Chapter 70
Chapter 70
Fado Mata yasa ta fito daga kitchen din ta shige d'akin Sajeeda,bata Jin zata iya cigaba da karyar makantar nan, dan idan har batayi Wasa ba Yaya Abu na iya cutar da Sajeeda ya zama dole tasan hanyar da zata bi wajen hana yaya Abu samun cikar burinta kasan ranta kuwa mamaki kawai take tana tunanin mai yasa har Yaya Abu ke San kashe Sajeeda Mai tayi Mata haka.? Sajeeda Haka Yaya Abu ta ringa tsinewa Yesmeen tana kwashe taliyar daya zub'e,ni kuwa hamdala kawai nake a raina da Yesmeen tazo ya ceceni,Ina ma Ina da kafar da Zan tashi da na gudu na bar gidanan,Ina ma Yesmeen zata gane ta Kira mahaifiyata a waya ta kawo min agaji tazo ta d'auke ni daga gidanan,idan yau Allah ya kareni, gobe fa idan Yaya Abu ta faki idon yesmeen ta zo ta dura min maganin na sha fa. Rai a bace ta gama kwashe taliyar ta fice waje ko kallona bata Kara yi ba. Hawaye ya hau zubo min da na tuna wai yayata ke san kasheni saboda abin duniya,sallati kawai nake da istigari Ina daga kwancen,wani ikon Allah Kuma sai naji zuciyata tana min sanyi. Ana kiraye kirayen sallah magriba naji sallamar su hamza a palon,dan makarantar boko mai hade da islamiya Abban Nusrah ya saka su,idan suka fita tun safe sai magriba suke dawowa,Ina Jin suna gaida Yaya Abu da bata amsa ba ta hau masifar su koma su cire takalmansu ita bata san rashin tarbiya shegu, ta hau auna musu zagi,sai na cije lebbena,Ina Jin wani irin nauyi a zuciyata,yanzu idan na mutu Yaya Abu haka zatayi ta cin zalin yarana. Uwa daya uba daya fa, shigowar su Annur d'akina yasa na bud'e idona,dan indai suka dawo haka zasu shigo dakina su zauna sosai nake Jin tausayin yarana da basuyi dace da uba nagari ba, muna zaune cikin rufin asiri da sutura ya zabi ya ciyar damu da haram. Hamza duk da yasan bazan iya magana ba sai da ya gaisheni,na lumshe idona na bud'e alamar amsa,Annur kuwa dama ba baki,da Ido kawai ya ringa bina idonsa ya Kada yayi jajjur da alama ransa a bace yake,jakar bayansa ya kunto ya d'auko biro da takarda ya fara rubutu dagani har Hamza kallon sa kawai muke Yana gamawa ya dago min takardar "Umma yaushe Mama zata tafi,umma kullum sai ta rankwasheni ta dokeni" Duk yadda na so danne kukan dake neman kwace min a gabansu sai na kasa sai da na fashe da kukan,bani da bakin bashi Amsa,bani da bambanci da hoto Nima kaina Allah zan kaiwa karar Yaya Abu. Hamza shima ya fara magana muryar sa na rawa "umma bana san wanan rayuwar da muke rayuwar mu a zango ta fimin dadi, umma tunda Abban ya zama Mai kudi kike rashin lafiya Annur ya kurmance aunty Yesmeen ta makance,su Yaya Saifullahi Suka tafi suka barmu mama bana san gidanan,nafi san gidanmu na zango nafison yadda muke ada" Ya karshe hawaye na gudu a fuskarsa shekarar Hamza Sha hudu amma yasan yayi wanan tunanin,Amma jahilar yayata bata tab'a zama tayi tunanin ta Ina Abban Nusrah ya samu kudin sa dare daya ba,sai ta fara tunanin hanyar da zata bi ta kasheni. Ina kuka yarana na sharar kwala sai da Yaya Abu da ta Zama matar gidan ta shigo dakina taci kwalliya cikin doguwar rigar shadda har da su kamshin turare,ashe duk kawaliya nan da take yi saboda Abban Nusrah ne,tsawa ta dakawa su Hamza tana "ku wuce kuje ku cire uniform kun zo Kun sakata a gaba Kuna kuka,kuna nufin baa isa a muku fada ba toh Baku Isa ba wallahi dole na muku fada idan kunyi ba daidai ba" Da gudu suka fice daga d'akin. Sai a lokacin ta juyo tana "Nasan ko an kawo Miki abinci ba ci zakiyi ba sai kiyi ta Abu Kamar wata yarinya ko wa zakiyi wa shagwaba oho" Daga haka ta fice daga dakin. Ni kuwa na fara Jan hasbunallahu wa neemal wakeel dan yanzu bakina bazai yanke wajen addua ba kuka da tunani a yanzu ba nawa bane taimakon Allah nake nema. Ina Jin karar tv nasan itace,Ina daka dai bansan wainar da ake toyawa ba nasan yarana basu isa su fito Palo ba. Wajen Sha daya naji muryar Abban Nusrah a Palo suna magana da Yaya Abu,na kasa kunne na Ina Jin Mai suke cewa,bayan ta Masa sannu da zuwa tace masa "Ina ka tsaya haka tunda zu Ina ta jiran dawowarka"? Dariya naji yasa ya fara magana Yana "Yaya Abu ya zaki tsaya jiran dawowa na ai da kinje kinyi kwanciyar ki" "Ta ina zan kwanta ai bazan samu kwanciyar hankali ba har sai ka dawo yanzu dai ga abincin ka can na Kai ma sama ko kasa zan sauko ma dashi"? "Aa a koshe nake wallahi Ina su Annur sun yi Bacci ne"? "Ee sunyi bacci tundazu" "Allah sarki yau ma ban ga fitarsu ba dan kafin na sauko har sun tafi" "Wai yanzu kana nufin bazaka ci abincin nan da na kwashi awani Ina girkawa ba"? "Yaya Abu wallahi a koshe nake da yake naje gidansu Baraka wacce nake ce Miki zan aura a gidansu naci abinci a satin nan ma nake so na tura gidan su in Sha Allah" Kirjina ji nayi yayi wani irin dokawa da k'arfi da naji abinda yace wa Yaya abu da naji tana ta maimaita "yanzu auren dai zaka yi Kabiru" "Toh zan ta zama hakane Yaya Abu kinsan hakan bazai yu ba dole na Kara Aure tunda Kinga Sajeeda ba lafiya ne da ita ba ni so nake ki taimaka min ma wajen shawo hankalin ta gobe da safe zan Gaya mata idan Allah ya kaimu bari na hau sama dan a gajiye nake" Jikina wani irin rawa ya d'auka da naji abinda Abban Nusrah yace wato aure zai Kara tunda ya riga da ya gama dani, a yanzu zai auro wata yazo ya fara sabuwar rayuwa da ita ni Kuma Ina nan na gama Masa amfani,kuka kawai nake Ina Kiran Sunan Allah. A ranar bacci bai ga idona ba haka na kwana Ina kuka da Addu'a ba kishin auren da zaiyi nake ba,cutar da yamin kawai nake wa kuka,har wani sabon zazzabi ne ya rufeni. Akan idona aka Kira sallah Asuba Ba iya sallah zan yi ba amma haka na rufe idona na daura niyyar alwala da zuciyata,nayi Sallah raka biyu,Ina daga kwancen ta hanyar ayyana komai a zuciyata kamar dai sallah nake, Ina iddar wa na fara istigifari. Tuni naji zuciyata ta rage nauyi. Karfe bakwai da rabi su Annur Suka shigo Suka gaisheni na musu addua a zuciyata suka tafi. Wajen karfe tara na fara Jin bacci na neman daukata kamar a mafarki naji muryar Gwaggo na kwada sallama a Palo. Tamkar wacce aka yiwa bushara da gidan Aljanna haka naji na zubawa k'ofar dakina ido. Yaya Abu.... Mg's skincare Kunji takennan kunsake jinshi shin yar'uwa nace wai haryanzu baki jaraba products dinsu ba😵💫yar'uwa mace fa yar ado da kwalliyace koda kina dakyau akace kikara da wanka😍sufa kayan mg's basa bleaching duka kayansu 💯 natural ne sannan organic zasu gyara sukuma goge Miki jikine kawai yakara bayya ar da ainihin zallar Madarar kyawun halittar da Allah yayimiki🥰
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111