Chapter 73
Chapter 73
da ma'aunin hankali shekarun little zasu iya kaiwa dai-dai da hasashen haihuwar Zinneerah. Amma yaƙi ya yarda da cewar shine ɗan data haifa ɗin. “Kanwata sai ina kuma?”. Murmushi tai masa daɗan shafar wuya. “Yah Khalipha zan fitane kawai”. Murmushin ya sake sakar mata shima, da matsawa ya bata hanya ta fice shikuma ya ƙarasa shigowa idanunsa na sauka akan Yayansu dake bama Little abinci a baki. Ji yay sun wani bala'in birgesa. Har yana ayyanawa a ransa inama ace yaron nan jinin yayan nasune da gaske. Takawa Khalipha yay ya zauna kusa da yayan nasu yana mai shafa kan little ɗin. Juyowa little yay ya kallesa sai kuma ya juya ya cigaba da karɓar abincin. Kaɗan yaci abincin yace ya ƙoshi, badan AK ya gaji da bashiba ya haƙura ya barsa. Haka ya cigaba da zama a jikinsa har ya sake komawa barci. Su Mmn Sadiq basubar gidanba sai wajen tara saura na dare. Da ƙyar aka raba little da jikin Yayah Adnan, dan lokacin da Khalipha dazai kaisu yazo amsarsa sai gashi ya farka a bazata. ya ƙanƙame AK ɗin yaƙi zuwa wajen Khalipha. Murmushi AK yay da lumshe idanun yana sunbatar little ɗin a goshi da shafar bayansa. Shi kansa ƙarfin hali kawai yakeyi, amma ji yake kamar karya rabu da yaron dan yayi bala'in shiga ransa. Daga ƙarshe dai da ƙyar ya yarda Khalipha ya ɗaukesa dan sai da aka haɗa da masa wayo. Motar na ficewa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya hawayen da baisan kona minene ba suna ciko masa idanu. Ƙoƙarin maidasu yay yana furzar da huci mai zafi da nufa garden ya zauna dan babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar kaɗaici. Yanda AK ya kaɗaice kansa Zinneerah ma harabar gidan ta fito can wajen motoci ta hau bayan ɗaya daga ciki ta zauna tare da faɗawa duniyar tunani. Gaba ɗaya zuciyarta a ruɗani da ɗimuwar kiɗima take. Shin a ina aka faɗi a ragaya ne? Wane darasi rayuwa keson karantar da ita a wannan gaɓarne bayan darasissikan data baro a shekarun baya?. Ko mahaukaci ya kalli little ya kalli Yah AK dolene ya danganta alaƙar jini a tsakaninsu. Dan abinda zai matuƙar baka mamaki ba kammaninne kawaiba. Hatta da wasu a cikin halayen Yah Adnan akwai alamunsu ga little. Kenan to....... “Kai ina”. Ta faɗa a fili tana girgiza kanta dake matuƙar sara mata. Kamar ance ta ɗaga kai can ta hango Baffah a barandar sama yana kaikawo alamar shima akwai abinda ke damunsa, wanda bata raba ɗayan biyu zancen kamanin little ne da Yayan nasu. “Ya ALLAH kai ne gagara misali, ka buɗemin tunani, ka yalwatamin fahimtata. Ka gafarta mini zunubaina”. Ta faɗa hawaye na silalo mata akan kumatunta masu zafi. Zurfi sosai ta ƙarayi a tunani har motar Khalipha daya kaisu mmn sadiq ta shigo gidan bata saniba. haskatan da yayne shima ya sakashi ganinta. yana gama fakin ya nufo inda take. Sau biyu yanayin sallama babu amsa, har dai ta kaisa ga ɗan bugar motar ta gefen kunnenta sannan ta kawo nannauyan numfashi tana dubansa. “Wane irin tafiya tunanine haka da zurfi ƙanwata?”. Murmushin yaƙe tai masa tana duƙar da kanta ƙasa. Hakan datai sai ya ƙara fiddo masa da kamanninta na baya sosai. Yay murmushi yana gyara tsaiwarsa da faɗin, “Zinneerah na tambayeki mana?.” Gabantane ya faɗi, amma sai cikin dauriya tace, “Ina jinka Yah Khalipha”. Kansa ya kaɗa mata yana ajiye keys ɗin hannunsa da wayarsa alamar maganar mai muhimmanci ce. “Dan ALLAH ki faɗamin gaskiya kin manta dani ko?”. Duk da tambayar tasa tazo mata a bazata dan ba ita tai zaton jiba sai da taji dumm. Ganin ya kafeta da idanu ya sata yin murmushin yaƙe tace, “Ban gane mi kake nufi ba Yah Khalipha”. “Nasan kin gane Zinneerah, amma tunda hakane bara na miki dallah-dallah”. “Tun randa na ganki a gidan nan nasan nasan fuskarki, amma na rasa ina na sanki dan kin banbanta da waccan ɗin dana sani a yanzu. Nasha gwadaki naga ko zaki nuna ke kin sani amma baki nunaba, sai yau da naga mama na tabbatar da cewa kece. Shiyyasa mamaki ya kamani na rashin nuna kin sanni da kikai kafin yau”. Tabbas taji kunya. amma sai ta dake, ta buɗe baki da zummar bashi amsa sukaji ƙamshin turarensa da takun tahowarsa. Duk kallon waje. sukai Zinneerah na haɗiye maganar da tai niyyar yi. Ganin yanda yake kallonsu ya sata jin wani iri, babu shiri ta diro akan motar tai cikin gida sum-sum duk da alamar ta zauna da Khalipha ke mata da hannunsa. Khalipha da shi kansa kallon da Yayan nasu ke musu ya bashi mamaki, cikin dauriya yace, “Yayanmu na zata ka kwanta ma ai”. “Shiyyasa kazo nan kake taɗi?”. Ya faɗa yana wucesa. Saurin waro idanu Khalipha yay waje da biyo bayansa. “Ni Abdul-Mutallab, jikan Abdul-Mutallab, ƙanin Abdul-Mutallab wane ni Yayanmu”. Ɗan juyowa yay ya dubesa. Hakan yasa kunya kama Khalipha yakai hannu yana shafa wuya da risinar da nasa idanunsa ƙasa. Wani irin juya idanunsa da suka ɗan fara sauya kala yayi yay gaba batare da ya sake cema Khalipha ɗin komaiba, dan harga ALLAH baya cikin hankalinshi da nutsuwar. Binsa da kallo Khalipha yay harya shige sashen Hajiya Iya. Kasa binsa yayi, sai kawai shima ya nufi sashensu zuciyarsa na ƙoƙarin karkato masa wani abu daban. ★★★★ Washe gari da safe suka tashi da tashin hankalin ruɗewar jikin Hajiya Iya. Dan tunanin data kwana yi jiya game da kamanin little da AK ya ja jininta sake hawa sama matuƙa. Ita Zinneerah bata fahimtaba dan duk zatonta Hajiya Iya barci takeyi, dan itama kanta barcin nata rabi da rabi ya kasance. Sai da ta farka da asuba taji hajiya iya na wani irin wahallen nishine hankalinta ya tashi. Ruɗani ya sata fita da gudu zuwa ɗakin AK ta hau bugawa tana kiran sunansa. Zaune yake saman sallaya yana karatun Al-Qur'ani dan shi ko sau ɗayama bai rintsa ɗinba. Yanda yaga rana haka yaga dare, a daren na jiya. Tunda yaji bugun ƙofar yasan ba lafiyaba. Ya ajiye Qur'anin tare da miƙewa a nutse ya nufi ƙofar ya buɗe ko sauraren Farah data farka da jan tsaki baiyiba. A rikice Zinneerah ta damƙo hannunsa jikinta na rawa ga hawaye na kwarara. “Yayanmu Granny, Granny Yayanmu, dan ALLAH kazo Granny karta mutu”. A take shima ya rikice. Ya shiga binta a baya tana riƙe da hannunsa har sannan tana jansa. Tunda suka shigo yaga halin da Hajiya Iyan ke a ciki sai hankalinsa yafi nata tashi, a take yay kanta yana kiran sunanta da ƙarfi. Zinneerah daketa yarfe hannu kukanta na ƙara tsananta ya duba cikin sarƙewar harshe yace, “Ɗakkomin waya a ɗakina, m....” Batama bari yakai ƙarsheba ta kwasa da gudu ta fice. A guje ta shigo ɗakin har tana bangaje Farah data sakko daga gadon tana mitar an tasheta tana barcinta. Wanwar Farah ta zube a ƙasan tiles ɗin amma ko kallonta Zinneerah bataiba ta nufi wayar data hango a drawer gefen gado duk da bata da tabbacin nasane. Sai dai tana kaiwa garesu ƙamshinsa dake manne dasu suma ya tabbatar mata nasanne. Duka ukun ta kwasa ta sake tsallake Farah dake nishi a ƙasa ta fito. Da ƙyar ya iya saita kansa ya lalubo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182