Chapter 14
Chapter 14
Sara Mata sai sauke numfashi take. Sajeeda kuwa ta nufi wajen bandakin Kabiru ya Kara matse jikinsa a bayan k'ofa a lokacin da Sajeeda ta dan leleka bandakin daga bakin k'ofa taga ba kowa ta rufo k'ofar Kabiru ya saki numfashin da ya rik'e. Yesmeen taji kamar ta Mata nuni da hannu akan ta duba bayan k'ofar sai dai tana tsoron Kabiru ya kashe ta kamar yadda yayi kirari Sajeeda ta dawo gefen gadon ta zauna ta kai hannun ta Kan Yesmeen tana "Mai kikaci daya b'ata miki ciki"? "Ba abinda naci umma tun dana kwanta nake ta fama da ciwon ciki sai zaryar bandaki nake" "Kin Sha magani"? Gyada mata Kai Yesmeen tayi tana satar kallon k'ofar bandakin tana adduar Ina ma Sajeeda ta Shiga bandakin ta gan Shi. Sajeeda kuwa ta fara magana tana Na farka Zan yi fitsari ban ga Abban ku a daki ba shine na fito na duba ko Yana Palo sai naji kamar tashin magana a d'akin ki Ina Abban ku yaje daddaren nan naga Kuma k'ofar palon a kulle na Kuma duba bandakin baya nan,wai Mai ke faruwa ne Yesmeen na daina gane wa Abban ku,ya canza gabad'aya Kamar bashi ba tunda ya hadu da wanan abokin nasa na fara ganin sauyi a tare dashi,bansan Mai yasa nake ji a jikina tarayyar sa da Abban ku ba alheri bane,na rasa Wanda Zan samu na yiwa magana ya fahimceni Abban ku ya riga da yayi nisa taya haka kawai abokin sa zai d'auko gida sukutum guda ya bashi kyauta ba dangin iya babu na baba ga uban kudin da yake tula masa,hankalina bai kwanta da wanan alherin ba, bani da kwanciyar hankali wallahi dauriya kawai nake tunda muka je wajen mutumin nan godiya nake fama da mugayen mafarkai idan na gaya masa sai ya rufeni da fada dake da Nusrah kawai nake ganin zan iya fadawa damuwa na ku gane yanzu dan Allah Ina Abban ku yaje da tsakar daren nan sai da ya tabbatar da nayi bacci ya tashi ya fice Ina tsoron abokin nan nasa ya koya masa wani mugun halin. Yesmeen kuwa zare ido kawai take ta kasa kwakwaran motsi dan tasan kunnen Kabiru na wajen su. Ganin Sajeeda ta damu tana cigaba da magana yasa ta daure murya can kasa tace "Umma in Sha Allah ba wani matsala ki kwantar da hankalinki addua kawai zamu ta yi masa mu Kuma mu ringa dage wa da Addu'a tunda kince ki na mugun mafarki Ki ringa dan tashi daddare kina addu'oi" Mik'ewa Sajeeda tayi tana "In sha Allah kuwa zan fara Addu'ar bari na duba su Saifullahi idan har ban ga dawowar Abban ku ba sai na dawo dakin ki na kwanta dan bazan iya kwana ni kadai ba. Mik'ewa Sajeeda tayi da sauri tana "kiyi kwanciyar ki umma bari na dubo su Saifullahi" Tayi waje da sauri dan so take ta kwana a d'akin nata ko wani uzurin zai saka ta Shiga bandaki ta ga kabirun duk da zuciyar ta cike take fal da tsoro da fargaba amma daga ganin da tayi wa Kabiru jiya tasan dole akwai wani mumunan abun da yake aikatawa idan ba tsafi ba taya zai yi tsirara Yana zagaya wuta daddare. Ita kanta ta fara tunanin kudin nan da yake cewa abokinsa ya bashi har da kyautar gida ba na Allah da Annabi bane. Kabiru kuwa iska ya kai wa Naushi a lokacin da ya ji Yesmeen nace wa Sajeeda ta koma ta kwanta wato Yesmeen so take ta tona masa asiri idan kuwa Sajeeda ta shigo bandakin ta gan shi ba abinda zai hana ya kashe Yesmeen. Sajeeda kuwa koma wa tayi ta kwanta tana ta tunanin Inda Kabiru yayi daddaren nan ta daga kai ta duba agogo taga karfe uku har da minti goma sha biyar. Tunanin Kiran wayar sa ne ya fado Mata hakane yasa ta mik'e daga kwancen da take ta fito daga d'akin a daidai lokacin da Yesmeen ta fito daga d'akin su Saifullahi. Da sauri tabi bayan Sajeeda tana "umma kin fasa kwanciya a d'akin nawa"? "Zan Kira Abban ku a waya ne naji Inda yaje" Yesmeen bin bayan ta tayi dan ba abinda zai Kai ta komawa d'akin ta. Kabiru kuwa Yana Jin motsin fitar Sajeeda yayi sauri ya fito daga bandakin Yana leka su Yana ganin sun shige d'aki yayi sauri ya fito daga d'akin ya bud'e k'ofar Palo a hankali ya fice Yana sharce gumi. Takaicin sa bai samu ya fesawa Yesmeen turaren mantuwar da aka bashi ba tsoron sa Kar ta fadawa Sajeeda wani abu. Sajeeda kuwa tana shiga d'akin ta,taga wayar Kabiru a gefen gadon. Haka ta zauna a gefen gado ta buga tagumi. Yesmeen kuwa ta zauna a kasa tana ta tauna harshen ta bakin ta kaikai kawai yake Kamar ta fadawa Sajeeda abinda ke faruwa bata san Mai yasa take ganin kamar Kabiru zai iya cutar da ita ba amma idan ta tuna kashedi da rantsuwar da Kabiru yayi akan zai kasheta sai taji gwara ta rufe bakin ta gam sai dai za tayi ta addua Allah ya tona masa asiri Sajeeda ta san halin da yake ciki. Basu jima da Shiga d'akin ba suka ji motsin bud'e k'ofa Sajeeda ta mik'e tsaye da sauri tayi hanyar waje taci Karo da Kabiru da ya hade rai, Tuni taji ta kasa Masa ma magana balle ta Masa tambayar inda yaje daddaren nan,Yesmeen kuwa da sauri ta mik'e Kabiru da ke Jin kamar ya harbeta ya bi ta da kallo Yana "Ke Mai kike yi a d'akin nan"? "Abban Nusrah farkawa nayi ban gan ka ba shine na kirata tazo ta kwanta anan dan tsoro nake ji yau ma nayi mugun mafarki" "Daga yau Kar ta Kara shigowa d'akin nan, ke yarinya ce daga na dan fita asibiti na dawo shine har sai kin wani kirata ta tayaki kwana ke Mai yasa baki da lissafi ne" Fadan borin kunya Kabiru ya rufe Sajeeda dashi ta Inda yake shiga bata nan yake fita ba,Yesmeen kuwa da gudu tayi waje tana Kara Jin tsananin tsoron kabirun. Sajeeda kuwa tsabar bakin ciki da takaici kuka ta fashe dashi dan bata san Mai tayi da har zai rufeta da fada haka ba. Ko kallonta bai yi ba ya kwanciyarsa Yana girgiza kafa. Sajeeda duk maganar da taso ta Masa sai hadiyewa tayi ta kwanta tana tunanin mafita,dan Kabirun ta da ta sani bashi bane wanan,rashin sallahrsa akan lokaci Yana damun ta ta rasa yadda zatayi shekara ashirin da uku ba wasa ba tasan halin sa amma a dare daya ya canza halayensa daga ya fara samun dan canji ita Kam haduwar sa da wanan abokin nasa bai zame mata alheri ba. A idon ta aka fara kiraye kirayen sallah asuba dan bakin ciki bai barta ta koma bacci ba, daga yadda yake girgiza kafa tasan idon sa biyu Kuma bazai tab'a tashi yayi sallah ba,ita kuwa dama fashin sallah take ballantana ta tashi amma tunda ba baccin take ji ba zata tashi tayi alwala ko carbi ne taja. Tana k'ok'arin tashi taji Kabiru ya janyota hakane yasa ta waiga tana kallon shi dan tasan mai yake Shirin yi tunda har ya fara shafata. K'ok'arin janye jikin ta ta fara
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111