Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Rufaffen Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ne yayi, idan har ta samu Sajeeda a boye ta sanar da ita,kila ta san yadda zata b'ullo musu su tsira da ran su ba abinda ya daga mata hankali da taji labarin masu yin kudin tsafin nan a karshe sai sun bada jinin su anyi kudi dasu,tana tsoron yayi kudi da wani a cikin yaran sa ko ita ko Sajeeda. A kallon da take yiwa Kabiru yanzu ba abinda ba zai iya yi ba dan ya riga da yayi nisa. Bakin Karen nan daya kawo musu gida jikin ta na bata akwai wani mumunan al amari a tare da Karen dan yadda yake tatala Karen na matukar bata mamaki, da kan sa yake kaiwa Karen abinci yanzu ko fita yayi ya dawo wajen Karen yake fara zuwa ya duba, idan ba karya idon ta ke mata ba akwai wani abu kamar pant da take gani an rataye wa Karen a wuya, idan tana kallon Karen ma sai taga Kamar ba normal kare ba,a yanzu d'akin da ta ga ya lodawa kwado kawai take so ta leka taga mai a cikin d'akin da yake b'oye wa. Haka tayi ta tunane tunane har aka Kira sallah Asuba ta tashi tayi sallah,tasan ba wai zurfin ilimi ko wani sani ne da ita ba amma tana rokon Allah da tawasali da kyawawan sunayen sa da sallatin da take yiwa mafi soyuwa a gare shi ba dare ba rana daya haska mata lamarin Kabiru kada Allah ya bashi ikon cutar da su. Sai da ta shafa ta koma bacci sai tayi sallah take samu tayi bacci Mai nutsuwa. Ko awa bata yi da komawa baccin ba ta fara mafarki Mafarki. Mafarki tayi a kwancen da take Karen dake bayan d'akin ta nata haushi Wanda Haushin da yake yi ne yasa ta bud'e idon ta. Can Kuma ta fara jin ihun Sajeeda Wanda ihun da take yi yasa ta mik'e da sauri ta fice daga d'akin tayi bayan gida. Inda ta tarar da Sajeeda a kwance a kasa Karen ya danne ta suna ta kokawa ita Kuma Sajeeda nata ihu,tana rik'e zanin ta da kamar zanin nata Karen ke san fusgewa da bakin sa. Ganin ta da Sajeeda tayi yasa ta fara mik'o mata hannu akan tazo ta taimaka Mata" Waige waige ta fara yi ta hango katon icce,ta tafi da gudu ta d'auko itacen tayi wajen Karen dan ta kwada wa Karen ya daga Sajeeda sai ta hango Kabiru ya taho wajen ta a guje da wuka yayo kanta kafin ya caka Mata ta farka a gigice tana sallati. Ko da ta farkan sai taga kamar d'akin juya mata yake sai da ta dawo daidai ta gane mafarki take yi,Wanda mafarkin kamar a zahiri,da sauri ta mik'e tayi waje tana fito wa palon ta tarar da Sajeeda a Palo da Kabiru dasu Saifullahi a zaune suna karyawa. Yadda ta Fado palon a firgice yasa Sajeeda mik'ewa tana "Yesmeen lafiyar ki kuwa"? Yesmeen da bata ma san rik'e take da zuciyar ta ba ta saki ajiyar zuciya tana godewa Allah da mafarki take, kallon tsanar da Kabiru ke jefo Mata yasa ta juya da sauri tana "Umma lafiya kalau mafarki nayi mara Dadi" Sajeeda kuwa ta cigaba da bin ta a baya har suka shige d'akin. Yesmeen ta rage tsayinta ta fara gaida Sajeeda da ta zauna a gefen gadon. Sajeeda ta amsa tana Kare Mata kallo dan wajen takwas da taga bata ji motsin ta ba ta yanke yi musu abincin dan tasan kila gajiya yasa Yesmeen din bata tashi ba. "Mafarkin me kika yi haka daya saka Kika fito a firgice"? Yesmeen kuwa da taje bakin windo tana leka Karen da ya dallaro harshen sa waje tana Kara tuna mafarkin da tayi ta juyo a hankali ta kalli Sajeeda taga irin kayan da tayi mafarki da Sajeeda ta saka shine a jikin ta sai taji hankalin ta ya Kara tashi,so take ta gane Mai fassarar mafarkin da tayi kafin ta fadawa Sajeeda wani Abu. Kabiru ya banko kofar da k'arfi Yesmeen a firgice ta ja da baya Sajeeda kanta sai da ta tsorata Kabiru cikin hade rai ya fara magana Yana "Baki ji Ina Kiran ki bane"? "Ban ji ba Abban Nusrah" Sajeeda ta mik'e tsaye dan ita yake kallo Yesmeen kuwa ta sada kansa kanta kasa dan a yanzu ba hallitar da take gani ya firgitata sama da Kabiru,bata San ya akayi Sajeeda bata tab'a lura da yadda jikinta ke rawa idan ta gan shi. Sajeeda bayan Kabirun ta bi sai da suka koma Palo suka zauna ya d'auko kudi daga Aljihunsa gudan Dubu Dubu ya fara mik'a mata Yana "Gashi nan a siyo Abubuwan da Babu a gidan" Turus Sajeeda tayi tana kallon kudin,dan a yanzu kudaden da take gani a hannun Kabirun ya fara girmama tunanin ta "Ki karba mana kika tsaya kallona" "Abban Nusrah Dubu dari naga fa kana miko min Abban Nusrah Ina kake samun kudi haka,a kasa da wata uku kayi irin wanan kudin" "Sajeeda idan har bayanin da na Miki na samun kudina bai gamsar da ke ba kisa a ranki sata nakeyi tunda ke dama baki tab'a kyautata min zato ba kullum sai dai ki munana min,Ina ga ai na fada miki duk karshen wata zan ringa d'aukar al bashi miliyan daya toh jiya albashi nayi idan kin ga dama ki yarda idan baki ga dama ba karki yarda wanan matsalar ki ne daga yau karki sake min tambayar daga Ina nake samo kudina ni ba yaron ki bane da Zaki saka ni a gaba kina min tambayoyi kamar danki. ke a rayuwar ki rayuwata ta baya ta kanikanci ne yake burgeki na dauko dari biyu ko dari da hamsin na baki, toh ni da wanan rayuwar da kike min fata har abada arziki da budi yanzu na fara gani,idan Zaki saki jiki ki mori niimar da Allah ya Mana toh,idan bazaki saki jiki ba wanan matsalar ki ce. Daga haka ya mik'e tsaye ya fara kwalawa Yesmeen Kira Da sauri Yesmeen dake daki ta fito har tana tuntube Tana isowa ta zub'e akan gwiwarta kamar dai yadda ta saba cikin girmamawa. Ya d'auko kudin ya mik'a mata Yesmeen hannunta ta hau rawa tana zuba addua a zuciyarta dan yanzu duk abinda zai fito daga hannun Kabiru tasan ba na halak bane. Daurewa tayi ta karba Kabiru cikin hade rai ya fara magana Yana "Kije kasuwa ki Karo Mana kayan amfanin gida dan Naga alamar babar ki bata san zuwa" "Kamar dame dame zaa siyo"? Kabiru shiru yayi Kamar mai nazari sai can kuma ya karbi kudin Yana "jeki Sako hijabin ki sai muje kasuwar idan na gama Miki siyayyan sai ki kawo kayan gida ni na wuce wajen aiki" Sai a lokacin Sajeeda tayi magana tana "Bance bazan je ba Abban Nusrah ka kawo na siyo kayan" "Bazan bayar ba" "Allah ya baka hakuri tunda kace da kan ka za ka siyo mai zai hana ka tafi da su Saifullahi Yesmeen Ina ga ko karyawa bata yi ba" "Da ita Zan tafi idan zaki hana Kuma sai naji" Sajeeda bata Kara cewa komai ba taja bakin ta tayi shiru. Yesmeen kuwa ta mik'e hankalin ta a tashe tayi cikin d'akin ta tana zuwa ta

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});