Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 99

Chapter 99

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

bakinsa. Duk da ƙyawun da yayi cikin ɗanyar shadda fara tas da ƙiba daya ƙara da haske hakan bai hana iyalan nasa shaida shi ba. A take fara'ar fuskar Inna ta ɓace ɓat sai gabantane ke wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zai buɗe. Cikin rawar murya tace, “Malam?!”. “Na'am Asabe”. Ya amsa kansa tsaye yana kallon cikin ƙwayar idanunta. Baya tai a tsorace zata zube dan ruɗani, a dai-dai sansa du Yaya Gajeje ke haɗa baki ita da Sa'a da Tinene data tashi zaune da ƙyar wajen kiran “Baba!”. Nanma kai tsaye ya amsa musu da “Na'am ƴaƴana”. Ai tuni Sa'a ta kwasa da wani irin gudu tayo kansa batare data saniba. Ta faɗa jikinsa tana fashewa da wani irin kuka maiban tausayi. Hannu biyu yasa wajen riƙe abarsa yana murmushi, ya miƙama Tinene hannu itama. Da sauri tayo kansa duk da halin ciwo da take a ciki itama ta shige jikinsa. Hayaniyarsu tasa Karima fitowa itama. Ganin Babansu yasata kware baki cike da firgici ta kwala ihun daya jawo hankalin maƙwafta suka fara leƙe ta kantaga. Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci gida ya ɗauki harama. dan tuni ashe jama'ar gari sunga baba sanda yake shigowa garin tare da matarsa. A take gida ya ɗauki murna, dan tuni dangin baba su Gwaggo Laritu harsun iso jin labarin dawowar ɗan uwansu. Sai koke-koke akeyi na farin ciki. Da ƙyar aka samu gidan yaɗan natsa aka kawoma Baba da baƙuwarsa ruwa. Babu musu suka amsa suka sha dan sunada buƙatarsa. Baba Rabilu cikin kasa haƙuri yace, “Yaya gaka da baƙuwa kuma bamusan wacece ba?”. Murmushi baba yayi yana mai kallon ƙyaƙyƙyawar matar, zuciyarsa fes da farincikin daya bayyana a saman fuskarsa yace, “Itama yayarku ce. Dan tazama ɗaya daga cikin zuri'armu tunda ta kasance Matata harma da tsohon ciki gashi nan”. Cikin mamaki da nuna bayyanannen farin cikinsu suka shiga sake mata gaisuwar girmamawa. itako cike da fara'a da mutuntawa a garesu take amsawa. Babu wanda ya lura a cikinsu sai jin faɗuwar Inna sukai timmm a ƙasa. Dan hatta da Tinene sai da ta gaida matar da baba ya kira da matarsa. Karima ce kawai ta wani gwalalo idanu tana kallonta. Kusan su duka kan Inna sukayi, banda Baba da ko motsi baiyiba sai dai ya kalli wajen. Ruwa Sa'a ta ɗebo da sauri ta kawo, Gwaggo Laritu dake riƙe da Inna ta amsa ta shafa mata a fuska. A take ta kawo numfashi tana binsu da kallo. idonta ta sauke akan baba da Amaryarsa. Babu zato sukaji ta fashe da kuka kawai ta fara sambatu “Dan girman ALLAH na roƙeku ku taimakeni ku hwaɗa mani gaskiya, kuce dani mahwalki nake ba gaske baneba, na shiga uku ni Asabe. Yanzu malam irin sakayyar da zakaimin kenan akan wahalar ganin ka dawo gida da nakeyi tsahon shekaru? Yanzu malam duk hwaɗi tashin da nake akanka karasa da abinda zaka dawo gareni sai kishiya? Na shiga uku na lalace ni Asabe. Shikenan watan lalacewata ya tsaya kuma sai abinda ALLAH yayi. Ku dubetahwa jama'a kamar aljana. Wlhy tahi Hauwa kyau da ƙuruciya.....” Ta ƙare maganar da ƙara jan wani nannauyan numfashi alamar ta sake suma......... ____________________________★ *_KANO_* Bayan dogon zaman jira dasu AK sukasha sakamakon gwajin DNA ya fito daga likitocin guda uku, Batare da ko su Dr Mahmud sun dubaba aka mikama Baffah. Shima ɗin bai buɗeba ya sake miƙama Dr Mahmud dan yasan amintaccen AK ne. Kuma shina ya yarda dashi ɗari bisa ɗari. Dr Mahmud da duk al'amarin yake neman rikita masa kai ya amsa ya buɗe takardun ɗaya bayan ɗaya zuciyarsa na wani irin harbawa da sauri-sauri. Sai da yayma takardun kallon kusan sakan biyar kafin ya ɗago ya ɗan dubi sashen da AK ke zaune rungume da Little dake barci yanzun. Cikin wani irin rawar murya da firgicin abinda ya gani ya maida kallonsa ga takardun yana magana da rawar harshe. “Ba lallai ku fahinci duka bayanan cikin takardun ba saboda wani abun daga bincike likitocine kawai. sai dai ina mai sanar muku cewar zan faɗi gaskiyar abinda na gani kamar yanda baffa ya bukata tsakanina da ALLAH”. Ya ɗan sharce gumin daya taru masa a goshi da cigaba da faɗin, “B...Baffah sakamakon duka takardun ya nuna ya..ron... Na na na AK ne, dan duk ƙwayoyin halitarsa babu banbanci da yaron kamar yanda ya biyosa a kammani”. Ya ƙare zancen da tsananin raunin harshe dana zuciya. Kusan a tare suma su Baffah zukatansu suka buga. AK dakejin kansa na neman tarwatsewa ya ƙanƙame little a jikinsa yana rumtse idanunsa da matuƙar ƙarfi, har takai yaron ya farka daga barci yana ƙoƙarin fara kuka saboda jin matsar da akai masa. Yanda yayi ɗinne yay matuƙar tada hankalin Dr Mahmud da gaba ɗaya hankalinsa ke akansa. Da sauri ya miƙe zuwa garesa yana ambaton sunnsa. Hakanne ya fargar dasu Baffa ruɗani da ɗimuwar da suka shiga suma duk sukai kansa. Da ƙyar suka iya ɓanɓare little daga jikinsa, Baffah da Abba suka riƙe AK ganin jikinsa na wani irin rawa maiban mamaki da tsoro, cikin ƙanƙanin lokaci kuma duk sai gaɓoɓinsa suka saki alamar ya suma. Wannan shine tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, dan kuwa dai Baffah ji yay tamkar ya fasa ihu dan tashin hankali goma da ashirin, yana matuƙar ƙaunar AK a ransa. Dan yana ɗaya daga cikin ɗa mafi soyuwa a garesa, sai dai yana dannewa ne gudun rarraba kan ƴaƴansa. Da ƙyar suka iya ɗagasa zuwa gadon duba mara lafiya dake a office ɗin Dr Mahmud. Mmn Sadiq kam kuka take sosai dan gaba ɗaya ta gagara fahimtar wannan al'amari maiban ruɗani da al'ajabi........ *_BAYAN WASU AWOYI_* Bayan wasu taƙaitattun awoyi aka samu nasarar farkawar AK da tun ɗazun ya farfaɗo daga sumar da yayi. A hankali ya buɗe rinannun idanunsa ya saukesu akan Baffah dake zaune riƙe da hannunsa. Sai Abba dake ta wajen ƙafafunsa shima a zaune. Mmn sadiq kam ta wuce gida tuni tare da little dan taje ta huta itama gudun kar taje ƙasa. Dan kallo ɗaya zakai mata ga gano tsananin tashin hankali da ruɗaninta. Kallonsu yayi ya maida idanun ya lumshe a hankali yana wani irin murmushi da baida maraba da kukan ƙunar zuciya. Idanunsa a lumshe yace, “Baffah nasan ba lallai ku yarda daniba akan bansan yaya akai na samar da Abdul-Mutallab ba. Domin ni kaina na kasa yarda da kaina balle ku da zan faɗamawa. Sai dai ku sani lallai ina cikin *_MAKAUNIYAR ƘADDARA_* babu wani haske da zai haska min idanun ganinta kuma sai UBANGIJINA da haƙurin fahimtata da zakuyi na ɗan wanu lokaci dazanyi ƙoƙarin ganin bakin zaren, b.........” Saurin katsesa Abba yay ta hanyar faɗin, “Ya isa Adnan. A yanzu halin da kake ciki baya buƙatar duk waɗanan maganganun. Dan Mahmud ya tabbatar mana da jininka yayi ƙololuwar hawa sama. idan kuma ka matsa da yawa za'a iya samun matsala. Mu dukanmu nan musulmai ne, muna kuma iya fahimtar yaran ƙaddara ko jarabawa, suk da dai ita wannan tazo mana a makance. Dan kai da Zinneerah ne ya kamata muji amsar tambayoyinmu a gareku, sai kuma gashi kuma neman amsoshin kukeyi a karan kanku. A ganina mafita ɗaya ce da shawara ta rage mana Alhaji”. Ya faɗa yana duban Baffah. Kai tsaye

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182