Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mata ido ita kuwa sai ihun idon ta yaji yake. Sajeeda da hankalinta ya Kai kololuwa wajen tashi ta hau magana tana "Abban Nusrah ko asibiti zamu Kai ta taki fada Mana mai ya samu idon ta. "Taya zamu kai ta asibiti bayan bata fada mana Mai ya samu idon ta ba sai ihun da ta cika wa mutane kunne dashi mai ya samu idon naki"? Yesmeen idon ta ta cigaba da murzawa sai da Kabiru ya Kara daka mata tsawa dan ya tabbatar da zargin da yake yi Ta fara magana tana "Abba fitila na kunna shine glass din ya fado sai naji yaji ya shigar min ido,idona Kamar an watsa barkono" "Sakarci ne kawai irin naki daga kunna fitila idon ki zai hau yaji ki wuce bandaki ki wanke fuskar ki" "Abban Nusrah ko dai asibiti zamu Kai ta" "Wane irin asibiti wai sai kace wani babban abu sakalci ne kawai irin na yarinya nan dalla wuce kije ki wanke idonki " Kabiru yace a dan tsawace ya juya ya bar d'akin cikin tsananin murna da mamakin yadda akayi Yesmeen ta kunna fitilar a yau yake Shirin b'atar da ita sai gashi ta saukaka Masa aiki komai ya zo masa cikin sauki Sajeeda kuwa bandakin taja Yesmeen ta hau wanke mata fuska Yesmeen na cigaba da ihun yaji,duk abinda Sajeeda take yi dauriya kawai take dan ba kwari ne da ita ba Koda Suka fito kasan murya Sajeeda ta hau magana tana "Dan Allah ki bar ihun Nan Yesmeen Kara daga min hankali kike ki barni naji da abinda ke damuna" Yesmeen har lokacin murza idon ta take abinda taji Sajeeda tace yasa ta daina murza idon tana "Umma Baki da lafiya ne har yanzu? "Bani da lafiya Yesmeen baki ga ko fitowa na kasa yi ba yau ihunki ne ya fito dani yanzu kin daina Jin yajin" Kikifta ido Yesmeen ta hau yi tana "dishi dishi nake gani umma har yanzu Ina Jin yaji" "Ba dole ba kin murza idon da yawa ki daina murzawa a hankali zaki ga kin daina gani dishi dishin,mamanki na hanya ma ta kirani a waya ki daure ki Shiga kitchen ki sama musu abu" "Umma wlh bazan iya Shiga kitchen ba dusu dusu nake gani" Sajeeda na k'ok'arin magana Kabiru da ya dawo dakin bayan ya gama waya da Rabiu yace "Ki barta Sajeeda zoki wuce ki kwanta itama ki barta tunda tace dishi dishi take gani,ai bazai Yu ta iya wani abu ba kafin su iso Zan samo musu abinda zasu ci ita Kuma idan na fita Zan samo Mata maganin ciwon ido Allah ya sauwake" Bari nazo na kwashe glass din nan Kar wani yazo ya taka Sajeeda yadda take Jin kaikaiyi yasa ta saurin mik'ewa duk da kamar ta zub'e saboda rashin kwari haka ta fice daga d'akin ta koma d'akinta ta hau susa tana kwalla Kabiru kuwa Yana ganin fitar ta yayi sauri ya fara duduba dutsen maganin daya saka a fitilar dan bai San Mai yasa yake Jin Kamar Yesmeen karya take a yanzu da yayi waya da Rabiu yake fada masa anya ba karya Yesmeen take ba ta gano shirin sa tunda jiya daya so tilasta mata ki tayi taya tashi daya zata je ta kunna fitilar" Hakane yasa yace ya duba dutsen indai ya gani a kasa tabbas kunna fitilar tayi idan kuwa bai gani ba karya take bata kunna ba. Yana cikin dube duben ya hango dutsen a wajen kofa,da sauri yaje ya dauki dutsen ya saka a Aljihunsa Yana ji Kamar an Masa bushara da gidan Aljanna wani irin kallo ya zubawa Yesmeen da har lokacin murza idon ta kawai take,yayi kasa da murya Yana "Sai naga da wane idon zaki cigaba da munafirci ke da gani sai dai a lahira" Ya fice daga d'akin da sauri. Wajen Sha biyu yayar Sajeeda da Asmau suka iso gidan, Kabiru ne ya d'auko su a Tasha a lokacin da Suka bugo waya akan sun iso dan baa garin suke ba daga Malumfashi suka zo dan Sajeeda duk haifaffun can ne har kabirun da ya zama dan Aminin mahaifinsu tsabar abotar Yasa Suka hada yayansu Aure,da fari Nuratu mahaifiyar Yesmeen Kabiru yaso aura ita Kuma a lokacin sai ta nuna Bata kaunar sa hakane yasa ya koma Kan Sajeeda da ta amsa tayin soyayyar sa iyayensu da suka Dade suna san zumunci ya Kara kulluwa a tsakanin su suka shige musu gaba wajen hada auren. Mallam Ayuba shine mahaifin Sajeeda yaransa hud'u akwai Garba Zainabu Abu da suke kiran ta da Yaya Abu sai Sajeeda sai Nuratu mahaifiyar Yesmeen da ta kasance Auta. Duk da Sajeeda ke bin Yaya Abu basu fiye shiri Kamar yadda take Shiri da Nuratu ba,dan Nuratu mahaifiyar Yesmeen nada balain saukin kai Kamar yadda itama Sajeeda ke da saukin Kai,Yaya Abu kuwa tana da balain zafi dan ko su bata daga musu kafa idan abu ya hado su,ba Wanda bai San bata da dadin shaani da dadin zama ba,hakane yasa Koda Nuratu ta rasu Sajeeda ta dage ita zata rik'e Yesmeen dan tasan,Yaya Abu bazata iya rik'e Yesmeen da amana ba. Yaya Abu shekara biyu da suka wuce mijinta ya rasu,yarta daya mace itama tayi aure a can Malumfashi,labarin dake Kai musu a can garin akan Kabiru ya zama Mai kudi yasa suka taho dan su gane wa idon su,dama Yaya Abu ta Dade tana san ta zauna a birni dan ko da can ji take dama itace a matsayin Sajeeda dake Aure a birni,a Kuma idonta a lokacin Sajeeda tana cikin Jin dadi da take Jin dama itace. Bata san tazo ita kadai hakane yasa ta taho da Yar kanwar mahaifiyar su Asmau wanan kenan" Tunda Suka shigo harabar gidan Yaya Abu take ta kalle kalle tana mamakin girman gidan,daga motar ma da Kabiru ya dauko su tasan cewar kudi ya zauna ba karya. A haka Kabiru yayi musu jagora har cikin palon sai da suka zauna ya tafi d'akin Kiran Sajeeda. Sajeeda A yanzu bazan iya fadar tashin hankalin da nake ciki ba dan wanan ruwa mai doyin ne ha sake zubo min zuwa yanzu na fara zargin wanan masifar Abban Nusrah ne ya saka min dan tsawon zaman mu hakan bata tab'a faruwa dani ba,ba bandakin wasu nake Shiga ba balle nace a bandaki mutane na kwasowa kaina cuta,bansan dai zargin da Zan yiwa Abban Nusrah ba,dan yadda nake fama da kaikayi banga yana yi ba,har yanzu ban manta shekaranjiya da ya kusanceni yadda naji jikinsa kamar ba nashi ba jikina ya dauki sanyi na Rasa tunanin da zanyi,Ina kuka na shige bandaki na Kara wanke jikina na fito a daidai lokacin da ya shigo d'akin Yana "Yaya Abu sun iso tana Palo ki fito ki same su zanje na samo musu abu basu kadai ba duka gidan gabad'aya tunda Yesmeen na fama da matsalar ido" "Abban Nusrah har yanzu ruwa mai doyin nan zubo min yake kuma" "Ya isa haka Sajeeda yanzu ba lokacin magana bane ba da bak'i a gidan ki bari idan na dawo sai muje asibiti kifito suna Palo" Daga haka ya fice daga d'akin nabi bayansa da kallo har ya fice. Haka na daure nayi waje dan banaso Yaya Abu ta gane

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});