Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 76

Chapter 76

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,251 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Sajeedan dan arzikin sa hauhawa kawai zai tayi ,har garinsu yaje ya siyi katon fili dan so yake yayi wa mahaifiyar sa gini itama ta mori arzikinsa,dan tana tambayarsa ya akayi ya samu kudi,ya sharara mata karya take ta yarda ta hau zuba Masa albarka,daga gidansu ya tafi gidansu Sajeeda da alama aikin da aka yiwa iyayen Sajeeda yayi dan Koda yaje basu Masa maganar daukota ba inda ya shirga musu karya akan nan da wata uku ma zasu fita wajen yanzu an dora Sajeeda akan magani,ya nuna musu tana samun sauki, Gwaggo ce ma kamar aikin bai wani Kamata ba sai cewa take ita dai zata d'auko Sajeedan,sai Babansu Sajeedan ne yace baza'a daukota ba tunda ance tana samun sauki,da yazo tafiya ya d'auko kyautar kudi ya Basu,duk sukayi turus suka kasa karba sai ya tuna zasu iya zargin ya akayi yayi kudi haka,sai ya saki murmushi ya hau sharoro musu karya ai yanzu harkar mai yake, Gwaggo kin karbar kudin tayi,dan haka kawai taji bata yarda da shi ba amma ta kasa zargin ko Yana aikata mumunan Abu wajen samun kudin dan gani take kamar bazai iya aikata mugun abu ba,bai Kuma yi Kama da mai aikatawa ba, kafin ya tafi ya sanar musu da zai Kara auren,babban su Sajeeda ya sa albarka dan gani yake kabirun ma yayi k'ok'ari da ya zauna da Sajeeda duk tsawon lokacin nan bai Kara Aure ba, da wani ne ma sakinta zaiyi yace bazai iya zama da ita ba, Gwaggo kuwa ji tayi kamar tayi ta yiwa Sajeeda kuka zuciyarta ta sosu da auren da yace zai yi tana tsoron ya Kara auren ya juyawa Sajeeda baya tunda Sajeeda ba moruwa take ba,sai da ta kasa dannewa ta hau rokonsa akan ya rike Amana ya kwatanta adalci a tsakanin su tana nan tana yiwa Sajeeda Addu'a in Sha Allah zata warke, Kabiru kuwa ya hau rantsuwar bazai tab'a juyawa Sajeeda baya ba,Babansu Sajeedan kuwa yace masa Yana auren yasa Abu ta dawo Dan Yana ciwon kafa ne da tuni yaje ya taho da ita da dan abin kunya ne ace taje ta tare a gidan kanwarta. A haka suka yi sallama ya taho bayan Gwaggo ta bashi lodin maganguna akan ya kawowa Sajeeda tayi amfani dashi,Yana yin nisa da gidan ya wurgar da ledar. Rabiu na d'aukar wayar ya fara magana Yana "kasan na kasa nemanta abinan kwanciya tayi,tak'i mik'ewa,Rabiuu Ina Shan wahalar yin ayyukan nan ni kadai nasan kalar wahalhalun da na sha daga lokacin da na fara harkar nan zuwa yanzu kai kuwa banga alamar kana Shan wata wahala ba" "Taya Zan Sha wahala bayan Ina taka tsantsan da komai,wanan kame kamen da kake fa kana auren yarinya da zata maka biyayya fa an wuce wajen,baka da fargabar komai sai dan aikin da bazaa rasa ba" "Toh idan na aureta bata bani hadin kai ba fa ta zama mai taurin kai irin na Sajeeda"? "Sajeeda a mutanen da tazo ai,na yanzu suna da San kudi ga Ateeka nan Ina ta moreta Ina cikata da kudi,Kuma ko damuwa batayi ba Dan tana samun abinda take so,Kamar yadda nima nake samun abinda nake so,auren nan kawai zaka yi,ka samu ka ringa cika duk aikin da aka baka,itama nasan ka kasa nemanta ne Saboda halin da take ciki,Ina ta baka shawara ka kaita a cika aikin nan kak'i Ido Kabiru ya zaro Yana "Bazan iya ba Rabiu iya wanan da nayi ya Isa ba sai na karasa ta ba har ga Allah baa san raina nayi harkar nan da ita ba taurin kanta ya jawo Mata" "Toh ai gani nake idan baka karasa ta ba bazaka saki jiki ka mori kudinka ba duk tsawon lokacin nan Wai ka kasa Kara Aure wai Kar aga ka mata wulakanci,da nine da tuni nayi biyu ma,nasan banda an rufe mata baki da tana magana zaka iya zuwa kace min zaka fita a kungiya dan naga kamar tsoron ta kake" "Bazaka Gane ba Rabiu Sajeeda tamun hallaci a rayuwa ta kaunaceni shi yasa nake jin ban kyauta mata ba amma zan tura gidansu Barakan sati biyu kawai zaa saka dan ko ba'a Sakani aiki ba yanzu ji nake idan banyi ta bayan nan ba Zan iya zaucewa na siye Iyayenta da kudi sosai,har sun kori saurayinta,duk da naga alamar ba Sona take ba Iyayenta ke tilasta Mata Ina sakar musu kudi nasan an wuce wajen. "Kudi ai sunyi a rayuwa abokina kayi abinda ranka ke so ko jarirya ka nuna kana indai kana da kudi,da gudu zaa baka,yanzu abinda za'ayi sai ka nemi wata a titi kayi aikin kafin kayi auren" Hira suka Kara tab'awa kad'an kafin suyi sallama Kabiru ya kwanta Yana tunanin yadda zai barje baraka idan har ya aureta,dan yarinya ce mai tarbiya dan ko gwada rike hannun ta bai tab'a ba dan babu ma fuska hakan ya Kara kwadaita masa da san ya aureta ya ringa yiwa Iyayenta ruwan kudi,da yake mabukata ne da hannu biyu Suka rike shi, mahaifin Barakan ma idan zai gaishe shi sai ya rusuna,ba Kuma komai ya jawo haka ba saboda Yana da kudine. Sajeeda Ba abinda na saka a gaba yanzu sama da Addu'a dan tunda bakina ya daina yankewa da addua nake Jin dadin jikina,babbar matsalata yanzu Yaya Abu ce da naga ta karfin tuwo take so ta kasheni,yanzu bata tilasta min naci abinci bama ta kawomin,dan sai dai naji muryarta daga Palo,sai dai idan Yesmeen ta faki idonta ta kawo min naci. Bansani ba ko canza salo tayi ni dai addua kawai nake Allah ya kareni daga sharrrinta. Ina nan a kwance wajen sha biyu na Rana sai ga Abban Nusrah ya shigo yana washe baki,hannunsa rik'e da waya,yana "Ma Sha Allah na shigo d'akin sai dai kasan ba magana take ba,bani Nusrah"? Muryar mijin Nusrah da naji yasa na baza kunnena Ina jin Mai suke cewa,barka barka da naji Abban Nusrah nayi Yasa na gane Nusrah haihuwa tayi,tuni hawaye ya hau zubo min na faranciki dan ban taba kawowa Ina rayye zata haihu ba,tana yawan Kira ta layin Abban Nusrah da sai ya shigo zai fada min ta Kira wani zubin idan ta matsa Masa sai ya kawo wayar ya saka a handsfree,haka zatayi ta magana ita kadai tana min kuka da Addu'ar samun sauki,Ina Umman take Abba dan Allah kasa tayi motsi naji ana yin suna Zan taho"? "Ai kema kinsan ba iya motsin za tayi ba amma bari naga ko zatayi" Ya matso da wayar bakina "hawaye na zubo min na fara gurnani dan ta jini,bani da bakin magana Amma Addu'a nake akan Allah ya bata lafiyar shayarwa,cikin rawar murya ta fara magana tana "Umma Allah ya baki lafiya kina raina cikin nan ne dama ya hanani zuwa washegarin suna zanzo,in Sha Allah akwai wayanda na saka suke miki addua anan umma dan Kamar larurarki bata asibiti bace Unma Sunan ki zaa saka wa jaririya zaa ringa kiranta da ummi" Rabon da nayi murmushi Ina ga tun kafin Abban Nusrah ya kashemin rayuwa,maganar Nusrah yasa na saki murmushi na fara gurnani,Abban Nusrah ya d'auke wayar daga wajen bakina yana "Yau kinsa Umman ki murmushi rabon da naga fuskarta haka har na manta" "Allah Abba naji dadi, in Sha Allah umma zata

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});