Chapter 55
Chapter 55
wani irin matsananciyar kunya. Ta kwaso kayan tana rintse ido kamar ta fasa ihu. shikenan ya gama gane mata sirrinta wayyo ita Zinne. Koda ta fito sum-sum ta wuce bata yarda ko sashen da suke ta kallaba. Fitar da yay da daddaren saboda zuwan abokinsa Dr Mahmud ta bama yaran gidan damar shan sharafin hirarsu yanda suka saba. Sai dai anayi ana leƙen waje wai karya shigo. Sai ma ALLAH ya taimakesu har suka tashi bai shigo ɗinba. Washe gari da safe ma har suka gama breakfast kowa ya fice yana ɗaki bai fitoba. Kasancewar juma'a ce da wuri su Zinneerah suka dawo gidan. A bedroom ta iske hajiya iya zaune tana karatun AL-QUR'ANI. Bata zaunaba ta ajiye school bag ɗinta da cire hijjab ɗinta ta fice zuwa kitchen dan yunwa takeji, yau bata wani zauna tayi karin kirkiba suka fita makaranta. Gaba ɗaya ta shafa'a da kasancewar sa a gidan. dan haka ta fito kanta tsaye ko ɗan kwali babu akan nata. Sai gashinta data wanke dan zuwa kitso dake ɗaure a tsakkiya. Tanada gashi duk da bamai wani uban tsaho bane, dan yakanzo mata dai har kafaɗa musamman idan ta wankosa a saloon. A yanda take tafiyar yasa sam bataga mutum dake tahowa a gabantaba. Gab sukai karo da juna. Ta ɗago a firgice tana murza goshinta zatai magana, amma sai maganar tata ta maƙale a maƙoshi ta tsaya kawai tana kallomsa. Shima ɗin dai kallo yake mata irin na sani, sai dai ya kasa tunano a inda yasan fuskar. Baki ta buɗe da nufin ambaton sunansa ya katseta yana murmushi. “Sorry Beauty. Ko kece Sister ɗin tamune?”. Saurin haɗiye maganar tata tai itama mamaki na neman kasheta a tsaye. Kenan bai ganetaba komi? Kokuwa basarwace irinta masu hannu da manda. Aiko inhar hakane itama ta iya ai, musamman a yanzu da take ƙara samun wayewar rayuwa da zamantakewa wajen malamta su Jamal. Kanta ta kaɗa masa tana ƙaƙaro murmushi. Tace, “Eh nice Yayanmu, kunzo kafiya?”. “Alhmdllh, amma kinma sanni kenan?”. “Eh mana. Na sanka a bakinsu Bahijja”. “Kai-kai a bakin magulmatan gidannan kenan. to ALLAH yasa dai basu koyama ƙanwar tawa gulma ba?”. Ƙayataccen murmushi ta saki har haƙoranta na bayyana fili. Hakan yayi dai-dai da isowarsa wajen. Ta buɗe baki da nufin bama Khalipha amsa idanunta suka faɗa cikin nashi. Wani irin yarrr tsigar jikinta ta tashi, tai azamar maida kanta ta duƙar ƙirjinta na bugawa saboda abinda zuciyarta ta hasko mata a yanzunma kamar jiya data fara ganinsa, koma wanda yafi na jiyan, idanunsu iri daya hatta da kwayoyin ciki. Juyawa Khalipha yayi domin son ganin abinda ya hanata maganar, yay murmushi a dai-dai sanda yayan nasu ke ƙoƙarin gittasu tamkar baima gansuba. Da sauri Khalipha yace, “Barka Yayanmu”. Hannu ya ɗaga masa kawai yawuce abinsa. Hakan yasa Khalipha ƙara matsawa gaban Zinneerah da kanta ke a ƙasa. Cikin raɗa-raɗan magana yace, Beauty bara muje massallaci, idan na dawo zakizo ki tayani hira”. Daga haka yabi bayan Yayan nasu ɗakin Hajiya Iya daya shiga. Nannauyan numfashi Zinneerah ta sauke tare da lumshe idanu ta dafe kirjinta. Zuciyarta na gargaɗinta akan abinda ƙwaƙwalwata ke hasko mata maiban tsoro da ruɗani. jiki a saɓule ta wuce kitchen dan neman abinda zata sakama cikinta ko taji dama. Sosai ran Zinneerah yake a jagule da tunani mai tarin ruɗani kala-kala. Ba komai ya janyo hakanba sai ganin da taima Khalipha. Wanda zuciyarta taƙi aminece mata cewar bai ganetaba. Amma har a ranta tana shiga ruɗani da al'ajabin yanda ya nuna ɗin. Itako tayi imani da ALLAH ko shekaru fiye da haka sukai bata gansaba duk randa suka haɗu saita ganesa. Kenan itace keta shirmenta shi baimasan tanayiba, koda yake alkairinsa garetane yasa ta kasa mantawa dashi bawai wani abuba. A take ƙwalla suka cika mata idanu, sai dai tai ƙoƙarin hanasu su zubo dan ba wannan matsalar kaɗai bace matsalarta, hadda wadda take tsoron bayyanar tabbatuwarta saboda ɗimuwa. Duk yunwar da take iƙirarin ji sai gashi ba wani abincin kirki taciba bakuma ta yarda ta fitoba har saida ta tabbatar a ranta sunbar gidan. Koda ta koma ɗakin Hajiya iya wanka ta farayi itama tai salla sannan tai zaman karanta suratul kahfi. Bayan ta kammala suka gaisa da Hajiya iya take sanar mata “Af Inno na kinga ina neman shafa'a. Idan kin idar da addu'arnan jeki ki gyara Moddibo ɗakinsa”. Cikin dauriya da danne damuwoyinta tace, “To Granny”. Daga haka ta miƙe zuwa ɗakin nasa datai zaman watanni kusan uku a ciki. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gyara komai ta baza ƙamshi. dan ita bama taga wani datti da ɗakin yayiba. Rufo ɗakin tai ta fito. Hakan yayi dai-dai da fara shigowar samarin gidan falon alamar yanzu suke dawowa daga massallaci. A ƙa'ida kuma duk irin wannan ranar anan suke lunch saɓanin breakfast kawai da sukeyi anan kowacce safiya. Ƙasa tai da kanta cike da jin kunyar kallon da Moos'ab ke mata tunda suka haɗa ido. Batare da tayi tunanin hardasu Khalipha ɗin suke tareba itama ta zauna a falon saboda harda Jamal daya ja hannunta suka zauna a centre table ɗin falon yana miƙa mata ledar hannunsa da faɗin, “Surprise sweet sisi”.. Murmushi tayi tana ƙoƙarin buɗe ledar. Ganin abinda ke a ciki ya sata waro manyan idanu waje ta ɗago da niyyar yin magana taja birki wajen ganin ta haɗiye abinda ke a bakin nata saboda idanunta da suka sauka akan wanda batai fatan ganiba.... Ledar hannun nata Khalipha ya zare yana faɗin, “Ƙanwata mi muka samu haka?”. Kasa amsa masa tai saboda wani kallo data kasa fassara inda ya dosa da Yah Adnan ya watso mata. Sai dai zata iya fassarashi da kamanni dana gargaɗi ko takaici. Tsam ta miƙe batare data iya amsa Khalipha daya fiddo agwaluma ɗaya dake a ledarba yana faɗin, “Lallai kayan daɗin nan dani za'a shashi ƙanwata”. Tana ƙoƙarin gittashi tace, “Na bakama Yah Khalipha kasha ma duka kawai”. Saurin bin bayanta yay dan shima yaga kallon da Yayan nasu yay mata, wanda ya tabbatar shine ya hanata zama wajen. “No. Kinga tsaya Beauty guda ɗaya ma ya isheni karɓa kayanki”. Badan tasoba dole ta tsaya ta amsa. Shi kuma yace, “Thanks” cike da wani salo daya sanya Moos'ab dake binsu da kallo cike da kishi yay azamar kauda kansa garesu. Koda ta samu ta shige bataso sake fitowaba Hajiya Iya ta korota domin zaman yin Lunch. Badan tasoba dole ta biyota, dan ko tace taci ba barinta zataiba sai dai ma tai mata faɗa. Duk sun hallara a dining har Baffa dasu aunty Ni'ima. Baffah ta fara gaidawa da juma'a, sannan ta zauna a kujerar data rage kusa da Khalipha da Meenal. Hajiya Iya kuma ta zauna a mazauninta da kowa ya sani. Sai da Ni'ima ta fara miƙewa ta zubama Hajiya iya abincin sannan Baffah. Sanin halin Yayansu itama Safiyya ta miƙe ta zuba masa dukkan abinda tasan yana buƙata a wajen. Daga haka kowa ya fara ƙoƙarin zubama kansa abinda yafi buƙata. Zinneerah dai duk jinta take a matuƙar takure. Kaɗan ta zuba dambun cus-cus a filet ɗin gabanta. Tana ƙoƙarin ɗaukar Mango juice ta zuba Khalipha ya rigata azamar ɗauka jug ɗin ya zuba mata a ƙaramin cup yana murmushi. “Thanks you Yaya” ta faɗa a hankali tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182