Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 62

Chapter 62

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

su. Sai da suka gaisa da yaya Abu ya shige d'akinsa sai da yayi wanka ya fito yana jin sa a cikin nishadi,batun sallah kuwa babu,dan yanzu idan akwai abinda ke Masa wahala bai wuce sallah ba,dan ba kowane lokaci yake yi ba,yau ba karamin dadi yaji da Yan matan da Rabiu ya hada shi dasu ba,har ga Allah daya daga cikin su ta kwanta masa Husna ya samu yadda yake so,dan har lambarta ya karba dan ji yayi ma zai iya aurenta bata fi sa'ar Yesmeen ba. Koda ya fito d'akin Sajeeda ya shige dan ya dubata. Sajeeda Mafarkin da nayi ya tsaya min a zuciya dan kasa ma samun nutsuwa nayi,sai da na saka Saifullahi ya ruko mun hannun Yesmeen ya kawota d'akina, daga mafarkin nan da nayi nasan cewar dagani har Yesmeen muna cikin mugun hatsari nama Shiga hatsarin tunda Kabiru ya gama dani, Yesmeen na ganin Saifullah ya bar d'akin tayi saurin Mai do da fuskarta kasa tana "Umma ya jikinki"? Sai na cije lebbena dan ni kadai nasan mai nake ji a jikina dan yanzu kasana ma ji nayi Yana numfashi shi kadai, "Umma dan Allah dan Annabi karki nunawa Abba kinsan komai wallahi dazu ma sai da ya zo har dakina ya shakeni ya Sha alwashin kasheni idan har sirrinsa ya fita Umma wallahi Abba zai iya kasheni ki taimaka min ki rufe sirrin nan, mu dage da Addu'a da saukar Qur'ani, in Sha Allah zaki warke idan guduwa ma zamu yi sai mu gudu" Girgiza kaina nayi ina "Yesmeen ranki da nawa a hannun Allah yake yau ko mutuwa nayi,lokacina ne yayi,ji nake idan ban tona sirrinsa ba bazan samu kwanciyar hankali ba,dan ya fara tunani tura su Saifullahi kasar waje,idan har zai iya mun wanan cutar ya kurmantar da Annur dan ya siyar da su Saifullahi ba wahala zai Masa ba gwara na nuna masa nasan sirrin sa" Yesmeen zubewa tayi a gabana ta hau magiya sai kuka take tana na rufa mata asiri Abban nusrah kasheta zaiyi idan na nuna masa nasani Na ruko hannun ta Ina "Ki kwantar da hankalin ki bazan nuna Masa ke Kika fadamin ba,ba Kuma magana Zan Masa ba da kaina nake so na gano sirrin sa ya Kuma san cewar nagani din ba fada min aka yi ba da naso na fadawa su Saifullahi sirrin sa dan su san cewar zai iya yin kudin dasu suma amma na fasa fada musu zan dai hana tafiyar tasu" Yesmeen magiya kawai take akan na rufa Mata asiri sai da na rantse mata akan bazan fada masa komai ba ta samu nutsuwa dan na yanke abinda zan yi bazai tab'a zargin Yesmeen ce ta fada min wani abu ba. Bayan fitar Yesmeen daga d'akin Yaya Asmau ta shigo na fada mata ta bar Yesmeen ba sai ta tafi da ita ba Yaya Asmau tafi nuna kulawar ta a kaina akan wacce na Kira da yayata ni gani nake ma Kamar murna take da rashin lafiyata tunda duk zata yi abinda ranta ke so. Ba Mai hanata. Kafin Yaya Asmau ta koma dakinta na Kara rokonta akan ta saka mallamai suyi min Addu'a da sauka tamun alkawari da zata saka ayi min Addu'a. Ba ta kuwa bar dakina ba sai da ta tabbatar da naci abinci Yaya Abu bata lekoni ba sai wajen goma ta shigo tana har yanzu bata ga Abban Nusrah ya dawo ba dama yana dadewa hakane"? Kai kawai na gyada mata. Ta sa Kai ta fita. Tana fita na fara susa dan wani irin kaikaiyi naji kamar na cire gabana na Yar ga ruwan dake bulbulo min duk wanan masifar uban yayana ne ya jefani saboda abin duniya. Haka na kwanta Ina zubar hawaye idan ya lafa na daina idan ya motsa na cigaba da susa,Ina Jin lokacin da Abban Nusrah ya dawo na dauka zai lekoni sai naji shiru Wanda hakan na nufin dakinsa ya wuce sai da ya dau tsawon lokaci naga ya turo k'ofar d'akin ya shigo sanye da jallabiya kudin haram sun zauna masa dan har wani kiba yayi Yana sheki. Ya zauna a gefen gadon Yana "Sannu Sajeeda ya jikin naki"? Mik'ewa nayi na zauna Ina "Abban Nusrah dare daya na wayi gari da wanan masifar a jikina,a ranar da na fara Jin canji a jikina a ranar da ka kusanceni ne na karshe Abban Nusrah shekara ashirin da doriya muna tare Kai ma kasan ban taba cuta makamancin wanan ba,Mai zai jawo min wanan masifar"? Wani irin kallo ya fara min cikin hade rai ya fara magana Yana "Toh mai kike nufi da tunda na kusance ki na karshe kika ji jikinki ya canza kina nufin ni na saka Miki cuta ko me?idan a jikina kika kwashi wanan cutar ni zaki gani haka ne,wanan cutar kila a bandaki Kika kwaso ko a wani wajen dan haka ki cigaba kawai da Shan magungunan da aka Rubuto miki Zaki warke a hankali kinci abinci"? Ba karamin daurewa nayi na danne abinda nake ji ba,na gyada masa Kai da naci abincin ya fara magana Yana "Ina ganin ya Kamata Yaya Abu tazo ta ringa tayaki kwana ni sai na ringa kwana a dakina har zuwa lokacin da zaki warke" "Tun baaje koina ba Abban Nusrah ka fara guduna kenan bazaka iya kwana da ni waje daya ba"? "Aaa Sajeeda akan me Zan gujeki,kawai Ina ganin a yanzu kina bukatar kulawa sosai,shi yasa nace tazo ta ringa kwana anan ai na dan lokacine" "Abban Nusrah bana so Yaya Abu tazo ta kwana Kai nake so ka kwana din idan Kuma dan larurata zaka ki kwana dani shikenan ba komai" Nace Ina Jin kamar na shako shi har sai ya daina numfashi so nake na Kama Abban Nusrah da kaina shiyasa nake so mu ringa kwana waje daya. Kabiru kuwa ganin Sajeeda ta dage yasa yace zai kwana din zuciyar sa fal da tunanin yadda zai gudanar da abunsa ba tare da su Yaya Abu sun gan shi ba. Haka ya ringa sintiri daga dakinsa zuwa na Sajeeda Yana tunanin yadda zai yi,bai san mai yasa wankan sai a bayan gidan zai yi ba ji yake Kamar ya taso su Yaya Abun yace su koma dakinsa su kwanta. Haka yayi ta juye juye har Sha biyun na dare Yana Jin saukar numfashin Sajeeda dake nuni tayi nisa a bacci,a hankali ya lekata ya ga baccin dai take cikin sand'a ya mik'e ya fito daga d'akin. Ya nufi bakin k'ofar d'akin Yesmeen ya Kara kunnensa Dan yaji ko zai jiyo motsin su ba abinda yake ji sai karar fanka. Cikin sand'a ya koma dakinsa ya jawo tukunyar kasar da ke d'auke da ruwan maganin ya tube Zigidir Yana jira daya ta karasa yayi waje yayi wankan. Sajeeda Duk abinda yake yi Ina kallon sa rufe idona kawai nayi Kamar Mai baccin Yana fita na bud'e idona kila wani abun zai aikata tunda Yesmeen tace na ringa fitowa karfe biyu na dare Zan ganewa idona. Gabana faduwa kawai yake a lokacin da na mik'e tsaye Ina Jin kamar na Fadi saboda rashin kwarin jiki cikin sand'a na isa bakin k'ofar Ina lek'e ta ramin mukulin k'ofar. A Kan idona yazo ya fito daga d'akin sa tsirara

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});