Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 79

Chapter 79

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,249 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shafa kowane shafi,sai naji kamar Ina gani" Gyada Kai Yaya Abu tayi tana ba shakka toh ga abincin ki nan sai kici" "Nagode mama" Yaya Abu wani irin kallo ta zuba mata kafin tayi hanyar waje,ta bar k'ofar d'akin Yesmeen din a bud'e tana ayyana irin dukan da za tayiwa Yesmeen idan ta gano tana gani kitchen ta koma ta d'auko ragowar maganin da ta zubawa Sajeeda ta fito ta koma d'akin Yesmeen cikin sand'a ta zubawa Yesmeen ido da idonta ke kallon sama har lokacin tana zaune a yadda ta barta abincin ta na nan a gabanta,sai shafa littafin addu'oi take tana miis mis da baki. A hankali ta tsugunna a gaban Yesmeen ta barbada maganin a cikin abincin,tana cigaba da kallon Yesmeen idan har Yesmeen tak'i cin abincin nan tasan tana gani idan kuwa taci tasan dagaske bata gani,dan ko kad'an bata yi motsin da Yesmeen zata san ta shigo ba ta koma gefe daya tana kallon yesmeen da har lokacin take ta shafa littafin,Yaya Abu kuwa tuni ta fara tunanin karya Yesmeen take tana gani,tayi gyaran murya tana "Kici abincin ki Mana sai ya hucce" Yesmeen duk abinda Yaya Abu take yi tana kallonta da ace Yaya Abu zata Mata kallon tsaf zata ga yadda jikinta ke balain rawa har tana hada gumi,da dukan alamu Yaya Abu so take ta kasheta itama dan tana kallon sama ne kawai amma tana kallon sadda ta zuba mata abu a cikin abinci,da kulle k'ofar d'akinta take Yi,Yaya Abu ya kafa Mata dokan ta daina kullewa dan ta tsani tazo ta ringa kwankwasawa, ta riga tasan Yaya Abu so take ta gano ko tana gani ko bata gani,a yanzu indai tak'i cin abincin nan zata gano tana gani,karshen ta idan Kabiru ya dawo aka fada Masa tana gani,a yau ya aikata lahira ba Mai iya kwaceta dan itama Yaya Abu ba karamin tsanarta tayi ba,da hankalin ta ba yadda zata ci abinda zai cutar da ita,a yau dai asirinta zai tonu dan bazata ci abincin ba, zata nunawa Yaya Abu tana gani,maganar Yaya Abu ya katse mata tunanin da take da tace taci abincin Mana Kar ya sallamce,duk Shirin da take yi na su gudu da Sajeeda idan har Yaya Abu ta tafi wajen Yesmeen gobe ya tashi a banza tsawan da ta daka Mata da "Kici abincn nan nace kuut a lailai yarinya nan ta dauka dunkulallen kai ne dani, har na shigo d'akin nan naganki da littafi kice min bakya gani,ci abincin nan nace" Yesmeen so take ta saukar da kanta ta kalli Yaya Abu tace tana gani,ta fada Mata dalilin da yasa tayi karyar makanta,indai da zuciya a kirjinta ai dole ta tausayawa Sajeeda da ita kanta,sai dai a madadin ta saukar da kanta sai ta hau lalubar abincin ta d'auko cokalin ta debo abincin duk bisa umarnin zuciyarta dan Yaya Abu na gabanta a tsaye ta kame kugu da alama kiris take jira ta rufeta da duka,tana bude bakinta Yaya Abu ta tunkude hannunta ta d'auke abincin dan tasan indai tana gani tasan bazata tab'a yarda taci ba,tana ficewa Yesmeen ta kifa tayi sujada tana godewa Allah Dan Allah ne ya rufa Mata asiri ya kareta,yanzu ba iya Kabiru ne abin tsoro ba har Yaya Abun bata tab'a tunanin zata tunkuda hannun ta ba ta dauka zata barta taci abincin ba abinda zai zaunar da ita a gidanan da Sajeeda Yaya Abu na tafiya gobe taga Kabiru ma ya fita zata Nemo Mai taimaka Mata su gudu,ta koma ta zauna tana Jin yadda kirjinta ke bugun uku uku,yau dai ta tsallake rijiya da baya. Tana dagowa daga sujada ta koma ta zauna a daidai lokacin da Yaya Abu ta sake dawowa da wani plate din ta dire a gabanta tana "Ga wani abincin kici wancan da na d'auke abu ne ya fada a ciki. Daga haka ta kullo rufo dakin Yesmeen ta koma kitchen ta d'auko abincin Sajeeda,a yanzu ta tabbatar wa kanta da yesmen bata gani,ba yadda zaayi ta kashe Yesmeen,dan bata ga amfanin kau da ita ba za Kuma a gano idan suka tafi lokaci guda da Sajeeda dama gwaji take so tayi ta Kuma ga Yesmeen din ba gani take ba. Sajeeda Hawaye kawai ke zubo min da naga Hamza Wai shi ya kaini bandaki ya gyarani,ya canza zanin gadon da na b'ata ko kyankyamina banga yayi ba ballantana ya toshe hancinsa. A fadar sa ma a d'akina zai kwana dan sunyi hutun makaranta,ina Jin lokacin da Yaya Abu ta kwalla masa Kira ya fita ba jimawa ya dawo da farantin abinci a hannun sa dama tare suke ci da Annur,shinkafa da taliya ne da miya,ya hau tsakiyar gadon ya juya abincin ya kalli Annur Yana yazo suci,haka Hamza ya ringa ci Yana bani a baki, Kamar yasan wani zubin da yunwa nake kwana dan Yaya Abu yanzu ba bani abincin take ba, Yesmeen Kuma ba ta iya zuwa ta bani dan Yaya Abu sai ta Kai Sha biyu a zaune a Palo tana kallo,a haka yayi ta bani har sai da na d'auke kaina ya bani ruwa na sha,yaje gaban mudubi ya kwaso magunguna na da ni nasan ba aikin da suke min amma ba bakin da zan hana a ringa bani,haka na Sha ya maida ledar gaban mudubi ya dawo ya zauna,Annur kuwa suna Gama cin abinci ya ringa buga game a tab din da Abban Nusrah ya siya musu,shi kadai ne banga Abban Nusrah ya siyawa waya ba,wayar Yesmeen ma da ya kwace Ina ganin dan Yasan tasan sirrinsa ne Amma sai cewa yayi wayar bata da amfani a wajenta tunda ba gani take ba,Hamza Kuma ya d'auko wayarsa ya ringa daddanawa,duk da ido nake bin su iya su da nake gani wallahi Dadi nake ji a raina,haka nake kwana ni daya Kamar mayya ba Mai kula dani,dama su barmin su su ringa kwana a d'akina nasan ko Yaya nayi gurnani Hamza zai tashi kila ya gane Ina bukatar wani abun ne,Yesmeen ma Yaya Abu ce ta koreta a ranar da ta shigo d'akin da dafa bango akan zata na kwana dani, Yaya Abu ta koreta akan me zata kwana ita da ba gani take ba ba Kuma wani abu za ta iya min ba. Shigowar Yaya Abu ya katse min tunanin da nake na juya Ina kallonta,tana ganin su Annur ta hade rai tana "Uban me kuke nema a d'akin nan"? "Ba komai dama munzo mu zauna da umma ne saboda ita kadai ce yau ma anan zamu kwana dan umma na bukatar kulawa tunda ba mai kulawa da ita daddare" "Toh wanan ne baku Isa ba,bazaku kwana anan din ba,kaji min yaro da iyayi waye yace maka baa kulawa da ita maza maza tashi ku tafi dakinku zan bata abinci" "Ai taci abincin tare muka ci abincin da ita dan Allah mama ki barmu mu kwana Yaya Saifullahi ma dazu da muka yi waya dashi cewa yayi mu ringa kwana da ita" "Toh bazaka kwana ba nace so kake kace bana iya kula da ita har wani waya ake bugo ma ace ka kula da ita dalla tashi ku ficemin daga d'aki" Annur da sauri ya dauki tab dinsa yayi waje,Hamza kuwa baa San ransa ba ya mik'e Yana

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});