Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 103

Chapter 103

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suka fita Suka barta,ihuu kawai take tana "Baba kana Ina Gwaggo ku yafe min tun baaje koina ba na fara ganin ba daidai ba,Kabiru na tuba ka bar kudin dan girman Allah ka maidani titi,wallahi ba Wanda Zan fadawa karka min haka Kabiru? Shigowar shugaba da bakakken Kaya da wani Kare daya dallaro harshensa waje yasa ta saki ihu taje ta manne da bango, Kabiru kuwa dake bakin kofa ya fara magana Yana "Mai gida burina sirrina ya rufu a rufewa kowa baki" Shugaba murmushi ya saki Yana "zaka iya tafiya ka dau hanya goben nan karka wuce gobe karfe daya zamu yi amfani da jinin ko ka isa can ba mai iya maka magana " Ihu Yaya Abu ta saka tana "ku rufa min asiri da jinina zaku yi amfani innalillahi wa Inna ilaihi rajiun kuyi min rai karku kasheni, Kabiru nice fa Abu yayar Sajeeda Mai na maka da kazo ka bada jinina mai yasa baka bada na Sajeeda ba" Kabiru ko kallonta baiyi ba yayi waje shugaba ya fita ya rufe k'ofar Ta tafi da gudu tana bubuga k'ofar kuka kawai take kamar ranta zai fita "kaicona na cuci kaina a garin san kudi,na jawowa kaina mutuwa wane kaddarar ne ya kaini gidan Kabiru shikenan yanzu mutuwa zanyi" Kuka kawai take tana hararo yadda zasu yankata. Kabiru Ko kad'an baiji komai ba har ya baro kungiyar dan yasan ba mai tab'a zargin Wai shi ya d'auke Abu,haka kawai yaji yayi mugun tsanarta,ko shi aka bawa wukar zai iya kasheta,babban burinsa a yanzu ya samu Yesmeen ko da a gaban mutane ne wallahi sai ya rabata da ranta,a rayuwarsa bashida babbar makiya sama da Yesmeen duk wanan masifar ita ta jawo.masa. Koda ya koma gida haka ya zauna yayi zuru Yana tunanin Rabiuu har ga Allah so yake ya bar kungiyar ya gaji yayi nadama,har tsawon wane lokaci zai dauka Yana aikata abubuwa dan asirinsa ya rufu da Yama riga da ya tonu,yanzu gobe idan mahaifiyarsa ta Kama shi fa Mai zai ce Mata. Idan yaje gobe Yan uwa Sajeeda suka gan shi fa Yadda yaga rana haka.yaga dare bai runtsa ba. Karfe bakwai na safe ya dau hanyar garinsu da Kare a Bayan mota baisan ma mai zai cewa mahaifiyar sa akan Karen ba. Zuciyarsa cike take da zullumi. Tafiyar awani ya karaso dashi har k'ofar gidan mahaifiyar sa da ta koma sabon gidan da ya Gina mata. Da Karen ya shiga cikin gidan Gabansa na dukan uku uku,a tsakar gidan ya samu mahaifiyar sa a tsaye wasu almajirai a tsugunne a gabanta,tana ganinsa ta saki baki tana kallonsa da Karen da yake ja da daya hannunsa tama kasa amsa sallamar da yayi Mata. "Wanan Karen fa Kabiru daga Ina haka ka taho da kare" Mahaifiyar sa tace a daidai lokacin da ya Isa gabanta ya tsugunna Yana gaisheta Bata amsa ba ta Kara jefa Masa tambayar "Wanan karen fa Kabiru kasan ko kad'an bana San Kare Mai ya hadaka da kare Kai ba mafarauci ba" "Hajiya akan hanyar tahowa nan na siya wallahi barayi ne suka addabeni shi yasa idan na kaita gida barayi zasuji tsoron shigowa. "Tun kana Abujan baka tsaya ka siyi Karen ka Kai gida ba sai da ka d'auko hanya zaka siya" Kabiru Kai ya hau sosawa ya dauki Karen yayi bayan gidan Yana "yunwa nake ji hajiya akwai abinci. Yana zuwa ya daure Karen ta wuyansa Ya koma ciki,Yana shiga yaga mahaifiyar sa ta kwanta kamar Mara lafiya Cikin mamaki yace "Hajiya lafiya kuwa na ganki haka"? "Wallahi Yanzu nan naji kaina ya sara min zazzabi ya rufeni ji nake wuyana a shashake ma" "Sannu hajiya Allah ya sauwake ya baki lafiya kina da pcm na dauko miki ki Sha"? Eee akwai a gaban mudubi d'auko min,sai ka Shiga kitchen akwai abinci a flask. Kabiru dakinta ya Shiga ya d'auko Mata pcm din da ruwa ya kawota dak'yar ta karba ta Sha tana rik'e wuyanta. Kabiru ya shiga kitchen ya debo abinci ya dawo palon ya zauna ya fara cin abincin ganin tana ta wash wash yasa yace "Hajiya ko dai asibiti Zan Kai ki"? Girgiza Masa Kai tayi idonta a rufe,a haka ya zuba mata ido Yana jera mata sannu. Ba jimawa yaga bacci yayi awon gaba da ita. Sai yaji inama a yanzu zai iya zagayawa baya ya nemi karyar tunda bacci ya d'auke ta,amma ba wanan damar saboda sai karfe daya na dare aka ce ya kwanta da Karen,kila yanzu ma ya gama da jinin Yaya Abu ya tabe baki Yana kwadayin ta ne ya jawo Mata. Bacci bacci yaji ya fara ji shi ma hakane yasa ya tashi ya Shiga daya d'akin da ya zama d'akin Baki. Yana kwanciya bacci yayi awon gaba da dashi. Mafarki A kwancen da yake yaji an turo k'ofar hakane yasa ya bude idonsa a hankali yaga mahaifiyar sa ta shigo da igiya a daure a wuyanta cikin b'acin rai ta fara magana tana "Kabiru mai nayi maka kake so ka kasheni saboda me zaka daureni, Kabiru ka kunceni Kabiru ka kunceni Kabiru ka kunceni" A firgice ya tashi ya hau kalle kalle sai da ya dau tsawon mintuna ya gane mafarki yake,mik'ewa yayi da sauri yayi waje dan sai yake ganin kamar ba mafarki yake ba a gaske ne mahaifiyar sa ta shigo. A kwance take har lokacin akan dogon kujera,ido ya zuba mata yana tuno mafarkin da yayi da ita Mai ke Shirin faruwa ne Mai yasa zaiyi mafarki da mahaifiyar sa tana a kunceta A hankali ya fita waje,ya zagaya bayan gida Inda ya daure Karen Yana zuwa yaga Karen a kwance Kamar yadda mahaifiyar sa ke kwance,gabansa yanke wa yayi ya Fadi ya hau tuna Sajeeda da yadda yayi amfani da Kare a madadinta. Cikin faduwar gaba ya karasa wajen Karen Yana zuwa ya tsugunna a gaban Karen ya kunce daurin wuyansa. Ya mik'e ya koma ciki ga mamakinsa Yana komawa ciki yaga mahaifiyar sa ta mike tana tattaba wuyanta tana ganin shi ta fara magana tana "Kasan ji nayi Kamar an shake min wuya mai ke Shirin faruwa dani ne"? Kabiru da jikinsa ya dauki rawa kasa ce Mata komai yayi mahaifiyar sa kuwa ta mik'e tana kila iska ne bata ga ta zama ba bari ta d'auko Qur'anin ta daga haka tayi d'akinta. Kabiru yayi waje da balain sauri hankalinsa a balain tashe sai a yanzu ya gano shugaba so yayi ya cuce shi ya yaudare shi ya nemi mahaifiyar sa, taya zai cutar da mahaifiyarsa?taya zai nemi mahaifiyar sa jikinsa rawa kawai yake ya d'auko wayarsa a daidai lokacin da Kiran shugaban ya shigo wayarsa. Rai a balain bace ya daga wayar Yana k'ok'arin magana shugaban yace "Matar da ka kawo jiya ta gudu,bansan ya akayi ta tsere ba dan haka ka kawo mana wani Jinin" "Bazan kawo ba ka kasheni kawai dan Nagaji da wanan masifa ba abinda kasani,tunda har ka bari Abu ta tsere nasan asirina ya gama tonuwa,har ni zaka yaudara kace na kwanta Da mahaifiyata a siffar Kare,Allah ya tona maka asiri wallahi wallahi bazan kwanta da Karen ba na gaji ba abinda zaka iya yi na bar kungiyar na daina yi kayi duk abinda zaka yi" "Nan da awa ashrin

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});