Chapter 134
Chapter 134
dawowarsu daga wajen walima ne Hajiya iya ta tilasta mata shan tea ganin bataci komaiba a can sam. Kusan rabi tasha tace ta ƙoshi, bai tanka mataba bai kuma kalletaba yanata aikinsa. Tsahon minta ɗaya ta fahimci baima da lokacinta sai ta cigaba da shan shayin hawaye na ziraro mata, cikin dabara take saka bakin lafaya ɗin tata tana sharewa harta kammala shanyewa ta miƙe da kofin a hannu. Tunanin ina zata kai ya sata duƙar da kai ƙasa, muya na rawa tace, “Ina ne kitchen?”. A yanda tai maganar ya tilasta masa ɗagowa ya dubeta na kusan sakan huɗu, ajiye lap-top ɗin yayi gefe ya kamo hannunta ya sake zaunar da ita kusa da shi, kansa tsaye ya janye lafayan data sa har a saman kai da ɗaura hannunsa a saman wuyanta. Sosai jikinta yay zafi. Kansa ya ɗan girgiza batare da yace komaiba ya miƙe tare da ɗaukar cup ɗin ya fice, zamewa tai a hankali ta jingina da kujerar tana lumshe ido da jan ajiyar zuciya, acan ƙasan ranta kuwa fal mamakinsa take da gulmarsa akan ashe yana da ɗan sauƙin kai. Tashi tai zaune jin ya sake dawowa, kanta a ƙasa harya ƙaraso ya sake zama a inda ya tashi yana miƙa mata magani da ruwa daya zubo a glass cup, babu musu ta amsa dan tana buƙatar maganin kodan ciwon da kanta ke mata. “Tashi ki cire wannan abun da kika naɗe jiki kamar magani kije ki kwanta”. Ya faɗa kansa tsaye yana ɗaukar lap-top ɗinsa ya cigaba da aikinsa. Miƙewa tai cikin bin umarninsa, sai dai gaba ɗaya tama rasa ta ina zata fara warware lafayar saboda tsananin kunya da shakkarsa. Ta saci kallonsa yafi sau goma, ganin shi hankalinsa ma nakan aikinsa yasata juya masa baya da fara warwarewa da sauri-sauri, ko batun linkewa bataiba ta ajiyeta gefenta ta haye gadon taja bargo har wuyanta tana sauke ajiyar zuciya dajan numfashi a gwame. AK daba kallonta yake ba, burinsa kawai ya kammala aikin shima ya kwanta dan kansa ya fara ƙarfafa ciwo ya ɗan dubeta jin ajiyar zuciyar data ja da ƙarfi. Ita kam runtse idanunta tayi da fatan barci ya ɗauketa ko zataji sassauci da nutsuwar halin da take ciki a yau. Har yanzu ta kasa daina imagine cewar Yayansu ne mijinta. Ta rasa miyasa su Granny sukai tunanin yin wannan kwamacalar? Inama laifin a bata Khalipha ko Moos'ab, amma maganar ta girmama Yah Abdul-Mutallab matsayin mijinta na aure. Da wannan tunane-tunanen barci ya ɗauketa, harya kammala abinda yake ya fita a ɗakin kusan mintuna talatin sannan ya dawo, fitilar ɗakin ya kashe zuwa ta barci, ya nufi gadon ya hau yana ɗan yamitsa fuska saboda kansa dake masa ciwo. Sai da ya zauna yaɗan jingina da gadon yana furzar da huci da lumshe idanu, kusan minti ɗaya sannan ya buɗe da waiwayawa yana kallonta ‘Komanta mai sanyi dai-dai da yanayinta’ ya ayyana a ransa dakai hannu ya gyara mata bargon dake neman toshe mata hanci. Ya mata kallon kusan mintuna uku kafin ya janye idanun nasa da sauke ajiyar zuciya. Cikin barci Zinneerah taji kamar an sakata cikin wani abu mai ɗumi da yafi bargon bata kariya daga sanyin da takeji, taja numfashi da iskarsa ta haɗa da daddaɗan ƙamshin turarensa wajen shige mata hanci, gabantane ya faɗi dan tabbas ɗumin yayi kama dana jikin mutum, babu shiri ta buɗe idanu duk da ɗakin babu wadataccen haske kuma kanta na'a ƙirjinsa ne. Ba ƙaramin harbawa zuciyarta tayiba na tsoro, sai dai can wani shashi na gargaɗinta akan karta nuna ta farka zaifi taimakawa tsananin kunya da fargabar dake tare da ita. Dole ta ƙarajin zuciyarta da jinin nikinta na cigaba da tsitsinkewa da tsananta sauri wajen gudu. Sarai ya fahimci ta farka, amma sai ya shareta saboda taimakama zuciyarta dake harbawar da har yake iya jiyowa bata salama. Su dukansu sun jima basuyi barciba kowa yana saƙa mai fisheshi, yayinda ɗumin jikinta ke raguwa saboda taimakon daya bata da jikinsa. Daga ƙarshe dai su duka barcin ya ɗaukesu saboda maganin da suka sha. _________________★ A ɓangaren su Mammah kuwa ita da aunty Zakiyya barci sai dai ɓarawo ne ya figesu, sunason zaman tattauna abinda ke musu kaikawo hakan ya gagara saboda Mahma, daga ƙarshema Mahma hukunci ta yanke ita zasu kwana ɗaki ɗaya da Mammah, aunty Zakiyya kuna ta kwanta wajen Farah. Wannan abu ya musu ciwo su duka amma babu damar magana. Itako tayi hakane saboda fahimtar take-taken Mammah akan son hana AK nuna kulawarsa ga amaryarsa. Rashin mafita yasa Mammah amsar wayar aunty Zakiyya ta sake turama AK saƙo bayan ta kirasa a wayar ta masa gargaɗin farko. sarai Mahma na lure da ita amma sai batai maganaba ta girgiza kai kawai tana nemawa ƴar uwar tata shiriyar UBANGIJI danshi tafi buƙata a yanzun. ★★★★ Kiran sallar farko ya buɗe idanu kamar yanda ya zame masa jiki, dan ko a london yake a irin wannan lokacin yake farkawa duk asubahi saboda alarm da yake saitawa. Sam barcin bai isheshiba, hakan ya saka idanunsa yi masa nauyi matuƙa amma ciwon kan ya sauka. Akan Zinneerah dake nannaɗe a jikinsa ya saukesu, yanda fuskarta tai wani fayau a barcin ya sakashi nutsuwa wajen ƙare mata kallon kusan mintuna uku, hannunsa dake a saman cikinta ya ɗaga a hankali yakai ga fuskarta yaɗan tallafi kuncinta ta gefe da ɗaura babban yatsansa akan laɓɓanta da suka daɗe suna tsole masa idanu. Yatsan ya shiga zagayawa a kansu taushinsu da santsinsu na masa daɗi, duk dama aɗan bushe suke a yanzu. Cikin barci ta dingajin kamar ana shafa mata lips, ga kuma hannunsa da kusan nauyinsa ke a ƙirjinta, ɗan motsawa ta shigayi alamar zata farka, sai kawai ya janye hannun nasa ya tashi zaune tamkar bashi ya aikata ba, buɗe idanunta yayi dai-dai da saukarsa a gadon yana faɗin, “Ki tashi kiɗan watsa ruwan ɗumi zakiji jikin ya saki gaba ɗaya”. Cikin muryar barci yay maganar dan haka ta fita a sanyaye da ɗan kauri kuma. Bata iya motsawaba harya fice dan wata irin matsananciyar kunya ke cinta, wai yau itace kwance a gado ɗaya da Yayansu. Jikinsu manne da juna, kai itako ina zata kai wannan abun kunya yau. Da wannan tunanin ta miƙe da ƙyar ta nufi toilet domin yin amfani da shawrsa nayin wanka. Tako ji daɗin wankan, dan jinta take fayau saboda zazzaɓin ya saketa, tana fitowa jikinta kawai ta tsane ta ciri doguwar rigar jallabiya a akwatin daya cirar mata kayan barci jiya ta saka, ta ɗauka turare a handbag ɗinta ta fesa sannan ta saka hijjab domin yin salla. Bayan ta idar da ƙyar ta iya zaman yin azkar, tanayi tana gyangaɗi harta samu ta kammala da ƙyar ta sake komawa gadon ta kwanta dan wani irin barci takeji bana wasaba. Shima koda ya dawo daga massallaci sashensa ya wuce ya sake kwanciya koma azkar ɗin shi bai iya zaman yiba. ★★★ A gidansu Hajiya iya kusan baƙi duk sun tashi da haramar wucewa yau, musamman ma ƴan danya da jikin Tinene ya rikice, dan kwana tai tana sheƙa amai a daren jiya, sai gabannin asuba tai barci. Da safe basu tadataba har suka kammala shirinsu, kusan ƙarfe takwas aka kawo musu abincin kari suda ƴan ɗanmusa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182