Chapter 164
Chapter 164
da ayyukanka. Idan kuma ka dage sai ka samu to lallai San zuciya kuwa ai ɓacintane ga duk mai sha'awa ko buri. Duk wanda basu haihu ba ya ALLAH ka azurtasu da zuri'a masu albarka a garesu, idan ba alkairi bane ALLAH ka sakanka musu da abinda yafi alkairi, ka yalwatasu da tarin haƙuri da juriya a zukatansu”. Da amin duk suka shiga amsawa, kuma kowa ya gansu da bayanin waziri, saurama suka shiga tofa albarkacin bakinsu. Sai da duk mazan suka gama kace nace Mahma da tun ɗazun al'ajabin su Zakiyya ya hanata tofa komai ta duba su Zakiyyan. “Wannan shine abinda naketa nusar daku amma kuka kasa fahimta, bansan miyasa a mafi yawan lokuta gatan rayuwa da tagomashin arziƙi dake zuwa cikin hannayenmu ke dulmiyar da zukatajen jin muna sama da kowa ba. Zamu iya zartar da hukunci ga kowa, zamu iya taka kowa dan ko anje an dawo babu yanda zaiyi damu. Duk da dai anata maimaita magana ɗaya amma dolene a faɗa. Kun zalunci yarinya saboda kuna mata kallon mai ƙarancin gata, sai gashi UBANGIJI ya biyo muku ta inda bakuyi zatoba ya ruftaku a ramin da kuka tanadi sakata ku kuka afka. Shi kansa Abdul-Mutallab kun cutar dashi ai, gara ace fitowa kukai kuka shaida masa ƙudurinku, idan ya amince fine, idan bai aminceba sai ku bi duk hanyar data dace wajen ganin kun lallaɓasa ya yardan koku haƙura har ALLAH ya kawo mata iyakar da zata samu. To yanzu dai dukma abinda zai faru ya faru. kun aikata a ɓoye ALLAH ya buɗa kowa ya gani, kunyi danku tsare mutuncinku gashi ya zube a idanun kowa. Kunyi don samun haihuwa, gashi an haihu ɗan yafi ƙarfinku dan nima ina bada goyon bayan hukuncin Abdul-Hakim (Mai martaba), kunyi dan gudun kishiya, ga kishiyar nan mai daraja ma kuwa da inhar Abdul-Mutallab ya wulaƙantata koda na second guda bazamu yafe masaba, dan ta cancanci a kula da ita a riritata. Kunyi dan kar Abdul-Mutallab ya suɓuce muku, gashi ya suɓuce mukun ya dawo inda baƙwaso ya rayu dagashi har ƴar uwarsa. Da wannan kawai aka barku ya isheku, dan nidai banga ribar da kukaciba anan sai asarar kuɗaɗenku dana lokacinku da kukayi a banza a wofi, idan kuma wannan baiwa da waɗan can ma basu yafe mukuba to yanzu aka fara wasan. Koda sun yafe muku sai kuma ku jira hukuncin UBANGIJI a gareku dan shi ne yafimu sanin abinda ya cancanta da mutane masu hali irin naku. Hindatu kinfi kowa ganganci matsayinki na uwa, duk da kuwa Zakiyya ce tai amfani da abinda ke damuwarki ta sarrafaki cikin sauƙi kika afka, amma ba komai ya jawo hakanba sai gurɓataccen tunaninki da son zuciyarki. Wanda inada tabbacin son Kabeer ne ɗawainiya dake ba komaiba, girman kai ya hanaki nutsuwa ki nema sulhu da shi sai kike huce komai akan yaronsa da baijiba bai gani ba. Gashi nan ai kin rasa Kabeer ɗin da Abdul-Mutallab ɗin duka harma da Adilah. ALLAH UBANGIJI ya rabamu da son zuciyoyinmu, ya yalwatamu da haƙurin ibadarka. Daga ƙarshe dan ALLAH ina roƙama ƴan uwana gafara a gareku iyayen Zinneerah, ku yafe musu, karkuyi dubi da halayensu da cutar da sukaima ƴarku. Dan tunkan aje ko ina ALLAH ya saka mata. Dan ALLAH ku gafarcesu ko zasu sami sassauci daga raɗaɗin da za'a bar rayuwarsu da shi. Keko Zinneerah bazance ki yafe musu ba, idan zaki iya yafe musu Alhmdllh, idan kinga bazaki iyaba ki barsu da ALLAH zai cigaba da saka miki ta hanyoyi daban-daban kamar yanda ya fara tun yanzu anan duniya. Kabeer da Hajiya Mama (Hajiya iya) kuma dan ALLAH ku yafe musu badan halinsu ba, kodan darajar Abdul-Mutallab dake a tsakani, dan ya can-can-cin yabo yaron nan ta fannoni daban-daban. Duk da kun sakashi a tsakiya game da wannan al'amari a koda yaushe burinsa yaga ya saka farin ciki a zukatan kowannenku koda kuwa shi zai ƙuntata tashi zuciyar. Dan ALLAH muyi haƙuri mu yafi juna kodan shima yay farin cikin da yaketa fata akan kwanciyar hankalinmu”. Baba ne ya fara jinjina kansa bayan kammalawar Mahma. Yace, “Kinyi bayani mai ƙyau hajiya, kuma nidai ta ɓangarena na yafe musu wlhy, dan koba komai abinda suka aikata ɗin ya zama tsanin nasara ga gudan jinina. Shiyyasa akace idan kaga UBANGIJI ya jarabceka da wani al'amari ka nutsu wajen kwatanta haƙuri dan zata iya yuwuwa wani tsanin zuwa ga nasara ne. Na yafe musu. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya”. A take aka shiga amsawa da amin duk cikin farin ciki. Maman sadiq da batace komaiba tun zamanta a wajen, tace, “Tabbas abubuwa da yawa sun faru an maimaita wasu anan amma wasu bazasu maimaituba. Ni shaidace daga wahalhalun cikin nan da yarinyarnan tasha wanda da da ƙarar kwana ranar haihuwarsa da ta bar duniya. Amma Alhmdllh, nagodama UBANGIJIN daya rayata, ya kuma kaimu ga ganin wannan ranar tunda gata a ɗakin mijinta cikin mutinci, kuma gaskiya ta buɗe a garemu ALLAH ya wanketa tun anan dunuya. Da yaso sai ya barmu muyita kallonta da laifin har ranar tashin alƙiyama. Nima na yafe muku domin ALLAH da wasu dalilai da Gwaggo ce silarsu (Hajiya iya) ALLAH ya yafe mana baki ɗaya ya kuma kiyaye na gaba”. Itama godiya suka shiga mata da amsawa da amin. Kafin Hajiya iya ta fara magana. “Tabbas dolene nima nace a yafemin ɗin bisa wani dalili, dan ƙila daban matsama Moddibo da ƙara aure ba da tunaninsu bai karkata ga hakan ba. Ni kuma ba komaine ya sani damuwarba sai ganin yanda matarsa bata ɗaukemi da darajaba. Hakama Hindatu. dan duk da Kabeer ya fita ƙarfin faɗa aji akan yarannan tana nuna masa iko a kansu, ko zancen auren yarinyarnan bamusan komai ba saida yazo gab. Koda yake duk ta wani tone-tone ya wuce, Moddibo ka yafemin kai da matarka dan zan iya saka kaina matsayin silar faruwar komai”. “Bake bace sila Granny, dan koda kikace na ƙara aure baki tursasaniba, sannan tsarin da sukazo muku dashi ya sakaki wannan tunanin kema. Dan haka nikam kima daina neman gafarata bakimin komaiba why”. AK ne ya faɗa cikin dauriyar abinda yakeji game da jikinsa. Mammah ta karɓe da faɗin, “Tabbar Inna ba laifinki bane, nice da wannan laifin, dan daban zurfafa da yawaba akan yaran nan da Zakiyya bataci galaba a kainaba har nakai ga bata goyon bayaba, dan ALLAH Adnan ka yafe min kaji, ajizancine na ɗan adam da son zuciya da tsoron rasaku tamkar yanda gangancina ya kaini ga rasa kabeer. Kishi ba hauka bane, kuma halas ne. Amma irin namu yayi muni da yawa dan muna zafafawa, da nayi haƙuri da hukuncinsa a wancan lokacin da duk haka bata faruba na tabbata. Dan ALLAH ku gafarceni baki ɗaya. Ɗiyata Zinneerah kema dan ALLAH ki yafemin kinji, wlhy bazan ɓoye mukuba tun randa na diro ƙasarnan naga yaron nan da kika haifa ƙaunarki data yaron ta kamani, duk abinda kukaga inayi borin kunyane kawai, amma har cikin raina son ɗanki dake kanki ya shigeni, koda nake cewa kar Adnan ya taɓaki ya sakeki inason na gwada yanda yake sonkine kawai ba wani abuba, kuma koda ya gama tsarani bawai ban fahimci tsaranin yayba. Sarai na san bazai iya sakinkiba wlhy, nima kuma bama zan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182