Chapter 108
Chapter 108
ma ta haifi yarinya,haka ta figeta ba ko tausayi,ta ajiyeta a bandakin ta debo ruwa ta hau watsa mata daga nesa tana toshe hanci,tuni taji wani irin radadi da azabar kaikaiyi ta fara girgiza Kai tana tuno yadda itama ta tab'a figar Sajeeda tayi mata yadda yar budurwar yarinya nan ta Mata,lailai ta yarda sharri dan aikene,Sajeeda bata da hakkinta gashi tun a gidan duniya an samu mai rama Mata,ta hau gurnani tana "Sajeeda ki yafemin na samu sauki a rayuwata nayi nadamar Abubuwan da na Miki,baba ka yafemin Gwaggo kimin addua kaicona" Kuka kawai take Yar budurwa na daka mata tsawa tana cudata da tsintsiya daga nesa,dan bazata iya ma matsowa kusa da ita ba. Koda ta gama wani wajen ta maida ta,ta dauko wani.kaya ta zura mata, duk rai a hade take.masifar babanta ya jawo musu balai ya rasa wa zai kawo gida sai Mai larura,abincin ma a wulakance ta bata tana tura mata cokalin bakinta Kamar zatayi amai,tana gama bata ta bar d'akin a fusace tana bazata yarda ta kwana ba indai kuwa babanta bai maidata ba a yau wallahi guba zata saka mata taci ta mutu. Wani irin tsoron Allah ne ya shigeta,da taji abinda yarinyar tace,duk wani mugunta da tayiwa Sajeeda yau gashi Yar cikinta na Mata har tana kirarin zata kasheta,Ashe duk abinda take Allah Yana kallonta lokaci ya bata ta gama duk abinda za tayi,Allah kadai yasan irin kararta da Sajeeda ta kaiwa Allah da har ta fara ganin irin wanan sakayya. Kuka kawai take dan har ta sake Bata kayanta wari ya dume d'akin. Har ga Allah da ace tasan idan ta mutu Aljanna zata tafi da ta roki Allah akan ya dauki ranta da wanan rayuwar kwanci tayar din,ashe baka yiwa bawa gori da halin da ya Shiga ciki,idan har kayiwa bawa gori da jarrabtar da Allah ya Masa,zaka iya wayar gari kaima a jarrabce ka kamar yadda itama kwadayinta ya kaita ga Shiga halin Sajeedan,kafin ta mutu tana bukatar Neman yafiyar Sajeeda da Iyayenta,kafin ta mutu tana bukatar ta nemi yafiyar Yesmeen, Yesmeen da bata Mata komai ba ta Dora Mata Karan tsana. Tana daki ta ringa jiyo muryar dattijuwar na yiwa wani Wanda take kyautata zaton shi ne maigidan akan ayau take so a fitar da ita daga gidan tunda ta farka, yadda taji muryarsa na rawa yasa ta tuna nata mijin da take juyawa da tana tunanin har da bakin cikinta ya Kashe shi. Ido ta zubawa k'ofar a lokacin da ta ji sun nufo d'akin mutumin na zuwa ya rike hannunta matarsa ta Taya shi Suka yi waje da ita. Suna zuwa k'ofar gidan matar ta saketa tana "Yayi maza ya kaita bakin titi" Ta rufo k'ofar. Mutumin da alama.yana tausayin ta. Haka ya nade rigarss duk da warin da take haka ya kinkimeta dan tuni ta dawo sirriya Kamar Mai cutar kanjamau. Da alama gidan nasa a wajen gari yake dan sai da suka yi tafiya Mai nisa Yana yi yana ajiyeta yana sosa hanci da wari ya saka ya ringa haka,karar motocin da take ji yasa ta gane sun kusa titi. Hawaye ne ya hau zubo mata dan idan ya ajiyeta bata san waye zai taimaka mata ba,Yana kuwa zuwa bakin titi ya ajiyeta yana "da ace kina iya magana da kin fadamin wani naki na neme shi na Kai ki,a yashe na tsince ki a daji da naje saro itace,nan wajen gari kike hanyar barin garin Abuja bansan Mai ya kawo ki Nan ba,har ga Allah naso na taimaka miki,amma naga hakan na Neman haddasa min matsala da mai d'akina Allah ya baki lafiya ya kawo Mai taimaka miki" Girgiza Kai Yaya Abu ta hau tana gurnanin Kar ya tafi ya barta ta taimaka Mata. Sai dai tana ji tana gani ya juya ya fara tafiya haka ta kwanta a titi tana sharbar kuka,ta dauka zata ma iya daga hannunta sai dai ta kasa,haka ta kwanta a kasan tana Kiran sunayen Allah dan yanzu bata da mataimaki sai Allah. Sajeeda Tunda muka dawo garin kano muka dan samu nutsuwa, Saifullahi shi ya ringa Kai kawo,bansan yadda yayi ya d'auko mahaifinsa a Kai shi asibitin mahaukata ba,sai da ya dawo yake fadamin,hawaye cike a idonsa ya hau rokona akan na yafewa Babansu iya halin nan da yake ciki kawai ya isa yasa a yafe masa dan tun a gidan duniya Allah ya ke hisabi,wani zai iya dadewa Yana sabawa Allah bai samu ya tuba ba har Allah ya dau ransa kamar yadda Allah ya dauki ran Rabiu a lokacin da bai tab'a tunanin ba,Wanda sai da ya mutu wasu da yawa Suka san halin da ya jefa kansa da arzikin sa ya fara konewa, Wanda ya na da tabbacin shi ne ya jawo mahaifunsu ya Shiga wanan kungiya,kila Allah Yana san mahaifin su da rahama shi yasa ya tona Masa asiri a gidan duniya kowa yasan halin da jefa kansa a ciki,na tuna baya da ba haka yake ba, mahaifunsu nagartacen mutum ne,haduwa da mugun aboki da San zuciya ya Kai shi ya baro" Hawaye kawai ke zubo min dan duk maganar da yayi ba karya tun kafin ma ya rokeni akan na yafewa Kabiru na yafe Masa dan Allah Yana San masu yafiya,nima zanso ya yafemin kura kuraina,ko iya warkar dani da yayi a lokacin da na fid da rai da rayuwa na fara kawowa kaina mutuwa Allah ya mikar dani, cikin ikonsa ya nuna min tsafi karya ne,raina a hannunsa yake ba a hannun kowa ba shi yake azurta Wanda yaso ya Kuma talauta Wanda ya so Allah shi buwayi ne gaggara misali,yayi min niimar da zan dawwama ina gode masa dan bana Jin ko duk kudin duniya zaa hada dan a nema min magani zan iya samun sauki,cikin ikonsa ba tare da an sha wahalar komai ba ya warkar dani,iya wanan kawai ya Isa yasa na yafewa Kabiru da Yaya Abu da naji kwana biyu ta tsaya min arai,bansan inda take ba dan bata je gida ba Nasan duk Inda take tana nan tana Shan wahala har ga Allah balain tausayinta nake ji,dan ko makiyina bana Masa fata ya Shiga halin da na Shiga balle jinina da muke uwa daya uba daya,cikin sheshekar kuka nacewa Saifullahi na yafewa Kabiru duniya da lahira yamin godiya ya kalli kanensa ya musu nasiha yace su ringa yiwa abbansu Addu'a,yayi wa Yesmeen godiya irin daiwaniyar da tayi dani. Ya maida kallonsa Kan Nusrah da ke rik'e da jaririyarta tabi ta rame Kamar ba ita ba,ya Kira sunanta ya fara magana Yana "Bawa bai Isa ya tsallaka kaddarar sa ba Nusrah hakuri zakiyi haka Allah ya kaddara Mana,banso na cigaba da miki b'oye b'oye mijinki ya aiko Miki da takardar ki saki biyu ya Miki yace bazai iya cigaba da zama dake ba idan kinyi yaye zai zo ya dauki yarsa" Jarumtaka na aro na yafa na hau sallati a zuciyata,abinda nake ta gudu kenan amma ba yadda zamuyi Na daure na fara magana Ina "Nusrah kice alhamdulillah" Nusrah take tabi umarnina tayi hamdala Banga alamar tashin hankali a tare da ita ba cikin kwantar da murya na fara magana Ina "Aure rai ne dashi Nusrah Allah yayi aurenki dashi ya Kare Koda ba ta silar mahaifin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111