Chapter 55
Chapter 55
ba,mai tayi?laifine dan an tausayawa halin da take ciki,tashi daya Muka wayi gari ta daina gani, iya wanan bai Isa yasa a tausaya mata ba sai ace zaa koreta,yau kina tunanin da Nuratu na rayye zata ji dadin irin yadda kike yiwa yarta ?karki manta fa baa san ranta ta mutu ta barta ba yau da bana rayye ke mai rik'e Yesmeen ce ban taba zaton haka daga wajenki ba" "Ikon Allah Wani Abu akace zaa yiwa Yesmeen din kike zuba wanan dogon bayani,kina magana kamar ni na kashe Nuratu,kina tunanin idan Nusrah ce zata ringa daga miki hankali haka,yarinya tun jiya ta Hana mu sukuni,kike ta zuba dogon bayani kinsan da mota ta kadeta da ta fita dinan dangin babanta ba yarda zasu yi ba karshenta sai sun kulle ki" "Ai na ma gama magana Yaya Abu Ni ke auren Sajeeda ba ita ke Aurena ba bata isa ta juya ni ba a karkashin ikona take da yardata ta rik'e Yesmeen a yanzu Kuma nace ta maida Yesmeen wajen mahaifin ta tunda Yana rayye ba mutuwa yayi ba a goben Nan Zan maidata" Tunda ya fara magana wani irin Abu naji ya tsaya min a zuciya,wutar kiyayarsa ruruwa kawai yake a raina ji nake kamar na samo wuka nayi ta yanyanka shi yanzu alwashin da nake Sha ma bazai ci kudin nan ba yadda yake san yaga ya kasheni sai dai mu tafi tare bana Masa fatan Rahamar Allah daga Rana irin ta yau har zuwa karshen numfashina addu'oi masifa da balai Zan ta Masa,tunda har dani zai yi kudi,ba abinda zai hana naso ganin bayan sa. Ganin Yana k'ok'arin barin palon Yana ta sheka rantsuwa yasa na fara magana cikin bacin rai Ina Jin ruwanan na zubo min Mai doyi "Wallahi ba inda zata je Abban Nusrah idan har ka dage ka gaji da rukonta sai ka sallameni nima na tafi,haka kawai ba abinda ta maka zaka koreta,baka tashi korarta ba sai da ta daina gani,mai zaka cewa mahaifinta ya makantar Mata da ido,a haka na d'auko ta,har yanzu baka ji a jikinka mutane zasu fara zargin akwai wani abu dake faruwa a gidan ka ba kasa da wata biyar ka Zama hamshakin mai kudi,Dan cikin ka ya kurmance yanzu itama Yesmeen ta makance kila nan gaba ma mutuwa za'ayi,duk wani abu na faruwa da dalili banda na gidanan,Koda kaddara Allah ya Aiko akan ce ga dalili kafin aukuwar kaddarar amma na gidanmu daban ne Annur daga kwanciya bacci ya tashi ya daina magana Yesmeen daga kunna fitila ta daina gani,sai nayi magana ace ba haka ba idan har ka shirya korar Yesmeen ka dawo mata da ganin ta sai ta bar gidanan" "Yaya Abu Kinga yadda ta juya zancen nan ko,banda Sajeeda bata da ilimi bata san yadda Allah ke juye lamarin sa dare daya ba,a cikin awa daya idan Allah ya so azurta bawan sa a yanzu Allah zaiyi silar da zai yi arziki,yanzu Mai ya hada kurmancewar Annur da makancewar Yesmeen da arzikin da Allah yamin yanzu ace matata ke min wanan zargin idan wani taji yana so ya zargeni ita ba mai hanawa bane,wanan wane irin abu ne,yanzu ba abin zargi a wajen ki sai ni kenan Shekara ashirin da uku muna tare ace baki san halina ba?baki San abinda zan yi da Wanda bazan iya ba mai kike nufi duk da kalmomin nan da kikayi da mutane zasu fara zargina"? Kallona kawai yake Yana hucci cikin bacin rai Yaya Abu kuwa ta fara bashi hakuri tana "Hakuri zaka yi Kabiru Sajeeda halin ta sai ita na rasa wacce iri ce ita idan har dan ance zaa Mai da Yesmeen take wanan maganganun sai kayi hakuri ka barta kana kallo ma ni da nake yayarta yadda ta hayyaya ko min kamar zata kawo min duka,yanzu da mutane na nan kaga sai su dauka ni muguwa ce Allah dai ya kyauta "Kuna dai kallon irin abinda take min toh wallahi na fara gajiya Sajeeda bata San darajar miji ba duk maganar daya fito a bakin ta fadamin kawai take ni kuwa na gaji bazan dauka ba" "Ya bazaka gaji dani ba tunda ka Gama Dani ya bazaka gaji ba tunda kayi kudi dani,ai a yanzu bani da wani amfani a wajen ka tunda har ka sadu da kare kazo ka sadu dani,bani da abin mora yanzu dole ka gaji dani" Abinda naso Fadi kenan sai na juye da "Tunda bansan darajar miji ba ya zaayi kenan"? Na jefa masa tambayar Ina ciza lebbena dan takaicin maganar daya fito a bakina "Aure zan Kara Sajeeda idan na Kara Aure watakila ki shiga hankalin ki" Daga haka ya juya a fusace yayi d'akin sa na bi shi da kallo hawaye na zuraro min inama Yesmeen ta fadamin da wuri kafin Kabiru ya cutar dani,dama sai da na ayyana haka a raina kila ya zabi yayi kudi dani ne Saboda ya kau dani yayi aurensa yaji dadin rayuwarsa,ni Dana Sha wahala dashi a madadin ma idan gajiya yayi dani ya sauwake min cikin ruwan sanyi na tafi da lafiya ta shine ya zabi ya cutar dani,yadda nake Jin kasana nasan Abu ne mawuyaci na dawo yadda nake,duk a tunaninsa bansan sirrinsa ba,yau ban da Ina tsoron jefa Yesmeen a cikin masifa da a yau Kabiru ya gane kuransa dan sai na Tara Masa jama'a,Amma a yanzu nasan mai Zan yi Dan idan har na bar maganar a cikina zuciyata na iya fashewa dan bakin ciki. A haka naja kafata na shige daki Ina jiyo muryar Yaya Abu na idan bana so ayimin kishiyar sai na Shiga hankalina da itace a d'aular da nake ciki da an sha mamaki dama idan Dadi yayi wa mutum yawa sai yace Dadi kasheni. Ban juya ma na kalleta ba har shige d'akina Nusrah ta biyoni bana Jin zan iya Mata wani magana yanzu dan Ni kadai nasan mai nake ji ga ciwon zuciya ga na jiki. Haka ta karaci zamanta ta gama koke kokenta akan makancewar Yesmeen tayi kasa da murya akan na taimaka na fada mata abinda nace Zan fada mata dan idan ta koma gida ba lailai ta samu nutsuwa ba haka za tayi ta tunani Ce mata nayi Kar ta damu zamu yi waya ba wani abu bane,bana jin a yadda na ganta a cikin damuwa akwai abinda zan iya gaya Mata haka ta zauna a d'akin tayi ta zuba min Sannu kafin ta tafi gidan ta ma sai da ta Mana abincin dare sai tausayina take tana yanzu wa zai na tayani aikace aikacen gidan tunda Yesmeen bata gani, Murmushi kawai na Mata nace kar ta damu su Saifullahi zasu ringa tayani tunda duk sun iya ji nake kamar na fada mata Yesmeen na gani yadda naga ta damu sai Kuma na fasa Ina tunanin mata magana ko ta waya ne ya zama dole na tashi tsaye na nemi mai taimaka min da Addu'a na kubuta daga hannun wanan azzalumin mutumin. Yesmeen Tunda Yaya Abu ta d'auko ta daga d'akin Sajeeda taji gabad'aya ta kasa samun nutsuwa,tayi nadamar tona sirrin ga Sajeeda yafi a kirga, dan tasan ba lailai ta iya dannewa ba zata iya tarar Kabiru da maganar. Kuka kawai take tana tunanin abin da ya Kamata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111