Chapter 146
Chapter 146
rufosa. ta Dining ma ya kashe tare da leƙa bedrooms ɗin dake a falon duk yaga akashe sannan ya nufi nacan ciki da take amfani da shi. Akwatin kayanta ya buɗe, duk da shi ba mutum bane mai buƙatar matarsa tasa kayan barci idan zasu kwanta tare ba, yafi buƙatar tazo masa a natural ɗinta, hakan bai hanashi ɗauka mata suba. Sai dai yau ba kamar jiyaba sai da ya zaɓo dai-dai da ra'ayinsa. Gaban Mirror ɗinta yaje nanma ya shiga shinshina turarurrukan wajen kamar mai neman wani daban. Sai dai abin mamaki ya kasa tantance wanda yake buƙatar jin, har takai ya fara buɗe kwalaben khumra dake wajen kusan kala shidda dan bama a kawo mata sauranba tukunna. Ya ɗan samu wasu a ciki, harya ɗauka biyu sai idonsa ya sauka akan kananun ƙwalabe dake cikin wani haɗaɗɗen kwandon saƙa na kaba da aka zubasu ciki kusan kala goma nanma. Murmushi ya danyi dan shi mutum ne mai son ƙamshi, ƙamshi yana ɗaya daga cikin abinda Farah tai galaba a kansa kenan dan itama gwanace wajen baza turare. Nanma shinshinawa ya ringayi ɗaya bayan ɗaya, sai dai ya kasa tantance wanda yafi daɗi da wanda yaji a jikinta. Sai ma neman rikita masa lissafi sukeyi. Nanma biyu ya zaɓa a ciki ya fice bayan ya kashe komai. falukanma duk kashe komai yayi ya rufe sashen baki ɗaya ya nufi nasa. Zinneerah da har ta gaji da jiran dawowarsa ta jingina da makarin kujera tana lumshe idanu ta buɗesu a hankali jin sallamarsa. Bataga mike hannunsaba dan kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa. Zamanta ta gyara da ɗaukar hijjab ɗinta ta riƙe a hannu gudun kar tai laifi. Babu jimawa kuwa sai gashi ya fito, batare da yay mata magana ba ya ɗauka remote ɗin tv ya kashe tare da nufar fridge, yana juyowa ɗauke da fura a hannu tana miƙewa. Fuskarta a marairaice tace, “Yayanmu zanje na kwanta barci nakeji”. Baiyi maganaba sai da ya karaso, ya ajiye roban furan da kamo hannunta ya zaunar. “Zauna kisha wannan sai kije ki kwanta”. Cikin langaɓe kai tace, “ALLAH yayanmu na ƙoshi barci nakeji kawai”. Harar daya zuba mata tasata ɗauka dan harya buɗe mata robar, cokalin dake haɗe da robar furan ta ɗauka ta fara sha a hankali tana lumshe ido dan barci takeji, sosai furan na mata dadi sai dai barci na neman kwafsa mata. Shiko lap-top ɗinsa ya ɗauka yana ƙarasa aikin nasa. “Yayanmu ALLAH ta isheni barci”. Ɗan ɗagowa yay ya kalleta, yaɗan jinjina mata kai kawai yana ajiye lap-top din daya kashe gaba ɗaya. Miƙewa yay hannunsa ɗauke da remote na ac ya kashe. Sannan ya tattara wayoyinsa da nuna mata hanyar ɗakinsa. Sosai ta ɗan waro masa manyan idanunta dake cike da barci waje. Sai dai yanda ya tsuke fuska dole ta haɗiye abinda ke bakinta ta maida kanta ƙasa. Sum-sum ta fara tafiya hanyar ɗakin da bata taɓa shigaba. Kasancewar ya tsaya kashe fitila ta rigasa shiga ɗakin. Da wani ni'imtaccen ƙamshi tafara cin karo, ta ware idanunta sosai tanabin bedroom ɗin da kallo baki sake. Komai yaji masha ALLAH, white and golden kamar kaci dan ɗaukar idon mai kallo. Ga uban sanyin ac. Tana tsaye a wajen harya shigo bata saniba. Sai jitai kawai anyi sama da ita gaba dayanta. Sosai ta firgita sai dai babu damar yin magana. Bai direta ko inaba sai toilet ɗinsa da komai yake a tsare kuma a tsaftace. Dan shi kansa kamshi yake na musamman. “Kiyi alwala”. Ya faɗa kansa tsaye. Sabo da alwalar kwanciya barci yasa bataji komai a rantaba, gashi dama ko shafa'i da wutiri ma bataiba. Alwalar ta ɗaura yana kallonta cike da nazari, da alama yana tabbatar da ingancinta a fannin addinine ne. Sai da ta kammala shima ya ɗaura tasa suka fito tare kamar yanda yay mata alama da ido. Da kansa ya sa musu abin salla. Ganin yayi tsayuwar alamar jansu salla yasata kallonsa da mamaki. “Yayanmu nayi sallar isha'i”. “Nima nayi ai”. Shiru tai bata ƙara maganaba harya tada sallar, itama tayarwar tayi dan bin umarni shine masalaha a gareta. Sunyi salla raka'a biyu suka ɗora da shafa'i da wutiri, sannan ya juyi ya dafa goshinta da ambaton. *اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ* *_Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh._* _Ya ALLAH ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa._ Lumshe idanunta tayi tana sauraren daddaɗan muryarsa mai cike da kamun kai da nutsuwa. Bayan ya kammala ya juya da ɗaga hannayensa sama ya cigaba da kwararo addu'oi kala-kala da harshen larabci. Sai da suka kammala addu'ar ya juyo yana fuskantarta da ƙyau. Tambayoyin ya fara mata a fannoni daban-daban daya shafi addini, wasu ta amsa wasu tace bata saniba dan a yanzu take kan neman ilimi, danma Alhmdllh batai wasaba akan hakan tunda ta dawo da zama kano. Ya gamsu da yanda tayi ɗin, ya kuma karba uzirinta, daga haka ya miƙe yana magana batare daya kalletaba. “Ga kayan barci nan ki canja”. Yana fa ɗaya yana nufi hanyar toilet. Kaɗan ya rage Zinneerah ta saki kuka amma ta dake ranta fal tsoro. Kenan anan zata kwana tare da shi yau ma?. Ta ayyana a ranta. Sanin bata da mafita kuma baya maimaita magana, gashi batason ya fito ya sameta batai abinda yaceba yasata ƙoƙarin canja kayan. Ganin turarrukanta tare da kayan ta mulke jikinta dasu duk da kuwa ƙamshin take dama. Tana gamawa yana fitowa ɗaure da towel jikinsa nata raɓar ruwa. Ƙasa tai saurin yi da kanta tana gyara zaman hijjab ɗinta data ɗora saman kayan barcin. Komai baice mataba ya hau tsane jikinsa da towel ɗin daya ratayo a wuya. Da wannan damar ta wuce toilet ɗin nasa sumi-sumi danyin brush tunda taga sabbi a toilet ɗin, dan ta tuna Hajiya Falmata tace duk rintsi karta kwanta batai brush ba, idan da dama ma ta haɗa da much freshener, sannan ta tabbatar duk sanda zata kwanta barci tayi tsarki da ruwan ɗumi koda ace ta yini amfani da shine. Brush ɗin ta farayi, sannan tai fitsari dayin tsarki da ruwan ɗumi. Much fresheners ɗinsa data gani ajiye a ɗan drawer ɗin glass ɗin toilet ɗin ta ɗauka, dan gasunan kala-kala, banana, cucumber, kai kala-kala ta fannin fruit duk gasu nan. Son da takema S...barry ya sata ɗaukarsa shi da banana ta saka sannan ta fito cikin sanɗa, a ranta tana addu'ar ALLAH yasa ya gama shiryawa dan shiyyasama ta daɗe danta bashi dama. Tsaye ta iskesa gaban mirror sanye da wando 3quarter iya cinya da riga mai buɗaɗen ƙirji farare tas. Yana fesa turare. Ta madubi yake kallonta harya kammala sannan ya juyo...........✍ *_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182