Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

ya ɗarsu a rayukansu, cike da son jin ƙarin bayani Naziru yace, “Zinneerah kekam miya kawoki hanyar jigawa keda ke a jihar katsina?”. Hawayen dake sakko mata ta share tana girgiza kanta. “Nima ban saniba, na samu kaina ne kawai a haka”. Sai yanzu ne Alhaji yay magana. “Lallai da alama kamar bata cikin hayyacintane ta baro gida fa kenan”. “Tabbas hakane Alhaji, kenan har yanzu Asabe bata canjaba ko kuma Zinneerah ma tayi gamo da abokiyar zama irin Asabe a gidan aure.” Maman Halima ta faɗa saboda ganin ciki a jikin Zinneerah duk da kuwa ta saka hijjab. A karon farko shima Khalipha da tun ɗazun baice komaiba sai kallonsu ya sauke numfashi. Gyara tsaiwarsa yayi a jikin bangon daya jingina yana kallon Zinneerah da keta satar kallon maman Sadiq da suke tsananin kamanni. janye idanunsa yay ya maida ga Naziru yana faɗin, “Inaga tunda har an fahimci bakin zaren ayi haƙuri haka har zuwa lokacin da za'a sallameta daga nan ɗin insha ALLAH. Sai dai ya kamata ku sanar mata wacece ita a gareta dan na kula ba fahimtarku takeba kamar”. Sosai duk suka gamsu da bayaninsa, suka zazzauna aka shiga gaisuwa da tambayar jikin Zinneerah ɗin, wanda Khalipha ya ƙara musu bayani game da matsalar dake tare da ita akan buƙatar hutu bisa ga lalurar cikin jikinta. Sun shiga mata addu'ar fatan sauka lafiya. Maman Halima dai ce da har yanzu ke zaune a kusa da ita tana riƙe da hannunta ta nuna mata wadda aka kira maman Sadiq. “Zinneerah wannan ɗin mahaifiyarki ce, duk da nasan baki santaba kamanin dake a tsakaninku da duk bayan da mukeyi a wajennan zai tabbatar miki hakan, kai namasan zakiji a jikinki koda ba'a faɗaba dan mahaifiya tafi gaban wasa ai.” Kafeta da kallo kawai Zinneerah tayi tamkar wadda ta suma a zaune. Sai da Maman Halima ɗin taɗan taɓatane ta kawo numfashi, sai kuma ga hawaye sharr. Batare datace komaiba tai ƙasa da kanta, daga haka bata sake ɗagowa ta kalli kowa a cikinsuba. Sosai hakan da Zinneerah tayi ya taba zuciyar Maman Sadiq. Dan ta fahimci kamar Zinneerah ɗin fushi take da itane kokuma kalar nata murnar kenan oho. Kowa ma dake wajen da irin fahimtar da yayma shirun na Zinneerah. Murmushi Alhaji yayi, cike da sanin yakamata da hangen nesa irin na manya yace, “Kubata lokaci kamar yanda likitan nata ya faɗa ko”. Sai kuma ya juya ga Khalipha batare da ya jira amsarsuba. “Likita yaushene zaku sallameta?”. Murmushi Khalipha yayi yanaɗan sosa gefen goshinsa. “Alhaji banine likitanba dai, amma insha ALLAH zuwa nan da kwana biyar haka akoda yaushe za'a iya bata sallama tunda jikin nata yana ƙyau, dama matsalar kamar daga cikin jikintane yasa aka riƙeta”. “To masha ALLAH, ALLAH ya kaimu, ya kuma bata lafiya”. A tare suka amsa da amin. Daga haka sukai musu sallama domin tafiya badan Maman Sadiq tasoba. Sai dai taji daɗin abinda Maman Halima ta faɗa akan cewar itace zata dawo ta cigaba da jinyar Zinneerah ɗin har a sallameta. Kowama yaji daɗin hakan har Khalipha. ★★★ Tun daga wannan ranar jiyyar Zinneerah ya dawo hannun Maman Halima, Khalipha ma bai janye daga mata hidimaba, hakama Naziru, ga Alhaji ma ya ƙaru. Sai ga Zinneerah ta sake zama ƴar gata, sai dai abinda kebama kowa mamaki har yanzu taƙi barin damar da zasu fahimceta game da komanta. Hatta haɗuwarta da mahaifiyarta sun kasa gane mike a ranta. Dan taƙi cewa komai, ta kumaƙi nuna murnarta a fili ko damuwarta. A duk yanda Maman Halima ke janta a jiki dan son jin wani abu gameda rayuwarta da Inna taƙi sakin jiki da ita, duk da kuwa ta fahimci babu wata mummunar manufa ga Maman Halima ɗin. Sanin yakamatane kawai irin na matar. Tun daga ranar Maman Sadiq bata sake zuwa asibitinba, sai dai ranta fal yake da damuwar yanayin Zinneerah a kanta. Tadai danne ne kamar yanda mijin nasu ya bata shawara akan ai haƙuri da komai har Zinneerah ɗin ta dawo gida. Itakam Zinneerah bawai farin cikine batai da ganin Mahaifiyartaba. Har ranta ita kaɗai tasan daɗi da take a ciki, sai dai wani ɓangare na zuciyarta ya sakata jin ciwo da zargin mahaifiyar tata ta watsar da itane akan sani kenan. Dan duk wanda zai kalli Maman Sadiq ɗin yasan tana a cikin kwanciyar hankali a gidan aurenta na yanzu. A ganinta idan ba tana saneba yaya za'ai ta watsar da ita tsahon shekaru batare data taɓa waiwayar inda take ba, hakama danginta. Wannan dalilinne ya saka yin kamar batai farin cikiba. Sai dai a randa abin ya faru tasha kuka a ɓoye, still rashin ganin kuma Maman Sadiq bata sake zuwa asibitinba ma ya ƙara taɓa mata zuciya. Ana gobe za'a sallamesu Khalipha yazo mata da zancen da yasata tasha kuka sosai, dan har saida ta kaita da zazzaɓi mai zafin gaske. Ba komai yaja hakanba sai jin Khalipha ɗin zaiyi tafiya. Ashe dama yana karatune a wata ƙasa can daban, hutu yazoyi gida shine yake ɗan zuwa nan asibitin yana rage zaman banza saboda asibitin nada alaƙa da shi. Yanzu kuma hutunsa ya ƙare, yaso ace sai an sallami Zinneerah yaji cikakken labarinta sannan. Amma sai Yayansu yaƙi saurarensa da ɗaga masa ƙafar ƙarin kwana ukun daya buƙata. Ya tabbatar masa da dole-dole saiya koma makaranta gobe idan ALLAH ya kaimu. Shiko a duniya baya taɓa iya ƙetare maganar Yayan nasu saboda ƙauna da girmamansan da sukeyi akaf gidansu koma yace family ɗinsu. Kuɗaɗe masu yawa da sayayya yayma Zinneerah ya kawo mata cike da damuwa. Bayan ya mata nasiha akan yanda zata kula da kanta yace ta bashi lambar mijinta koda ya tafine zai nemsa suyi magana ta waya. Shiru Zinneerah bata iya cemasa komaiba akan wannan magana. Ya sake mainaita mata, nanma shiru tai sai hawaye dake gudu a kumatunta. Ƙyaleta Khalipha yayi, dan a tashi fahimtar kawai ta bashi cewar Zinneerah kodai rabuwa tai da mijin nata kokuma bata buƙatar ana alaƙantata da shi bisa wani dalili na ɓacin rai. Dan haka ya ƙyaleta kawai saboda ya amsa lambar Naziru. koma miye zai dinga ji daga garesa kawai. Haka dai Khalipha yay mata sallama ya wuce ya batta da kukan zuci. Dan hatta Maman Halima da bata daɗe da saninsaba yaron da halayensa sun sakashi shiga ranta sosai. Dalilin tafiyar Khalipha gaba ɗaya yinin ranar a rashin daɗin rai Zinneerah tayisa a asibitin, harma tanaji ta ƙagara a sallamesu gobe idan ALLAH ya kaimun, gara taje gidan maman tata taji nata dalilin itama na guje mata datai ta barta cikin wahalar rayuwa.. Haka dai a daddafe suka kai washe gari, inda ALLAH ya taimakesu aka basu sallama tunda safe. Dan haka Nasiru yazo ya kwashesu dan yakai gidan yayan nasa inda mahaifiyar Zinneerah ke rayuwa a yanzu matsayin gidan aurenta..............✍ *_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya.

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182