Chapter 129
Chapter 129
nane da juna sallama ya gudo gida. Lokacin daya shigo gidan Farah tayi barci, dan haka shima kayan jikinsa kawai ya zare yay wanka da neman makwanci saƙe-saƙe fal ransa. Musamman fargabar zuwan su Mammah gobe idan ALLAH ya kaimu da Mahma ta sanar masa. Sam bayason Mammah tazo ta tada hankalinta a cikin wannan taron mutanen ƴan biki, shiyyasa tun ɗazun abin ke damunsa da ƙyar yaketa faman tausar kansa. Yau sukai niyyar tahowa Mahma ta sake lallaɓasu akan su zauna zaman shirya abubuwa yanda zasu iya tunkarar Baffah. Dan sunyi aniyar tahowa su shiga garin danya da akace musu amarya take kafin su wuce kano. Hakan yasa Mahma kautar da hankalinsu har amarya ta isa ɗakinta lafiya sannan. Tasan dai idanma sunzo a gobe insha ALLAH aikin gama ya gama kuma. _______________________★ Washe gari aka tashi da shirin gagarumar walima wadda daga ita kuma sai miƙa amarya Zinneerah ɗakin mijinta. Zinneerah data kwana a ɗakin AK ita da Adilah kuwa da zazzaɓi ta tashi, amma tanata daurewa dan har wasu ƴan sauran gyara da suka rage hajiya Falmata tai mata a daren. Tsabar gyaran data sha maranta har wani ciwo yakeyi mata. Haka dai ta cigaba da daurewa har hajiya Iya ta shigo ɗakin domin dubata. Dan Adilah dake fashin salla ma ko tashi a barci batayiba. Sun gaisa da hajiya iya take tattaɓata ganin duk tayi wani iri, “Kai Inno ai zazzaɓi ne a jikin nan naki, haka kika kwana da shi ma ko?”. Cikin ƴar shagwaɓar da suka sabama hajiya iyan ita dasu Jamal ta ɗaga mata kai idanunta na cika da ƙwalla. Sannu hajiya iya ta shiga jera mata, kafin ta taimaka mata shiga bayi dan ta samu tayi wanka. Koda tayo wankan ta samu ta shirya cikin atanfa sabuwa ƙal data amshi jikinta ɗas ta fito a amaryarta, Adilah kanta data farka sai yaba ƙyan datai takeyi, murmushi kawai Zinneerah keyi dan sosai take ganin girman Adilah ɗin kasancewarta ba ƙarama ba, sai dai kawai ALLAH ya bata ƙaramin jiki ga kuma yanayin inda ta tashi rayuwar turai, dan ita hausarma ba iyawa taiba tunda ba zuwa Nigeria ɗin Mammah take bari tayiba. Iya kacinta dasu magana da turanci, saiko AK dake iya jin yaren Mammah na larabci sukanyi, shiyyasa basa shiri da hajiya iya sosai saboda takaicin Adilah ɗin bata iya hausaba. Tea hajiya iya ta kawo mata a sha da magani ta sake kwanciya kafin lokacin walimar. ★★★ A katsina kam ko breakfast ɗin arziƙi basuyi zaman yiba suka kamo hanyar kano, lokacin da suka iso gidan anata kwasar mutane zuwa ƙaton hall ɗin da za'a gudanar da walimar. Yanda anguwar ta rikice da kai kawon motoci masu kwasar mutane yasa dole su Mammah suka fakin tun a waje, Mahma ce kawai ke dauriyar gaisawa da mutane, amma Mammah da Aunty Zakiyya sunata shan ƙamshi. Koda suka iso cikin gidan sun sami Baffah tare da baƙi, yana ko ganinsu yabar baƙin da uncle Ahmad ya nufosu fuskarsa ɗauke da murmushin daya sake fusata Mammah, aiko tayi kicin-kicin da rai tamkar zata fasa ihu. Sai dai batace komaiba bisa ga gargaɗin Mahma da sukasha. Duk yanda Aunty Zakiyya taso nuna halin nata ga Baffah kasawa tai, dan wani irin kwarjini yay mata da cikar kamala. Dole tai ƙasa da kanta tana gaisheshi da girmamawa. Shima cike da fara'a ya amsa mata harda tsokanarta. Yanda Mammah ta ɗauke kanta daga garesa haka shima yayi tamkar bai gantaba, cikin girmamawa yacema Mahma su shiga ciki. Murmushi tai masa, yay gaba suna binsa a baya har sashensa tacan baya da ƙofar falonsa ta ainahin bedroom ɗinsa take. Dan yasan acanne kawai babu wani hayaniyar mutane da hankalinsu zai kai kansu saboda wutar bala'i daya hanga a idanun Mammah. Kafin su shige ya aika Jamal da sukaci karo ya sanarma hajiya iya zuwansu, daga nan ya wuce a haɗo abinci a kawo musu. Mammah zatai magana cikin masifa Mahma ta dakatar da ita da idanu, dole taja bakinta tai shiru tana haɗiyar zuciya. Cikin ƙanƙanin lokaci hajiya iya ta ƙaraso tareda su Bahijja dake ɗauke da abinci, suna ajiyewa suka gaishesu suka fice. Mahma da aunty Zakiyya ne kawai suka gaida hajiya iya, Mammah kuwa sai da Mahma ta harareta sannan ta gaisheta da ƙyar. Hajiya iya bata damuba kam, dan ba yaune farauba. Yanda hajiya iyan ta nuna rashin damuwarta ya ƙara zafar Mammah ta fara magana a ƙufule, “Kabeer miye wannan ke nufi?”. Tai maganar tana ajiye masa invitation card a tsakkiyar centre table. Uncle Ahmad daya shigo falon ne ya ɗauka ya duba ya maida ya ajiye. Kasancewar shima ɗan zafin kan ne a gadarance yace mata “katin gayyatar walimar liyafar cin abincin auren gudan jininmu mana”. Kallonsa tai rai a ɓace tana juya idanu, “Kai kuma bansa da kaiba mijin tace, kaji da taka matsalar kafin ka tsoma baki a ta wasu”. “Hakan na nuna miki cewar wadda ta maidani mijin tace ɗin tafiki komai, tunda ke kin kasa maida Yayana mijin tace ɗin saboda ƙarancin ƙyaƙyƙyawan nazari da kishin hauka dake damunki. In banda abinki Hindatu tayaya kike tunanin raba ƴaƴa da mahaifinsu ta ƙarfin tsiya? Ke waya rabaki da naki har suka bar duniya”. “Wlhy Ahmad ka kiyayeni, kasan na fika zafin kai”. “Anƙi kiyayar taki, kiyi duk abinda zakiyi”. “Zako kaga mizanyi ɗin, dan wlhy wannan auren kun ɗaura banza saina rabashi, in banda son zuciya taya yaro yana zamansa lafiya da matarsa zaku ƙaƙaba masa auren yarinya baƙauya mara galihu.........” A fusace hajiya iya ta katseta da faɗin, “A rashin galihun nata shi ɗan naki ya gani yakeso, tunda har ya iyama yarinya ciki a waje ta haihu ita ƴar son naki bata haifaba. Hindatu ki kiyayeni wlhy, ina ɗaga miki ƙafa saboda ɗanki, amma inaga wannan karon saina fito miki a Amina ta, moddibo ne dai ya dawo gidansu kenan daga shi har ƴar uwarsa babu kuma yanda kika iya. idan buƙatar kasancewa kike dasu kema saiki dawo gidan ubansu ki zauna cikin kishiyoyin da kike gudu. Dan daga yau na yanke shawarar moddibo ya dawo ƙasarnan da zama kenan da iyalansa idan kin gansa a wata ƙasa sai dai yaje harkokinsa ko gaisheki ya dawo wlhy”. Tsabar yanda zuciyar Mammah takai maƙura a hasala sai kawai ta fashe musu da kuka. “Wlhy bazan yardaba, bazan yarda a rabani da ƴaƴana ba tunda nice na haifi abuna bayan wahalar rainon cikinsu dana sha. Ita matar Ahmad data kwace miki shi miyasa kika kasa komai sai ni zakibi ki sama ido akan nawa ƴaƴ.......” “Hindatu!!”. Baffah ya daka mata tsawa jikinsa har rawa yake na ɓacin rai. Murmushi hajiya iya tayi da ɗaga masa hannu. ta duba Mammah da ƙyau tana faɗin, “Itama ba ƙarfina tafi ba, kamar yanda kika ɗauke su moddibo muka barki yanzu kuma lokacin dawowarsu cikinmu yayi, itama lokacin da zan nuna mata nina haifi Ahmad ɗin yayi ai”. “Wlhy ni kuma nayi alƙawarin yin amfani da ƙarfina na uwa wajen raba wannan auren, ɗa kuma da suka haifa a waje zaimin bayanine dalla-dalla dan ubansa”. Ran Mahma da yay matuƙar ɓaci da abinda Mammah keyi bayan sai da ta ƙwaɓeta kafin su taho ta kama hannunta ta maidata ta zaunar a fusace. “Hindatu wai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182