Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 84

Chapter 84

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,231 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

taurari mudin kika mallakeshiπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ Kira ko WhatsApp 09037870422 Karku manta muna da supplement kala kala Na matsi Na gyaran breast Na hips Na slimming Na fari Na gashi Dasauransu Haka zalika muna : HADIN MAI JEGO HADIN UWARGIDA HADIN AMARYA Kuma duka afarashi me rahusa kedai kawai kituntubeni πŸ‘‡πŸ‘‡ 09037870422 Muna garin kano muna tura Kaya ko,Ina cikin aminci 🀝 Sai Allah yakawoku *WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84* *PAGE 75* Gwaggo Tsananin tunani da mafarki da take yi da Sajeeda ya matukar daga mata hankali,dan a yanzu ba dama ta kwanta sai tayi mafarki da Sajeeda a cikin mawuyancin hali, wani zubin tayi mafarki ma da an kawo Sajeeda a cikin makara wai ta rasu,ko tayi mafarki da ita tana "Gwaggo ki zo ki daukeni Ina cikin wani hali Gwaggo kizo ki kawo min agaji" Idan ta farka haka za tayi ta kuka har sai da ta samu Babansu Sajeedan tana fada Masa akan zata je ta dubo Sajeeda ya barta ta d'auko ta,amma haka zai ce mata Kar ta damu mafarki ne kawai,idan har ta dage akan zata d'auko Sajeeda mijinta na iya tunanin sun dauka ya gaza kula da ita ne Har fada sai da suka so suyi dashi akan zuwa d'auko Sajeeda sai babba yalwa ce ta mata magana akan ta bar zancen zuwa dauko Sajeeda tasan Kabiru na iya k'ok'arin sa wajen nema mata magani abinda zata yi kawai ta ringa yiwa Sajeeda Addu'a dan bakin uwa nada tasiri akan yayanta,da wanan shawarar ta zage wajen yiwa Sajeeda Addu'a ba dare ba rana,daga lokacin Kuma da ta fara Addu'a sai ta cigaba da ganin Sajeeda a mafarkin, Wanda tuni ta gano Sajeeda na tsananin bukatar taimakon ta dan ko da Rana ta kwanta sai tayi mafarki da ita, Babansu Sajeeda haka zai yi ta mata fada akan dan ta saka Sajeeda a ranta da yawa ne shi yasa take yawan mafarki da ita,a babu yadda Gwaggo za tayi ta hakura da zuwa dauko Sajeedan ta cigaba da mata Addu'a, azumi da sadaka kuwa cikin yin sa take,dan a yaranta Sajeeda itace mafi soyuwa a gareta ta rasa wane irin cuta ne ya d'auke mata magana ya shanye Mata jiki yake fito mata da ruwa ta gabanta, musamman taje babban asibti ta tambayi likita ko da akwai kwaron da idan ya ciji mutum yake d'auke Masa magana har ya shanye masa jiki,ta lissafa Masa yadda jikin Sajeedan yake, likita yace gaskiya bai tab'a ji ba,sai dai idan wani cutar ne na daban zata iya kawo Sajeedan a dubata,Koda ta dawo daga asibitin haka ta baje tunani tana yi akan gaskiyar kwaron da Kabiru yace ya ciji Sajeeda gashi Sajeeda bata da bakin da zata Fadi abinda ya sameta,Bata San Mai yasa take Jin akwai wani boyayyen lamari game da rashin lafiyar Sajeeda ba,daga yadda take gurnani tana buga kanta da alamar akwai abinda take so ta fada mata amma bata da bakin yi Mata magana,mai ya samu Sajeeda haka?anya ba wani Abu mijinta ke b'oyewa ba shi yasa ya dage akan bai yarda su daukota ba, menene dalilinsa nakin yarda su taho da Sajeeda da ba wani Abu za ta iya Masa ba,a iya saninta akwai jinya da larurar da idan ya samu mutum dole sai an maida mutum gida an nema masa magani,yanzu idan fa ta rasa Sajeeda Kabiru wata zai samo ya shimfida sabon rayuwa da ita,Sajeeda fa ba mai maye mata gurbinta,har ace tana raye a matsayin ta na uwa amma yarta na Abuja a kwance a haka zata zauna watarana sai dai a Aiko mata da ta rasu,Abu da tasani bazata tab'a iya kula da Sajeeda ba,ta Kuma san saboda abin duniya Abu ke zaune a gidan, bazata zauna ta biyewa Babansu Sajeeda Taki dauko Sajeeda ba,a matsayin ta na uwa tasan da akwai matsala dole ta taimakawa Sajeeda dan bata da kowa sama da ita da mijinta idan mijinta yayi iya nashi k'ok'arin ya barta itama tayi nata k'ok'arin. Da wanan shawarar da ta yanke ta Kara tunkurar Babansu Sajeeda da maganar zuwa d'auko Sajeeda inda a ranar babba yalwa na gidan,Babansu Sajeeda ya ringa fadan kullum sai sun yi waya da Kabiru yace Sajeeda tana samun sauki shi bai ga amfanin zuwan da Gwaggo za tayi ba, Gwaggo kuwa ta rushe da kuka akan sai taje sai dai duk abinda zai faru ya faru, Babansu Sajeeda ya zuciyo ya hau fadan idan ita ke zaman kanta sai taje ya gani,babba yalwa ganin abin na Neman zame musu fada har Gwaggo na sai dai idan ya saketa ita dai sai taje ba zata zauna a Aiko mata da yarta ta rasu ba. Babba yalwa tacewa Gwaggo abin ba sai ya kai ga haka ba abinda za'ayi bari a Kira Yaya Asmau taje ta dubo Sajeeda idan har jikinta ba sauki,da gaskiyar Gwaggo dole a dauko Sajeeda. Da wanan shawarar aka nemo Yaya Asmau da itama take ta san zuwa duba Sajeedan dan tana ranta,ana fada mata ta amince akan zata je,ana sauran kwana biyu da zata taho Abujan. Gwaggo ta bazama nemo magungunan gargajiya tunda take bata tab'a zuwa wajen wani mallami ba sai gashi tayi asubancin zuwa wajen wani shahararen mallami da ya kware a warkar da mutane masu laruran Aljannu da karya sihiri,haka Gwaggo ta hau zayyana masa larurar Sajeeda yace mata bazai iya ganewa ba sai an kawota ya ganta,ya ya tofa addu'oi a ruwan zamzam akan a Kai wa Sajeedan,kafin a bata a daura mata alwala idan ta Sha a shafe mata jikinta, abinda Kuma yafi a kawota ya ganta. Gwaggo haka ta kaiwa Asmau ta mata bayani ta hada da rokon tana zuwa taga alamar Sajeeda jikinta ba sauki ta kirata a waya zata zo su taho da ita dan bazata iya ba. Gwaggo har da kukanta ta d'auko kudi akan ta Kara na mota Yaya Asmau taki karba kasancewar bata san gidan da suka koma a Abuja ba sai ta hau Kiran Kabirun dan ya kwatanta mata sai dai har ta karaci kiransa bai dauka ba,har Yaya Abu ma da ta kirata bata dauka ba,sai lambar Nusrah ta kira Nusrah ta Mata kwatance dan indai ta sauka a tasha duk wanda ta samu ta fadawa sunan unguwa da lambar gidan zai Kai ta har k'ofar gida. Da asubar fari ta d'auko hanya bayan Gwaggo ta rakata har Tasha tana rokon ta tana isa gidan ta mata waya. Koda ta iso bata Sha wahalar samun abun hawa ba tana fada Masa unguwar da lambar gidan yace ta hau su tafi. Tafiyar mintuna Suka iso katafaren gidan,Yaya Asmau taki yarda gidan kabirun aka kawota dan gidan ya wuce tunaninta saboda haduwarsa sai da ta tambayi

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});