Chapter 64
Chapter 64
sosa ko'ina na jikina ba,kasana kuwa sai bulbulo da ruwa yake Mai doyi, Abban Nusrah kuwa ya farka daga baccin da ya fara d'aukar sa ya kalleni yana "Jikin ne Sajeeda sannu bari na dauko miki magani" Ya mik'e ni kuwa na cigaba da sosa jikina da naji kamar wuta ake huramin,yanzu ba iya kasana nake jin kaikaiyin ba duk jikina gabad'aya. Kuka kawai nake Ina Kiran Sunan Allah,ko maganin da Abban Nusrah ke miko min ban iya karba ba,kafin gari ya karasa wayewa jikiina yayi wani irin rudu rudu ya canza kala Kamar ba na mutane ba. Kabiru Hankalin sa ba karamin tashi yayi da yadda yaga jikin Sajeeda ya koma ba dan tuni duk fatar jikinta yayi wani irin duhun kala a idonsa ma sai yaga kamar fatar jikinta ya koma kalar Karen da ya sadu dashi, sallati kawai yake a ransa Yana tunanin abun yi dan shugaban su bai fada masa duk haka Sajeeda zata dawo ba,gashi yace ba abinda zai iya yi a akai haka Sajeeda zata tayi ta fama,da alama Sajeeda dak'yar ma take numfashi, hankali a tashe ya koma dakinsa ya d'auko wayarsa ya Rabiu a waya Yana d'auka ya fara zayyana mishi abinda ke faruwa,Rabiu kuwa ya hau tsara masa abinda zai yi da zai kau da zargin komai a zuciyar Sajeeda,ya kashe wayar ya turo Masa lambar Wanda zasu je wajen sa da bakin su ya zama daya. Kabiru kuwa kamar gaske ya koma d'akin Sajeedan da ta daina ma iya sallati sai hawaye da numfarfashi da take faman yi, Haka ya taso Yaya Abu akan tazo su Kai Sajeeda wani asibitin. Yaya Abu kanta sai da ta tsorata da yadda jikin Sajeedan ya koma, tafiyar mintuna Suka iso wani karamin asibiti batare da b'ata lokaci ba likitan da Kabiru ya Kira ya hau duduba Sajeeda, Kabiru da Yaya Abu na zaune suna kallon sa har ya gama ya fita. Sajeeda Kukan zuci kawai nake dan nasan tawa ta Kare ,ta k'arfi nakeso na damko Yaya Abu na fada mata Kabiru ne ya jefani a halin nan amma na kasa magana dan ji nake jikina Kamar ba nawa ba,abinda yake bani mamaki da Kabiru yadda ya nuna damuwar sa kamar bashi yayi kudi dani ba,har da dan hawayen sa yau daa ce bansan sirrinsa ba cewa zanyi nafi kowa dace da samun miji Mai kaunata dan Yaya Abu sai kwantar Masa da hankali take saboda ya kasa Zama waje daya duk wanan abin fa yasan asibti bazasu iya min magani ba, amma saboda ya nuna bai San komai ba yake ta sintirin kawo ni asibiti,Koda likita ya dawo bayanin da naji Yana yiwa Kabiru da Yaya Abu yasa hawaye ya fara gudu a fuskata,Wai a fadar likitar da nake tunanin hada baki yayi dashi Wai wani kwauro ne ya cijeni,wanda cizon kwaron guba ne,gubar ne ya haifar min da wanan kaikaiyi da canza fatar har ruwan dake zubo min a jikina,matsalar Kuma wanan kwaron ba lailai ko na Sha magani na warke ba sai dai ayi ta adduar sauki na ringa Shan magunguna akai akai, Abban Nusrah da Yaya Abu kuwa sai sallati suke, Abban Nusrah har da hawayensa Yana rik'e likita Wai ya taimaka masa idan da akwai abinda zai iya yi akai,likita kuwa yace ba abinda zai iya Yi akai ya cigaba da bawa Abban Nusrah hakuri akan ya daina daga hankalinsa kawai ya maida hankalina sa wajen kula dani kila a gaba a dace na warke. Abban Nusrah a tunanin sa bansan sirrinsa ba haka yayi ta min sannu Yana rike da hannuna har ruwan da aka samun ya Kare aka sallame mu bayan ya lafto uban magunguna Yaya Abu kuwa sai cewa take wane irin kwarone haka ita dai bata tab'a ji ba. Abban Nusrah kuwa ya hau ce mata akwai yasan ma wata da ya ciza. Haka muka dawo gida, Abban Nusrah ya ringa kula dani,Yana wani tattalani,ni kuwa kullum jikina Kara rikicewa yake a yanzu ko tashi bana iya yi, adduar zuci kawai nake dan wani irin rama nayi,ba abinda kake hangowa a jikina sai kasusuwana,jikina kuwa na ta fidda ruwa mai doyi,yanzu Abban Nusrah bama ya iya kwana a dakina,amma idan garin Allah ya waye kafin ya fita haka zai ta kula dani,har da dan kukansa wai duk ya nuna ya damu da halin da nake ciki,Yaya Asmau kuwa kullum sai ta kirani,ta dubani,ta Kuma shaida min ta saka a ringa min Addu'a ana min saukar ita tafi yarda da makiya ne suka jefe ni ba wani kwauro daya cijeni,daidai da mahaifina da mahaifiyata sai da suka zo dubani,ba Wanda zai zo dubani bai girgiza da yadda na dawo ba,duk Wanda ya tambayi Mai ya sameni haka,Abban Nusrah da Yaya Abu sai su hau bayanin kwaro ne ya cijeni shi yasa na dawo haka, tunda iyayena suka zo nake Neman hanyar da zan fada musu sirrin Abban Nusrah ko Zan samu su tafi dani su nemi mallamai su mun Addu'a,bansan Kuma ta yadda zan fada musu ba dan bana iya magana bansani ba ko wani abu Abban Nusrah yamin da ya saka naji bana iya magana, fadar tashin hankalin da iyayena suka Shiga da halin da nake ciki bata bakine dan mahaifiyata Gwaggo tunda tazo bata da aikin da ya wuce kuka,a gaban idonsu kuwa Abban Nusrah sai Kara kula dani yake, duk dan ya nuna musu Yana kula dani, Na lura so take ta kebbe dani,amma ganin Abban Nusrah yasa ta kasa sakin jikinta tana dubani sai ta fita,mahaifina kuwa kwana daya kawai yayi ya koma,akan zai Nemo min maganin gargajiya kila a dace, ana sauran kwana biyu mahaifiyata ta koma Abban Nusrah ya fita da zumar wai zaije ya dawo akwai kayansu da ya iso da zai je ya gani bazai Dade ba zai dawo. Fitarsa da minti biyar sai ga mahaifiyata ta shigo fuskarta cike da damuwa ta zauna a gefen gadon tana Kare min kallo hawaye ya hau zubo mata tana "Sajeeda Kinga yadda kika dawo kuwa?Wane irin kwarone wanan da zai cijeki ki koma haka,har cizon sa yasa kiringa fitar da ruwa mai wari haka daga gabanki?Wai me ke faruwa da ku ne haka?ya akayi Yesmeen ta makance?mai ya kurmantar da Annur,?na kasa gane Mai ke faruwa da ku haka,na tambayi mijinki yace dare daya kuka wayi gari Annur ya daina iya magana Yesmeen Kuma ta daina gani,duk a cikin shekara daya wanan masifar ta same ku haka mai yake faruwa haka? Gwaggo ta sosa min inda yake min kaikaiyi na hau k'ok'arin na bud'e bakina dan nayi magana amma na kasa alama kawai nake Mata da hannu dan a Kira min Yesmeen ko zan samu ta fadawa mahaifiyata abinda ke faruwa bani da sama da ita,ita zata iya taimaka min na fita daga hannun wanan azzalumin,amma mahaifiyata ta kasa ganewa sai kuka ta saka min tana adduar Allah ya bani lafiya tana Shan alwashin daina bacci dan addua kawai zata ringa min,karshe sai Yaya Abu ce ta shigo d'akin,ta ajiye kumatu tayi jajjir da ita saboda Jin dadin da ta samu da alama rashin lafiyar da nake Dadi yake mata dan tamkar ita ta Zama matar gidan,ita ke girki,ta ajiyewa Abban Nusrah nasa,duk abinda ranta keso kawai take yi,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111