Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 72

Chapter 72

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,233 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zan iya magana sai dai duk a banza na kasa magana,bazan so mahaifiyata tazo ta tafi batare da na fada mata halin da nake ciki ba,bansan taya Zan sanar da Yesmeen ta fadawa Gwaggo halin da muke ciki ba,da zan samu da Yesmeen ta nunawa Gwaggo tana gani,da zan samu da Yesmeen ta fadawa Gwaggo duk abinda ke faruwa,nasan ko ban iya magana ba Gwaggo tafiya zata yi dani, suna shigowa na fara hawaye ganin babba yalwa a bayanta yasa naji wani irin farinciki,ba damar magana bansan yadda zan nuna musu jin dadin ganin su ba,sai na fara buga kaina da bango Ina gurnani hawaye na zubo min. Gwaggo ta saki hannun Yesmeen dan har da ita suka shigo ta iso wajena da sauri ta rikeni,tana "Sajeeda zaki jiwa kanki ciwo ki bari wani abu kike so a yi Miki?wajen ma da kike kwance a jike yake" Ni kuwa kallon yesmeen da kanta ke sama kawai nake Ina gurnani,Wanda ni magana nake akan ta fadawa Gwaggo abinda ke faruwa,duk gurnanin da nake Yesmeen Taki sauko da kanta,mai yasa Yesmeen itama zata min haka,Yaya Abu dai bata d'akin ballantana nace shi yasa taki nuna musu tana gani,haka nayita hawaye da Ina iya motsa hannuna ne ma da sai na nuno Yesmeen din kila Gwaggo ta gano magana nake so da ita. Babba yalwa sallati kawai take a lokacin da tayi tozali dani, tama kasa karrasawa wajen da nake kwance sai cewa take "Hauwa dama haka Sajeedan ta dawo innalillahi wa Inna ilaihi rajiun wane irin cuta ne wanan taya zaa barta a gida baa je an nema Mata maganin gargajiya ba?ai bana Jin wanan larurar tata ta asibiti ce?yanzu kenan ko tashi bata iya yi sai dai tayi Kashi ko fitsari a kwance"? "Haka ta dawo babba shi yasa na kasa samun kwanciyar hankali wanan ruwan da kike gani daga gabanta yake fitowa mai wari ba fitsari tayi a kwance ba ban taba ganin larura irin na Sajeeda ba shi yasa nacewa mijinta ya bari mu gwada maganin gargajiya yak'i" Ido babba yalwa ta zaro sai a lokacin ta matso kusa da wajen da nake kwance tana "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun yanzu a jikin Sajeeda warin nan ke fitowa? Hauwa har kika barta tun lokacin da kika zo baki tafi da ita ba Aikuwa dole mu tafi da ita aje a jarraba maganin hausa bana Jin ma larurarta na asibiti ne," Abinda nagani kenan mijinta ya hana "Aikuwa dole ya bari mu tafi da ita sannu Sajeeda Allah ya tashi kafadunki ya baki lafiya" Murmushi kawai nake Ina godewa Allah a zuciyata da ya aikomin da su a daidai lokacin da rayuwata take cikin hatsari yayata take Neman rabani da numfashina" "Ina shi kabirun yake ne dan gwara yazo indai ya bamu izini a yanzu zamu juya mu tafi" Cewar Gwaggo babba yalwa na k'ok'arin magana Yaya Abu ta shigo d'akin da farantin abinci,so nake kawai su Gwaggo su gane so take ta kasheni,hakane yasa na fara gurnani Ina buga kaina da bango Gwaggo ta rikeni tana "Sajeeda ai sai ki jiwa kanki ciwo wani Abu kike so"? Gurnani na cigaba da yi Yaya Abu ta ajiye farantin abinci tana "haka take yi idan taga abinci ko tana san wani abun ku muje daga d'akina ku ci abincin kafin ku gama na gama bata abinci na kintsa ta" Ina Jin Mai tace na fara buga kaina Ina gurnani nasan so take su Gwaggo su bata waje ta kasheni,sai Gwaggo ta girgiza kanta ta hau share hawayen da take ta hanasu zubowa saboda tausayina tana "Bazan iya cin komai ba sai dai ki Kai babba taci abincin ki kawo abincin na bawa Sajeedan" "Kuje kuci abincin nan Gwaggo rashin cin abinci zai saka Sajeeda ta samu lafiya ne ku tafi daki kafin mijinta ya sauko bai dace ma ya sauko yazo ya sameku anan ba,haba Gwaggo" Gwaggo na k'ok'arin magana babba yalwa ta daga Mata hannu tana "Muje daga d'akin kafin mijin nata ya sauko" Babba yalwa tayi hanyar waje Gwaggo ta bita a baya duk da gurnani da nake dan Kar su fita su barni da ita. Suna fita ta kalli Yesmeen dake tsaye tana "uwarki kika tsaya yi bazaki fita ki bani waje ba shegiya ai wallahi sai su Gwaggo sun tafi dake" Yesmeen lalubar hanyar tayi tafita waje dan tasan Sajeeda bazata tab'a yarda taci abincin hannun Yaya Abu ba,ba karamin dadi taji da ganin su Gwaggo fadar Kuma zasu tafi da Sajeeda ya mutukar faranta mata,dan da haka zasu samu su gudu,dan itama bin su zata yi Wanan karyar makantar ma ya dameta,ta fara gajiya makarantar da bata zuwa duk yafi daga mata hankali. Sajeeda Duk yadda Yaya Abu taso na Sha shayin k'in Sha nayi,dankalin ma naki ci,dan nasan idonta ya rufe da san ta kasheni,ganin su Gwaggo bazai saka ta fasa ba. Tsaki tayi ta dire kofin shayin ta hau masifa akan Kar na Sha din kwana biyu bata San iskanci da na tsiro dashi ba, haka ta jani a kasa ta kaini bandaki ta kwakwara min ruwan sanyi tunda na fara larurar nan ko Yaya ruwan sanyi ya taba jikina haka Zan ta Jin kaikaiyi Ina gurnani dan ba hannun da zan sosa jikina Kamar zan zauce haka nake ji dan ko bacci bana yi Kuma Yaya Abu tasan da haka,amma haka ta kwara min ruwan sanyi ta kwara min a gabana ta cire zanin gadon ta shimfida wani kayana ma duk sun min yawa haka ta d'auko wani doguwar Riga ta saka min,sai yatsuna fuska take tana magana kasa kasa dan duk abinan da take yi saboda su Gwaggo ne ni kuwa kuka kawai nake Ina cije lebbena dan wani irin azababen kaikaiyi nake ji a ko'ina na jikina gashi ba damar susa. Tana gama fesa Air freshner tayi waje. Tana fita da minti goma na fara Jin maganar ita da Abban Nusrah a palo bayan ta gaishe shi ta sanar Masa da zuwan su Gwaggo Sai naji yace "Su Gwaggo Kuma da sassafen nan" "Eee wai Sajeeda suka zo dubawa Gwaggo duk tabi ta dagawa kanta hankali' "Jiya fa munyi waya da ita nace mata kar ta damu dan yanzu ma na gano wani likita da yace min akwai wani acan kasar waje idan har aka kaita zaa samu magani a wajen sa,yanzu Shirin da nayi na zuwa wajen likitar ne ai da Gwaggo ta daina dagawa kanta hankali' bari na duba Sajeeda sai na je mu gaisa da Gwaggon" Turo k'ofar d'akina yayi na zuba Masa ido,kudin haram ya zauna wa Abban Nusrah yayi wani irin kib'a Kamar bashi ba, murmushi ya sakar min ya zauna a gefen gadon yana "Sannu Sajeeda ya jikin naki"? Kiga Gwaggo da Dora wa kanta wahala da sassafe nan tazo nafa ce mata Kar ta damu Zaki samu sauki dan an samo likitan da ya San Kan larurarki kasar waje zan Kai ki,kinsan Sajeeda ba abinda bazan miki dan na faranta Miki Rai ba,bari naje wajen su Gwaggo mu gaisa sai na dawo akwai maganar da zan miki" Daga haka ya mik'e yayi waje na bishi da ido Ina mamakin halinsa duk abinan fa ya d'auka bansan komai ba rashin maganar nan nawa na matukar

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});