Chapter 6
Chapter 6
akan gado Ko a wani wajen kaga da kunya ko" ""Umm ni dai na tafi massallaci sai ki dage da nema" Yayi waje. Sajeeda Kuma ta shige bandaki dan tayi wanka ta yanke idan ta iddar da Sallah sai ta gyara d'akin ko zata gani. Kabiru kuwa yana fita ya labe daga waje Yana kallon lokacin da su Saifullahi suka fito daga gidan suka nufi massallacin. Sai Kuma yaji kirjin sa ya masa nauyi Mai bambanci Arne da musulmi sallah ce fa, yanzu haka zai yi sati kenan ba saka goshin sa a kasa ba? tuna irin kudin da zai yi yasa ya ture tunanin a ransa dan a wanan yanayin da yake ciki kudi kawai shi ne burin sa dan Rabiu yace masa Rabin masu kudin garin nan duk ta haka suka yi kudin su. Sai da ya ga yaran sun dawo sun shige ciki shima ya fito daga lungun da ya b'uya ya Shiga gidan. Koda ya Shiga daki Sajeeda ya Tarar ta daddage da neman pant da hijabin da tayi sallah a jikinta har zanin gadon ta canza sabida Neman da take shi kuwa ya hade rai dan ko da wasa baya so ya bata fuskaar da zata ishe shi da maganar pant din ta. "Abban Nusrah kaga har daga katitar nan nayi wlh Babu pant ba dalilin sa" "Mtsss kina da matsala wlh Tom mai Kika daddage kina nema daya ne dake"? "Aa ba dayane dani ba Ina ta mamakin yanda zan kwana da abu a gefena yanzu na duba ko sama ko kasa bangani ba" "Baki da abin yi ne Sajeeda ki cigaba da nema idan Kuma ba barawone ya shigo ya rasa mai zai dauka sai wandon ki" Kabiru yace tare da Jan siririn tsaki,ya kwanta Yana zai koma bacci karfe goma ta tashe shi daga bacci zai je wajen abokinsa da ya bashi kyautar kudi yace masa yaje Yana san ganin sa. Da toh ta bishi ta fito daga dakin tana tunanin kila wani wajen ma pant din yayi ta tsaya wahalar da kanta. Tare suka yi abincin karyawa da Yesmeen dake bata labari taji motsi jiya a bayan windonta,ko baccin arziki bata yi ba Dariya Sajeeda ta saka mata ta ringa ce mata matsoraciya yanzu haka b'eraye ne. Sajeeda Tare muka ci abinci da Abban Nusrah da yazo fita ya bani Dubu biyar Wai nayi cefane har ga Allah daga jiya zuwa yau bansan kalar Farin ciki da Addu'ar da nayi wa Abban Nusrah ba, hakika ya kyautata wa nida yarana,dan ko da Abban su ya fita suka shigo hirar kyautar da aka musu kawai suke Annur kuwa ya hau cewa "Nayi mafarki Abba ya Zama mugun Mai kudi Wai ya gina wani gidan bene duk muna ta murna amma ban ga umma a gidan ba" Murmushi na saki Ina "idan baka gani a gidan ba wata Abban ku ya auro kenan,a lailai auta kyautar da aka ma ya maka dadi irin wanan mafarki haka. Tare muka yi aikin abincin da aka kawo min da Yesmeen dan Kamar na mayar nima na dan huta tunda na samu Yan canji,dan daidaikun Rana ne baa kawo min aikatau Kuma har ya zame min jiki. Da yamma Ina d'aki sai ga Abban Nusrah ya shigo gidan da sallama fuskar sa Kamar gonar auduga ba kowa a gidan sai ni kadai dan duka yaran sun tafi islamiya. Nima ganin fuskarsa a washe yasa nima na washe bakina Ina "Abban Nusrah Mai muka samu ne naga fuskar ka d'auke da Annuri haka" Zama yayi a gefena Yana "Sajeeda Ina ga mun kusa zama masu kudi" "Allah Abban Nusrah abokin naka ya nemo ma aikin ne"? "Daga wajen sa nake yanzu haka ai yanzu ma zama bai Kama ki ba tashi Zaki yi mu tafi ki tayani yi masa godiya Kinga yau ma kudin daya bani kyauta Sajeeda" Gwalo ido nayi a lokacin daya bud'e ledar dake hannun sa wrapper Dubu Dubu ne guda biyar,mik'ewa nayi na dafe kirjina Ina "Abban Nusrah duka wanan kudin ya baka aikin me yake yi haka"? "Ke kinsan kudin sa kuwa wanan ai ba komai ne ma a wajen sa ke baki ga alkawarukan da yamin ba a ciki kuwa har da kyautar gida yace bazai manta alherin da na masa muna Yara ba" Kudin daya dora a cinyata kawai nake juyawa har ga Allah sai najini a tsorace tambayoyi nake so na yiwa Abban Nusrah amma bana so na rusa Farin ciki da yake ciki,a wanan zamanin har wane irin kudine da shi haka jiya ya bashi kyautar dubu dari biyu yau Kuma ya d'auko dari biyar ya bashi. "Wai ya na ga ba kya farinciki ne Sajeeda Allah ne ya turo min shi ya taimaka min fa Allah yasan tsawon shekarun da na dauka Ina aikin wahala" Murmushi yak'e nayi Ina "ba haka bane Abban Nusrah Mai zai hana ni murna kawai Ina ta mamakin yanda daga jiya zuwa yau ya iya baka kyautar dubu dari bakwai zugudum a wanan zamani ko dan uwan ka ke da wanan kudin ba lailai ya iya baka irin wanan kyautar ba" "A wajen masu kudi kyautar dubu dari bakwai ba komai bane Sajeeda sabida dai bamu da kudin ne shi yasa kike ganin yawan kudin, ba za ki gane abinda na ke fada ba sai anjima idan mun je gidan Zaki tabbatar da ko miliyan daya ya bada kyautarsa ba zai ji komai ba" "Allah ya saka masa da alheri" "Ameen Ameen ai idan ya samo min aikin nan sai na siya miki tsalallen mota,su Saifullahi ma sai na bi su da motoci" "Allah ya yarda yasa arzikin na alheri ne a gare mu Abban Nusrah kasan wani arzikin masifa ne,ni wlh a rayuwata rufin asiri kawai nake so bani da wanan burikan tashin hankalin indai zanci sau uku a rana yarana su kawo bukatar su na musu ba tare da na gaza ba wlh Alhamdulillah" "Sajeeda kenan yanzu dai tashi kije ki boye mana kudin ki zo ki fada min Abubuwan da ake bukata a gidan" D'aki naje na boye kudin na dawo wajen sa duk jikina a sanyaye bansan mai yasa ban ji Ina mugun Farin ciki ba shi kuwa sai zuba yake yana lissafa yadda idan ya samu kudi zai canja mana rayuwa ko girki da na so dorawa hana ni yayi yace yau bazaa yi girki ba Kuma bai yarda na Kara karbar aikatau ba. Koda Yara suka dawo haka ya tara su Yana tambayar su abinda suke so. Tuni duk suka haukace da murna daga Mai cewa machine yake so sai Mai cewa keke yake so Annur kuwa sai tsalle yake Yana mafarkin sa ya tabbata Abban su ya Zama Mai kudi,Abban Nusrah kuwa sai washe baki yake Yana su Kara saka su a addua ai Yana ganin nan da sati biyu zamu bar gidanan. Ni dai da ido nake bin sa yanda ya hakikance Yana zuba lissafi Taya mutumin da ba shi da ko asi sai ya fita yayi buga buga tashi daya ya ringa wanan lissafe liisafen sai Kuma nayi tunanin Allah Kan iya azurta bawan sa a dare daya zai Kuma iya talauta bawan sa a cikin mintuna. Bayan sallah isha yace na shirya mu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111