Chapter 78
Chapter 78
da aka hada mi shi na Yan ajinsu dan shine monitor school bus ya kawo shi dan ya d'auka dan yau zasu yi presenting shi yasa ya dawo,daga haka ya fice daga d'akin. Hawaye kawai nake Ina kallon yesmeen,Yesmeen tana ganin k'ok'ari take ta taimaka min Wanda ita bata san rashin fadawa kowa da tsoron da ta saka a ranta zai kai ga Yaya Abu ta samu cikar burinta akaina ko shi Abban Nusrah ya karasani,tunda ya fara tunanin nemana ta baya,haka ta tsaya min surutun idan Yaya abu tayi tafiya zata faki idon driver ta fita ta samo mota yazo ya d'auke mu. Addu'oi da ta saba yimin tayi min ta tofa a ruwa sauran ta shafa min a jikina,haka ta zauna a d'akin har sai da taji motsin bud'e gate tayi sauri ta fice daga d'akin. Kabiru Koda Suka fita a gaban mota Yaya Abu ta kame,ta dora mayafin ta akan kafadarta bai kawo komai ba yaja motar suka dau hanya wani katon super market,sai k'ok'ari yake wajen danne zuciyarsa daga kallon Yaya Abu da yaga tana ta wani musketa musketa ga kamshin ta da ya cika motar,tuni zuciyarsa ta fara Masa sake saken da yake k'ok'arin yakicewa daga zuciyarsa da karfi, magana da tayi cikin murya kasa kasa yasa ya waiga Yana kallon ta "Yanzu idan na tafi gobe wa zai cigaba da maka girki"? Murmushi ya saki yana "hajiya Abu kenan ai bani da matsalar abinci dan zan iya siyo mana muci,ko na yiwa baraka magana ta ringa dafa min har ku dawo,banda haihuwa nan da akayi ma da sati na sama Zan tura gidan su Barakan dan gaskiya zamana haka bazai tab'a yuwa ba" "Wai har yanzu zancen auren naka na nan"? Yaya Abu tace tana jin bacin ran ambatar Barakan da yayi,wai duk kwalliya nan da take yi take Masa signa ya kasa ganewa,ko dan Yana ganin ita yayar Sajeeda ce shi yasa yaki ganewa Gashi yau taga alamar ta burgeshi tunda Yana ta satar kallon ta, mik'a ta farayi tana hamma ta gantsaro kirjinta tana "Ni sai nake ganin kamar da ka dan jinkirta da zancen auren mu ga abinda Allah zaiyi" Kabiru tuni yaji tana neman hargitsa shi,da mikar da tayi,tuna yayar Sajeeda ce ita yasa ya kau da Kansa daga kallon ta yana "Tom idan ban auren ba haka Zan zauna,ai a haka ma nayi k'ok'ari, ban ga alamar Sajeeda zata samu sauki kusa ba Auren kawai Zan yi saboda Kar na fada hallaka ko da naje gida ai na fadawa su baba Zan yi auren duk sun saka min albarka itama Sajeedan duk da bata iya magana nasan ta amince da nayi auren saboda larurar ta,Baraka yarinya ce mai tarbiya in Sha Allah bazan samu matsala da ita ba zata rik'e su Annur da amana. Yaya Abu daina gane Mai yake cewa tayi dan hankalin ta yayi mumunan tashi,tana ji tana gani,duk burin da take ci da mafarkin da take da ta aure shi ta mallaki arziki Mai yawa zai tashi a banza,ba ranar banzan da bata yi mafarki ta zama matar gidan,tana abinda ranta ke so ba,idan har ta bari yayi auren nan,ba yadda za'ayi ya tab'a aurenta,Kuma kila karshen zamanta a gidan ya zo,dan zaa iya cewa ta dawo da Sajeeda gida taje ta cigaba da kula da ita,da a ce ta samu cikar burinta da yanzu anyi sadakar bakwai din Sajeeda,kila kafin tayi arbain ta samu Kan kabirun yace zai aureta, zama bai ganta ba tun kafin Kabiru ya Kai ga turawa gidansu yarinya da yake cewa zai aura ,har suka iso super market din Kabiru yayi ta jidar kaya haka tayi ta zuba tunani,har sai da Kabirun ya tambayeta lafiyar ta kuwa tace masa ji tayi zazzabi na neman rufeta,ya Mata sannu Yana bari ya karasa siyayyan ya maidata gida. Koda suka koma gida d'akin ta ta shige tana tunanin yadda zata yi. Ya zama dole tayi Abu da gaggawa bata san wane irin taurin kai ne da Sajeeda ba,bata ga marabarta ma da mataciya ba tunda komai yi mata ake, arzikin nan itace ya Kamata ace ta samu,tunda Sajeedan tazo gangara gwara kawai ta rage mata wanan wahalar a kwantar a tayar din,tunda ta daina yarda taci abincin shaketa kawai zata yi har sai ta daina numfashi karyar ma rashin lafiya zata yi yadda bazata wani jewa Nusrah ba ko da Wasa bata San nisa da gidan. Kabiru Kuwa tana shigewa ya bita da kallo har ta shige, ya rasa tunanin da ya Kamata ma yayi akan Yaya Abun yadda take shishige Masa da Masa shagwaba har mamaki yake,ko jiya da safe haka ta hawo sama da sleeping dress,ko mantawa take ita yayar Sajeeda ce,yau da ace basu hada jini da Sajeeda ba ai da ya samu nama. Kiran da Rabiu ya Masa ya tuna Masa aikin da ke gabansa, kwana biyu kacal ya rage Masa,sai yaji dama Yaya Abu ba yayar Sajeeda bace da ba abinda zai hana ya nemeta,Sajeeda kuma da zai nema asirin sa a rufe da sai yadda yayi da ita jikinsa Kuma yak'i bashi hadin kai, wanka ya sake Yi ya fice dan ya nemo wacce zata biya Masa bukatar sa Yaya Abu kuwa karfe shidda na yamma ta fito daga daki,ta dora girki,dan bata da burin daya wuce yau dinan ta samu cikar burinta,idan har ta sake bawa Sajeeda abinci bata ci ba ba abinda zai hana ta danne Kan Sajeeda da pillo. Tana gama girkin ta zuba na Sajeeda ta saka maganin ta ajiye a gefe,ta fito daga kitchen din tayi wanka ta caba ado dan so take ta karfin tuwo ta jawo hankalin Kabiru kanta,sai da aka iddar da Sallah isha ta fito daga d'akin tasan Kabiru tunda ya sake fita bai dawo ba,gwara kawai yanzu tayi abinda za tayi kafin ya dawo din,tana Shiga kitchen ta hau kwallawa Hamza Kira da take jiyo maganar su a d'akin Sajeeda,dan so take su bar d'akin ta samu ta bawa Sajeeda abincin. Hamza na zuwa ta bashi abincinsa tana su wuce suje suci abincin su. Hamza na karba ya koma d'akin Sajeeda. Ita Kuma Yaya Abu ta fito da abincin Yesmeen dan ta tsani taga ta fito daga dakinta tana bin bango,ba karamin Haushin Yesmeen take ji ba dan wani zubin sai taga kamar ma tana gani,a yau ne kawai ta gama girkin bata shigo kitchen neman wani Abu ba,amma indai tana girki sai ta shigo,a hankali ta turo k'ofar sai taga Yesmeen ta saki littafin hannun ta da sauri ta mai da idonta sama,Yaya Abu ta saki baki tana kallon ta dan sai taga kamar karatu ta shigo taga tana yi" Ba dai Yesmeen tana gani ta musu karyar bata gani ba,ta nufi wajen da Yesmeen din da kanta ke sama tana kalle kalle tana zuwa gabanta ta d'auki littafin taga littafin addu'oi ne daga dukkan alamu Yesmeen karya take yi musu tana gani idan bata gani taya zata dauki littafi tana karantawa,yesmen kuwa da jikinta ke rawa tana zuba Addu'a a zuciyarta Wayance wa tayi tana waye nan"? "Nice nan ke da bakya gani ya akayi kike karatu"? "Kafin na daina gani na Saba da karanta addu'oi mama shi yasa duk da bana gani,nakan d'auko na ringa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111