Chapter 20
Chapter 20
take kallo zanin da ke jikinta ma a yau tayi mafarkin ta dashi Ganin Sajeeda ta kallota yasa ta nufi wajenta tana "Sannu umma na shigo na duba ki ne da naga har sha daya baki fito ba" Sajeeda bata iya ce Mata komai ba dan gabanta zugi kawai yake mata. Mik'ewa tayi tana "Bari na shiga bandaki Ina zuwa" Tana shigewa Yesmeen ta fito jikinta na rawa dan boye tashin hankali da take ciki tayi dama tunda aka kawo Karen nan tasan da akwai manufar da ya saka Kabiru ya kawo karen, Yanzu Kabiru ya rasa wa zai cutar sai Sajeeda mai ta masa haka da ta cancanci irin wanan zaluncin daga wajensa a iya sanin ta da zaman da tayi a gidan,Sajeeda kullum k'ok'ari take ta kyautata masa amma sakayar sa zai yiwa Sajeeda kenan,kuka kawai take na tsananin tausayin Sajeeda bata san Mai ma'anar abinda ta gani ba bata san wane cutarwa Karen zai yiwa Sajeeda ba,ta riga da tasan sirrin Kabiru a yau Allah ya haska mata abinda Kabiru ke nufi da kawo Kare cikin gidan zata yi iya k'ok'arin ta dan ta taimakawa Sajeeda Koda kuwa nata rayuwar zai zama a cikin hatsari. Sake sake kawai take a zuciyarta Motsin Sajeeda da taji a palon yasa ta goge hawayen ta ta fita waje. Ta tarar da Sajeeda a zaune tayi fayau da ita kamar mara lafiya. Kitchen ta shige ta d'auko flask din da ta zuba Mata kunnun gyada da Kofi ta Kai Mata palon ta fara k'ok'arin zubawa Sajeedan sai Sajeeda ta daga Mata hannu tana "Bazan iya sha ba yesmeen bana Jin dadi bani da lafiya bansan Mai yake damuna ba ba daidai nake ba" Sajeeda ta karashe kwalla na zubo Mata Yesmeen kuwa ta zuba mata ido itama idonta ya ciciko da kwallan tausayin Sajeeda kila ma jininta ake zukewa. Cikin rawar murya Yesmeen ta fara magana tana "Umma Allah ya baki lafiya Wai me yake damun ki haka"? Sajeeda share hawayen daya zubo mata tayi tana "Bansani ba Yesmeen idan har Zan kwanta sai nayi mugun mafarki da Karen da Abban ku ya kawo na rasa dalili jikina ba kwari Ina Jin ciwo a jikina bansan Wanda Zan fadawa ya gane Mai nake ji ba,na fadawa Abban ku yace ran Alhamis zai fitar da Karen Kinga jibi kenan rabona da bacci mai Dadi har na manta har tsoron rufe idona nake yi" "Umma daga mafarkin nan da kike yi da Karen nan da Abba ya kawo Zaki san ba kalau ba kinsan wasu karnukan fa mayune Dan Allah umma ki dage da Addu'a ki daina ma bacci,idan za ki yi Addu'ar ki fito Palo kiyi saboda kiyi a nutse" "Ina yi Yesmeen sai dai Ina fara yi bacci zai daukeni ni gidanan gabadaya nake so ma mu bari nidai haduwar Abbanku da wanan abokin nasa bai zame min alheri ba dan sai da suka hadu nayi bankwana da kwanciyar hankali Ina ta so na nusar da Abban ku ya kasa gane kiga fa daga zuwa gidanan Annur dina ya kurmance wallahi banga alheri a tarayyar Abban ku da abokin nan nasa ba na dai cewa Abban ku ya maida Karen nan Inda ya d'auko yace jibi zai maida Karen" "Umma ki dai cigaba da Addu'a kafin kiyi bacci kiringa karatun Qur'ani" Kiringa kwanciya da alwala ni tunda na fara mugayen mafarkai na dage da Addu'a na rage mafarkin dan biyun dare nayi nake tashi nayi ta Addu'a" "Zan saita alarm a wayata in sha Allahu zan ringa tashi biyun daren So nake ma na Kira Abban ku nace masa zanje asibiti bana Jin dadin jikina zanje likita ya dubani" "Sannu umma ki daure ki sha kunun Kinga da zafin sa" Dak'yar Sajeeda ta sha kunun kamar wacce aka yiwa duka haka take jin jikinta. Daga sallahr asuba ta koma bacci,a cikin baccin ta taji Kamar ana zungura mata abu a gabanta ta rasa wane irin masifa ne wanan" Wajen biyar na yamma su Saifullahi suka shigo gidan a guje suna ihun murna Sajeeda dake can daki ta fito da sauri Yesmeen dake kitchen itama ta fito daga kitchen din tana kallon su Faisal ne ya fara magana cikin murna Yana "Abba ya siyo sabuwar mota dalelliya yana waje yanzu zai shigo" "Umma ke Kinga kyaun motar"? Cewar Saifullahi Yana washe baki Sajeeda Da ido kawai nake bin su dan ban ji digon farin ciki a zuciyata na siyan motar da suka ce Abban su yayi ba,ni a yanzu ma tsoron yadda Abban su ke kashe kudi yake dan naji Wai Yana shirye shirye tura Saifullahi kasar waje yayi karatu,a kasa da wata hudu Abban Nusrah yayi irin wanan kudin,anya kudin nan nasa na halal ne kuwa. Bakin sa a washe ya shigo palon Yana kada mukulli ya nufo wajen da nake tsaye Yana "Sajeeda na Miki sabuwar amarya fito waje kiganta" So nake na mishi tambayoyi amma na kasa Kamar wacce aka likewa baki haka nabi bayansa,na ga dalaleliyar motar a tsakar gidan,bansan kudin motar ba amma nasan masu kudi ke hawa irin motar nan Wanda ya isa ya tadda Kai" Yake kawai nake Ina Masa Allah ya sanya alheri cikin murmushi ya Miko mun mukulin Yana "Ke na siyawa Sajeeda babban burina dama na samu kudi kiji Dadi na faranta miki ba kaina na siyawa ba ke na siyawa" Sakin baki nayi ina kallon sa ya gyada min kai "Ni Kuma Abban Nusrah baka siyawa kanka ba sai ni"? "Kin cancanci na siya Miki Sajeeda" Girgiza kaina nayi na maida Masa mukullin Ina "bazan karba ba Abban Nusrah dan duk Wanda ya tambayeni Ina na samu motar Nan bansan mai zance Masa ba" Take ya hade rai ya hau masifa kamar zai kawo min duka Wai so nake nace sata yakeyi bata hanyar halal yake samun kudinsa ba" Nidai shiru nayi bance Masa komai ba. Sai gashi a ranar yayi fushi yak'i kwana a dakina duk hakurin da na bashi yaki ya saurareni. Washegari ma ko ta kan Sajeeda bai bi ba yana tashi ya Shiga kitchen ya dafa abinci dayaji namomi ya zuba a plate din da yake kaiwa Kare abinci dan da kansa yake hadawa Karen abincin da yake ci. Zuciyarsa cike take da farinciki dan a yau zai samu cikar burinsa dan idan komai ya tafar Masa yadda yake so ya zama multi millionaire Har ya d'auki abincin zai yi waje ya ajiye saboda fitsarin daya mugun matsar sa. Sai ya nufi bandaki dan yayi fitsarin. Yesmeen dake labe tana lekansa da tun jiya take Addu'a Allah ya bata saa da nassara. Ganin ya ajiye abincin yasa ta fito da balain sauri hannunta dauke da shinkafar beran da ta Nemo tun a jiya. Tana zuwa ta juye shinkafar beran gabanta na mugun faduwa. Ta fito daga kitchen kenan taci Karo da Kabiru cikin mugun faduwar gaba ta ja da baya ya shige yana watsa Mata mumunan kallo tayi waje da gudu. Ya d'auki abincin yayi bayan gida. Yana zuwa ya tsugunna a gaban Karen ya ajiye abincin a gabansa. Da sauri Karen ya fara cin abincin Yana kada jelarsa. Kabiru kuwa sai shafa Masa baya yake Yana tunanin yadda zaiyi a Daren yau dan abinda akace yayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111