Chapter 89
Chapter 89
wani ya shigo d'akin amma Bata San koma waye ba,dan da sauri aka koma, ta dauka Wanda ya shigo zai kawo mata agaji sai dai shiru take ji,haka tayi ta kasa kunne tana Jin motsin sa,a lokacin da ta ji karar bud'e gate da tashin motarsa hannuwa ta daga sama ta hau yiwa Allah godiya dan a yau zata bar gidan bazata sake tayi Wasa da wanan damar ba,Sajeeda kawai take ji batasan yadda zasu gudu ba. Duk da tashin motarsa da taji,kin fitowa tayi daga bandakin dan gani take kamar tarko ya danna mata dan ta fito daga bandakin,jin bata Kara Jin motsi ba yasa ta murza mukullin a hankali ta fara leko da kanta a hankali ganin babu kowa yasa ta fito daga bandakin da balain Sauri,tana zuwa bakin kofa taga a kulle da alama Kuma ta waje aka kulle k'ofar, tuni ta zub'e a kasa ta hau rizgar kuka,dan bata san ta hanyar da zata fita daga d'akin ba,ta mik'e da sauri ta hau duba windows din d'akin,nan ma ba hanya dan duk da bugular a jiki,ko kanta ma bazai iya fita ba,haka ta koma bakin kofa ta ringa jijjigawa wai ko zata samu k'ofar ta bud'e,gashi ba waya a hannun ta ballantana ta Kira wani,idan zata shekara tana bugu mai gadi bazai tab'a jiyota ba, Tuna kila zata iya samun extra mukulli a drawers din d'akin yasa ta mik'ewa a zabure ta hau hargitsa d'akin. Ta kusa minti talatin tana duba d'akin kafin ta samu wasu mukulai a saman drawer d'akin,jiki na rawa ta dauki mukulayen ta hau gwada bud'ewa,har ta fara karaya dan duk bana k'ofar bane,tana gwada na kusan karshe taga k'ofar ta bud'u,ta saki wani irin ajiyar zuciya tana yiwa Allah godiya, hijabinta kawai ta saka tana fitowa ta haye sama da sauri dan maigadi zata roka ya taimaka mata ya dauko Mata sajeedan dan ji take bazata iya tafiya ta barta ba. Tana zuwa ta tura k'ofar d'akin ta hango Sajeeda na kife a kasa sai numfarfashi take Yesmeen da gudu ta karasa wajenta ta dagata tana hada ido da Yesmeen ta hau hawaye so take tayi gurnani magana amma ta kasa Saboda jikinta duk a mace saboda rashin kwari makogaranta wani irin zafi yake saboda gurnanin da ta ringa yi da jiyo ihun Yesmeen,ji tayi numfashi ma wahala yake Mata,hannun ta da take iya dagawa ta hau shafa Yesmeen tana gurnani kasa kasa "Yesmeen Mai ya miki Allah yasa Bai cutar dake ba,bani da kafa Yesmeen Ina Jin ihunki ba dama na taimaka miki" Yesmeen da tsananin tausayin yadda ta shigo taga Sajeeda a kife yasa ta Kara rushewa da kuka tasan gurnanin da take magana take amma bazata iya gane mai take cewa ba, tuna bata da lokacin zama Kabiru na iya dawowa ya rutsa su yasa ta jinginar da Sajeeda a jikin gado tana "Umma guduwa zamu yi bamu da lokaci Abba idan har na sake ya dawo nasan sai ya kasheni,har d'akina yazo zai min fyade umma yau ya gane Ina gani,ya rantse sai ya kasheni bari na Nemo abin hawa yanzu nan na dawo kinsan bazan iya d'aukar ki ba Umma" Yesmeen duk da sauri take magana tana k'ok'arin mik'ewa taji Sajeeda ta ruko hannunta da sauri jikinta sai rawa yake Yesmeen ta koma ta tsugunna Sajeeda ta hau jijjiga Mata kai tana gurnanin magana "Ki tafi ke kadai Yesmeen mutuwa Zan yi kirjina ciwo yakemin zuciyata zafi take min ba amfanin rayuwata tawa ta riga da ta Kare kimin alkawari Zaki tonawa Kabiru asiri idan Kika gudu,Yesmeen Allah ya Miki albarka ya cigaba da kareki zan je na hadu da Yar uwata mahaifiyar ki,ki gudu kawai Yesmeen karki bari ya dawo ya Sameki" Yesmeen da ba gane Mai Sajeeda ke cewa tayi ba ta dafa ta tana "Umma kinsan bansan Mai kike cewa ba bari na Kira Mana Mai motan ko Mai gadi ya sauko dake mu buya a wani wajen" Sajeeda girgiza Mata Kai ta hau yi tana grigiza Mata hannu Yesmeen kuwa tayi waje da sauri,Sajeeda ta bita da ido hawaye na cigaba da gudu a fuskarta, numfashinta k'ok'arin daukewa kawai yake tana Jin wani irin nauyi a kirjinta sallati kawai take tana adduar dacewa da Rahamar Allah dan ji take mutuwa kawai za tayi dan daga lokacin da taji ihun Yesmeen taji abu ya soketa a kirji,tasan Kabiru lalatawa Yesmeen rayuwa kawai yake so yayi,a yanzu bata san matsayin da zata ajiye shi ba Dan ya wuce duk Inda take tunani, ihun Yesmeen yasa ta fara k'ok'arin sauka daga gadon Amma ta kasa har sai da ta motsa jikinta da karfi,ta fado daga Kan gadon gurnani kawai take da iya karfinta tana Jin kamar makoshinta na tsagewa sai Addu'a take akan Allah ya hankado wani ya taimakawa yesmeen, tuna Kabiru kila dan Neman biyan bukatarsa yake san neman Yesmeen kila ma ya cutar da ita kamar yadda ya cuceta yasa taji kirjinta na wani irin nauyi da suya har numfashinta na d'aukewa a wanan halin taga Yesmeen ta Fado dakin. Yesmeen A guje tayi gate Mai gadi da bai tab'a ganin ta ba dan bai tab'a ganin ta fito ba ya mik'e tsaye Yana kallonta har ta iso wajensa tana hakki Sai dai Yesmeen tuni taji jikinta yayi sanyi da irin kallon da Mai gadi ke mata da alama bazata samu kansa cikin sauki ba. "Baiwar Allah daga Ina lafiya dan Ina zaune a gate dinan banga lokacin da Kika Shiga ba"? "Ni Yar gidan ce baka tab'a ganina bane dan ba fitowa nake ba,dan Allah matar gidan ce ba lafiya so nake ka taimaka min ka samo min abun hawa na Kai ta asibiti" Wani irin kallo Mai gadin ya hau yi mata dan ji yayi Sam Bai yarda da Yesmeen ba dan bai tab'a ganin ta ba,ko matar gidan da take fada dazu suka yi tafiya da Yara dan duk tunanin sa Yaya Abu ce matar Kabiru tunda har rakosa wajen motar take wani zubin,bai Kuma tab'a ganin Yesmeen da Sajeeda ba "Dan Allah ka taimaka min idan bazaka Kira Mai mota ba ka taimaka min mu sauko da ita sai na kai ta asibitin dak'yar take numfashi Kar tazo ta mutu dan Allah" "Gaskiya ban yarda dake ba dan duk yaran gidanan na sansu bansankii ba sanan matar gidan da safe suka yi tafiya da yaran wacce matar gidan kike nufi"? Yesmeen tasan idan ta tsaya yi masa bayani zai cigaba da bata Mata lokacine har Kabiru ya dawo ya rutsa ta a gidan. Tayi waje da sauri dan ta Nemo mai motar tazo su d'auki Sajeeda. Sai dai ko da ta fito sai ta rasa hanyar da zata bi dan lokacin da Suka dawo bata wani yi kalle kalle ba tunda a matsayin bata gani Suka taho,gashi layin shiru ba yawaitar mutane sai manyan gidaje, gudu ta ringayi kad'an kadan tana bin layin da ta ga a mike. Horn din da taji da zata Sha kwana yasa ta sunkuya da sauri kamar tana gyara takalmin ta a daidai lokacin da motar ya wuceta a guje,tabi motar da kallo ganin motar ta tsaya a k'ofar gidan yasa ta gwallo ido dan Kabiru ma ta hango a gaban motar, Hannunta dafe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111