ba ta haye gadonsu ta kudunduna ta rufe idonta,tabbas Sajeeda nada Aljannu babu tantama da alama burin da taci na auren Kabiru ba zai tab'a yuwa ba dan dak'yar Aljannun ta su barta ta zauna lafiya idan ta ma samu nassarar kashe Sajeedan yanzu ma sajeedar tsoron ta take ji,a kwancen da take ta tafi tunanin suna Yara lokacin da ta addabi Nuratu mahaifiyar Yesmeen da Sajeeda,ranar da ta Zo ta hada musu sharri a kan su suka cinye abincin Babansu mahaifiyar su ta zane su,a ranar Nuratu Aljanunta suka tashi ta shaketa da bango har gobe da tabon a wuyanta shi yasa Sam basa shiri da Nuratu har kowa ya Kama gabansa har Kuma suka manyanta bata manta shakar ba dan farcenta ta soka mata a wuya,kila irinsa ne da Sajeeda, tsoro ne ya Kara rufeta,ta cije lebbenta tana hararo Asarar da zatayi na rasa arzikin da ta ciwa buri,tuna yadda taga Kabiru dazu da yaje d'akin Sajeeda ya saka ta mik'ewa zaune,mamakin yadda Kabiru zai nemi Sajeeda da gabanta ke fidda ruwa kawai take,da yanzu bata je d'akin ba haka zai nemi Sajeeda kila shi ma ya kwaso cutar yazo ya zuba mata idan da ta samu nassarar kau da Sajeedar, tuni taji tsigar jikinta na tashi har yawu na taruwa a bakinta dole Kabiru yaso Kara Aure,idan har shaawa na iya sawa ya nemi Sajeeda da Babu abin mora a jikinta,haka tayi ta juye juye tana tunanin kila ma Yana can Yana neman Sajeeda tunda ya haye da ita sama,zata san yadda zata yagi rabonta kawai amma bazata tab'a iya auren Kabiru ba Koda Sajeeda ta mutu sai dai idan roba zai ringa sawa. Yesmeen a hankali ta fito daga sip din ta jike da gumi Kamar an watsa mata ruwa,har yanzu jikinta bai dainawa rawa ba,dan ta hararo kalar shaka da dukan da zata Sha a wajen Yaya Abu da Kabiru ya ganta a kasan gadon,ita kanta bata san yadda tunanin wanka mata mari yazo Mata zuciya ba,cikin sand'a ta fito daga d'akin dan ba motsin da take ji,ta kalli matattakalr bene tana tunanin halin da Sajeeda ke ciki, hankalin ta ya tashi da sama da Kabiru ya maida Sajeeda dole tasan yadda zasu gudu a kurkusa,a yanzu ma so take ta samu wayar Hamza tunda shi yasan tana gani ta Kira Nusrah a waya ta fada mata halin da ake ciki,ko ta Kira Gwaggo idan har basu samu guduwa ba dan yau da gobe idan asirinta na rufuwa na karyar makanta watarana dole asirinta ya tonu,yau ma Allah ne ya tsallakar da ita. Har zata haye sama ta tuna hatsarin da ke cikin hawa saman, Kabiru na iya Kamata. Haka ta koma d'akinta,ta watsa ruwa ta daura alwala mai kyau,ta saka wani sabon doguwar rigarta da wata kanwar mahaifin ta ta taba Aiko Mata tsaraba tana balain san rigar shi yasa ta kasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111