Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

binne abu sai da ya zo matakin karshe Yesmeen ta kashe shi. Hawaye suka Kara zubo masa daya tuna kalar wahalar da ya Sha har ciwo yaji a garin gudu dayaje makabarta binne abu, Sajeeda kuwa cak ta tsaya tana kallon shi a lokacin da taga Wai duk wanan abin saboda Karen da ya kawo ne,tsabar mamaki kasa ma matsowa tayi Saboda yadda taga ya fice a hayyacin sa har da kuka,ko da dan cikinsa ne ya rasu iya tashin hankalin da zai nuna kenan, saboda Karen dama yake kirarin kashe Yesmeen har da kukansa.? Kabiru hanyar waje yayi Yana ji Ina ma mafarki yake yi ya Kara yin bayan gida yana kallon Karen,ko kashe Yesmeen yayi yanzu baya Jin zai hucce,zai so ya azabtar da Yesmeen,zai so yaga Yesmeen ta Sha wahala kafin ma ya kasheta. Da Jan kafa ya juya yayi hanyar waje dan wajen Rabiu zaije ya fada Masa duk Abubuwan da suka faru. Sajeeda kuwa har ya fice mamaki bai saketa ba kanta yayi mugun daurewa da wanan al amari dama duk wanan tashin hankalin akan Karen da Kabiru ya kawo ne tana Jin motsin fitarsa. Ta buga k'ofar toilet din tana "ki bud'e Yesmeen ya fita" Yesmeen bud'e k'ofar tayi har lokacin jikinta rawa yake idonta yayi jajjur saboda kukan da ta Sha. Koda ta fito Sajeeda ido ta zuba mata dan bama tasan tunanin da za tayi ba a yanzu A hankali ta Kira sunan Yesmeen tana "Yesmeen da gaske ne ke Kika kashe Karen da Abban ku ya kawo"? Yesmeen bata iya magana ba dan batasan yadda zata yiwa Sajeeda bayani ba tunda idan har ta fada Mata ita ta kashe Karen sai ta tambayeta dalili. "Yesmeen Mai yasa Kika kashe Karen Wai Mai ke faruwane na kasa gane abinda ke faruwa Mai yasa Kika kashe karen"? "Umma yadda kike mafarki da karen nan haka nake mafarki da Karen ko bacci bana iya yi, haka Zan ta mafarki ya shigo Yana k'ok'awa dani idan kinzo cetona sai ya koma kanki hankalina ya kasa kwanciya da Karen a gidan nan shi yasa na saka masa maganin b'era" Yesmeen ta karashe tana mamakin yadda ta samu tayiwa Sajeeda karya dan bazata iya fitowa ta fadawa Sajeeda gaskiyar abinda ya faru ba dan da ace duk a hirar su ta tab'a zargin kabirun ne sai ta fada Mata,bata taba zargin sa ba tafi zargin abokinsa idan ta fito ta fada mata abinda ke faruwa ba lailai ta fahimceta ko ta yarda da ita ba" "Da kinsani baki kashe shi ba Yesmeen tunda na fada miki gobe yace zai maida Karen wajen Mai shi,ransa yayi mugun b'aci da abinda kika yi,ni tunda nake dashi ma ban tab'a ganin bacin ransa haka ba abin ya bani mamaki akan Kare hankalin sa ya tashi haka har da kukan sa wlh har yanzu mamaki nake na d'auka wani mugun abu Kika masa Allah dai ya kyauta Yesmeen abinda za'ayi ki hada kayan ki kala biyu kije wajen hajiya kareema kice nace kiyi kwana biyu zuwa lokacin nasan Abban ku ya hucce sai na Miki waya ki dawo" Yesmeen jiki na rawa ta hau hada kayanta dan ko Sajeeda bata ce ta tafi wani wajen ba bata isa ta kwana a gidan ba,tasan Kabiru bazai tab'a barin ta ba dole zai mata wani Abu,idan har zai iya cutar da Sajeeda matar sa uwar yayansa wacce ita da bazai cutar da ita ba. Tana gama hada kayan ta Sajeeda ta d'auko kudi ta bata akan tayi kudin mota dan hajiya kareema kawar tace a Kuma tsohon unguwar su take. Koda ta karba har tazo fita ta dawo baya tana kallon Sajeeda ji take Kamar ta rik'e hannun ta ta fada Mata duk abinda ke faruwa,sau uku tana gwada bud'e bakin ta dan ta fadawa Sajeeda abinda ke faruwa sai taji ta kasa,haka kawai hawaye ya hau zubo mata gani take idan ta tafi Kabiru zai cutar da ita amma ba yadda za tayi. Sajeeda dungure Mata Kai tayi tana "ke Kika jawowa kanki ai da kinyi hakuri da gobe zai fitar mana da Karen daga gidanan kije idan na samu na shawo Kan sa yau Zan kiraki ki dawo yau gidan wani iri zai yi idan bakya Nan" "Umma Dan Allah ki dage da Addu'a umma Ina yawan mafarki marasa dadi umma karki yi wasa da Addu'a Kamar yadda kike zargin abokin Abba nima na fara zargin sa dan Allah umma kiringa addua kina yi mana" Murmushi Sajeeda ta saki tana "Ina Addu'a yata in Sha Allah ba abinda ya Isa ya mana har sadaka zan fara yi dan sadaka maganin masifa ce in Sha Allah ba abinda zai iya yi mana idan tarayyar sa da Abban ku ba alheri bane Ina rokon Allah ya kawo karshen abotar su Allah ya Miki albarka" Ameen umma Yesmeen tace tana jin zuciyarta wani iri bazata yafewa kanta ba idan har wani Abu ya samu Sajeeda Anya bazata tsaya ta fada Mata gaskiya ba Mai yasa Sajeeda ta kasa d'aukar haske a duk abinda ya faru,daga tashin hankalin da Kabiru ya nuna na mutuwar Karen ya Kamata ace Sajeeda ta gane wani Abu amma ta kasa ganewa. Har bakin gate Sajeeda ta rakata sai tayi kamar zata mata magana sai ta kasa har Sajeeda ta maida k'ofar gate din ta rufe. Banda bata san ta dagawa Sajeeda hankali ba abinda zai dawo da ita gidan kabiru ba abinda ya faranta Mata sama da karen da ta kashe dan tasan ta wargaza komai a yanzu Kuma addua zata dage ba dare ba rana. Kafin ta samu abun Hawa ta tsaya a hanya ta siyi alewa duk yaron da tagani sai ta bashi. Sajeeda Har karfe goma na dare Abban Nusrah bai dawo ba zuwa yanzu sai naji hankalina ya tashi na kasa gane Mai yake damun Abban Nusrah hakika uban yayana ya canza akwai wani boyayyen al amari,tunda Yesmeen ta tafi na fara mazartar maganganun ta sai naga kamar akwai abinda take b'oyemin haka kawai bazata ce na ringa addua ba,yadda Abban Nusrah ya nuna tashin hankalin sa akan Kare har yanzu kaina a daure yake. Haka tunani ya cike min zuciya na rasa tunanin ma da ya kamata nayi. Abban Nusrah bai dawo gidan ba sai wajen Sha biyu na dare na dauka zai dawo fuskarsa a hade sai naga fuskarsa a sake ya dawo. Bai nuna wani abu ba Kamar ma wani Abu bai faru ba har na bashi abincin sa ya fara ci Yana fada min dalilin daya sa bai dawo da wuri ba Kaya ya Kai wani kauye, Ni kuwa ganin sam bai nuna wani abu ba yasa na fara magana cikin kwantar da murya Ina "Abban Nusrah dan Allah kayi hakuri da abinda Yesmeen ta maka na hadaka da girman Allah" "Haba haba ba komai fa ni har na manta ma dan dama abokin nawa nake ji Koda naje wajen sa na fada Masa abinda ya faru bai wani nuna bacin ransa ba shi ya sa na sauko dama shi nake ji ya bani aron Kare na kashe masa,Amma a yanzu na sake gano wani goben nan Zan d'auko bai Kai Wanda ya mutu girma ba muna bukatar Kare a gidanan"

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});