Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 104

Chapter 104

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

dai-dai ya ɗago ya sashi saurin haɗiye sauran zancen yana zazzare ido. AK ya gyara tsaiwarsa idanunsa na canja launin ɓacin rai, cikin nutsuwarsa da rashin sakewa yace, “To dakazo kana faɗamin idan kuma nine nayi cikin fa?”. A razane mutumin ya waro idanu waje. Sai kuma yay saurin yin ƙasa da kansa yana girgizawa. “Haba-haba Alhaji ni nasan hakanma bazata faruba. Ai daga ganinka anga mutum mai mutunci da kamun kai, kawai dai an rufekane, amma dan ALLAH karka bari so ya rufe maka ido ka ɗaukama ƴaƴanka uwar banza”. “Ai kaine banzan sha-sha-sha” AK ya faɗa a fusace, cikin kaushin murya yace, “Mutumin banza kawai, saboda tsabar rashin mutunci ko kunya bakajiba kai kazo kana aibantamin mata? To bara na sanar maka kaima kaje ka sanar tunda naga shine aikinka. Shi wannan cikin da kuka ganta dashi nawane. Nine nai mata kuma ta haifamin, daɗin hakannema yasa na aureta yanzu stupid ɓacemin anan”. Da sauri mutum yabar wajen kuwa tamkar zai kifa, AK ya rakashi da wani irin kallon tsana da takaici, tsabar takaici dole ya buɗe motar da yake a jingine ya shiga batare daya rufe murfinba ƙafafunsa a waje. Sosai launin idanunsa suka sake canjawa, badan kar ace yayi ƙarantaba da lallai saiya nunama shegen mutumin nan kuskurensa yau wlhy. Tsaki yaja da dafe kansa dahar ya fara masa ciwo ƙasa-ƙasa zuciyarsa na masa zugi. Tabbas yanada buƙatar dawowa ƙauyen nan domin wanke yarinyarnan duk da har yanzu baisan yaya ya samar da Abdul-Mutallab ba..... “Yayanmu!” Moos'ab ya sake kiran sunansa a karo na uku. Sai yanzu kunnensa ya ji, ɗago idanunsa yay ya dubesa, Moos'ab yay ƙasa da kansa cikin girmamawa yace, “Baffah ke kiranka”. Komai baicema Moos'ab ɗinba ya fito a motar ya nufi cikin zauren maigari inda su Baffah suke tattaunawa da Baba akan abinda suka sani game da ƙaddarar data afkama Zinneerah da har yau basusan mafarintaba. Waje ya samu ya zauna yana ƙoƙarin ɓoye ɓacin rai da takaicin da mutumin can ya cusa masa. Cikin girmamawa ya sake gaida su Baba dan yanzu dai a matsayin suruki yake. Sosai baba yaji daɗin wannan girmamawa. yakumaji a ransa AK ya kwanta masa, yana taya ƴarsa murna dajin insha ALLAH ta samu mijin marainiya. A nutse baba ya sake maimaita masa bayanin da yayma su Baffah game da Zinneerah, sannan a ƙarshe ya roƙesa alfarmar dawowar Zinneerah danya domin shirya mata biki nanda wata ɗaya. Ɗan murmushi AK yayi kansa a sunkuye yace, “Baba karka damu, duk yanda kukaso muyi mu masu biyayyane a gareku, sai dai kayi haƙuri a yanzu bata ƙasar tana can London, insha ALLAH nan da sati biyu zata dawo”. Cikin ɗan waro ido Kawu Rabilu yace, “Landan kuma? Ita Zinni ɗin?”. Sosai yanda Kawu Rabilu yayi ya basu Saifudden dariya. duk sukai ƙasa dakai suna gumtse bakuna. Baffah ne ya amsama kawu Rabilu da cewar, “Eh suna can gidansa tare da mahaifiyata da taje ganin likita. Amma kamar yanda ya faɗa insha ALLAH nanda sati biyu zasu dawo, kuma insha ALLAH suna dawowa zata dawo nan ɗin itama a ɗauketa kamar kowace ƴa a kaita gidan aurenta”. Jinjina kawuna suka shigayi na gamsuwa. Yayinda bakin Baba da nasu Kawu ya kasa rufuwa. Kasancewar yamma tayi sukai haramar tafiya. Naman zabi da basuciba haka maigari yasa aka saka musu a mota hardasu tsarabar mangwaro, gwaba, kashu da nono da ƙwan zabbi. dan su Baba suma sai gasu da nasu tsarabar harda Gwaggo Laritu da labari ya kaima ta bakin ƴaƴanta. Lokacin da zasu wuce haka jama'a suka zagaye motocinsu anata ɗaga musu hannu. Sosai su Baffah sukaji daɗin wannan karamci, dan haka suka tafi zukatansu fes kowa na ALLAH ya sanya alkairi. ★★★ Tun kafin Baba ya shigo gida labari ya samu su Inna. Zaune ta tashi dangangan kamar ba itace kwance kashirɓan tana kukan ciwo da ɗan nishi ba. Cikin masifa take cema mai kawo labarin, “Kukam dai annamimanci bai muku kaɗan abaki Sahware. In banda shegen munahinci yaushe kikaga wata Zinni da har za'a ɗaurama aure. Dalla hice mani agida kahin nai miki bankaɗa wlhy”. Baki Safare ta taɓe tana faɗin, “To oho ni dai Asabe. Koki yarda ko karki yarda yanzu na wuto ana ɗaura auren Zinni a masallacin juma'a. Banga dalilin da zaisa nazo na hiɗi abinda bashike nanba”. “Kai kedai Sahwar ALLAH ya tsine maki albarka bankaɗaɗɗiyar mata watsatstsiya. Ki hitamin a gida wlhy kona nafka maki shegen duka naga mai ƙwatarki”. Fita Safare tayi tana wata shegiyar dariya. Ana haka kuwa sai ga Tinene ta shigo gidan a guje tana hakki. “Ke kuma lahiya kika shigoma mutane kamar wata korarra?”. Yaya Gajeje ta faɗa dan shigowarta kenan gidan ko zancen Safare batajiba. Cikin hakki Tinene ta dafe kanta dake mata ciwo dan dama sayan paracetamol ta fita yi, tace, “Inafa lahiya Yaya Gajeje. wlhy wani labari najiyo yanzun. ga baba can a babban massallaci an ɗaura auren Zinni da wasu mutane manyan ƴan gayu al-qur'an”. Tsit gidan yayi na wucin gadi, sai da Sa'a tace, “Inna anya kuwa maganarnan bada gaske bane? Bara dai na hita nima na jiyo mana”. Yaya gajeje da sai yanzu taji abinda ke faruwa cike da zumuɗi tace, “Jeki jeki maza Sa'a. Kai ALLAH ya tabbatar da wannan zance da nayi hwarin ciki mara misali wlhy”. Amaryar Baba da duk ke saurarensu tun ɗazun bata tsoma bakiba ta kalli Yaya Gajeje da cewa, “Wacece wai ita Zinni ɗin?”. Kai tsaye Yaya Gajeje dake murmushi tace, “Ƙanwarmuce itama mama........” A fusace Inna ta zaburo tana watsama Yaya Gajeje harara, “Ƙanwarku a gidan ubanwa. Gajeje ki kiyayeni. Ke kuma munahika da kike tambaya bara a faɗa miki, itana ƴar kishiyace da zaman gidan nan ya gagareta kamar yanda kema zai gagareki. Dan wlhy na ɗau alwashin yanda na watseta kema saina watseki a gidan nan dama garin nan baki ɗaya”. Murmushi amarya tayi tana ɗauke kanta batare datacema Inna komai ba. Hakan kuwa ba ƙaramin harzuƙa zuciyar Inna yayiba. Ta miƙe dingangan kamar ba ita ke ciwo ba tahau zazzaga bala'i tana zagin amarya da mmn sadiq da Zinneerah. A wannan bala'in baba ya shigo shi dasu kawu da yara ɗauke da kayan sweets dasu biscuits da huhunan goro cikin gidan. Suna shigowa Gwaggo Laritu ma na shigowa......... ★★★★ A ɓangaren su Baffah kam tunda suka bar Danya kowa ke tattauna karamcin da akai musu da abokin tafiyarsa. Motar su AK ce kawai ta kasance shiru dan tunda suka tafi ya jingina kansa da kujera ya lumshe idanu yana tariyo maganar mutumin nan ma ɗazu daki-daki cikin ransa. Lokaci-lokaci Dr Mahmud kan kallesa yayi murmushi. Sai da suka kusa shiga cikin kano ne ya ɗan sake dubansa da tsokana, “Haba ango duk daɗine ya saka zama kurman ƙarfi da yaji?”. Shiru AK bai motsaba, sai da ya mula dan kansa ya ɗan buɗe ido ya harari Dr Mahmud ɗin, cikin rashin sakewarsa yace, “Dama haka kake da sa ido?”. Dariya sosai ta kama Dr Mahmud har yana dukan sitiyari. Hakan ya saka AK ɗan sakin murmushi ya maida kansa ya sake kwantarwa da lumshe idanu. daga nan bai ƙara tankawa Dr Mahmud ɗinba daya cigaba da tsokanarsa har suka isa gida. Sun iso suka iske hajiya Bilkisu da suke kira

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182