Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 171

Chapter 171

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

zuwa duba Inna kafin a shiga hidimar bikin amma AK ya hana, acewarsa ta bari a gama biki sai suje dan akwai maganar Dr Mahmud ma da Sa'a a ƙasa. Kamar yanda ya umarceta da haƙurin haka ta haƙura aka shiga shagalin bikin su Abidah da aka shiryama bidi'oi kala-kala, danma AK ya zaftare wasu a ciki yanata faɗa. Ranar ɗaurin aure a bazata sai ga sunan Khalipha a cikin anguna. An zarga masa igiya uku da ɗiyar Uncle Ahmad Raheenat (Noor). Kowa kam yayi farin ciki da wannan haɗi musamman ma Uncle Ahmad. Shima dai ango da gaske yanaso dan ƙiri-ƙiri ya nuna farin cikinsa. Abin sauƙin ma shima yanada gidansa dama da yake gini, ƴan abubuwane kawai suka rage a ƙarasa dan haka aka hau sauran aiki babuji babu gani. Matar Uncle Ahmad tayi baƙin cikin wannan haɗi itakam, sai dai babu yanda zatai dole ta haƙura. Dan dama taƙi sakin jiki da matan gidan sam. Suko da yake ba kanwar lasa bane duk sai suka watsar da ita suma suka cigaba da sabgogin gabansu. A bikin nan dauriya kawai Zinneerah keyi dan batajin daɗin jikinta, hayaniyarma sam bataso, shiyyasa lokuta da dama zaka sameta can gefe a killace. Hakan sai yayma AK daɗi dan bata halarci bidi'a ko daya ba da akai garama kamu da akayi anan cikin gidan. Ana saka kiɗa kuwa sai da tabar gidan saboda ciwon kai mai tsanani. Can gidansu ta koma tai kwanciyarta ta hutama ranta. Ansha shagalin biki harna kwanaki uku aka miƙa amare ɗakinsu. Adilah lagos, Safiyya Abuja. Sauran kuma Ni'ima da Abidah duk anan kano ne, sai Noor da aka bari sai nan da kwanaki uku an kammala aikin gidan Khalipha. (To amare da angwaye ALLAH ya sanya albarka ya kawo ƴan dugwi-dugwi iyalan baba). Washe garin da aka shashshare daga bikin nan kuma aka kai kuɗin auren Sa'a danya. Inda baƙi suka sami tarba ta mutunci da girmamawa. Inna ga dama ta samu amma babu halin damawa, sai hawayen zuci takeyi. Dan tuni aka maidota gida. Sai dai a duk sanda ta kalli Tinene da tsohon ciki ranar sai ciwonta ya rikice. Hakan yasa suka yanke shawarar maida Tinene gidan Gwaggo laritu harta haihu, dan an ajiye magana randa ta haihu za'a ɗaura mata aure damai cikin tunda ya amsa nasane. Daga kai kuɗi baba yace shikam dai baimaga wani abun jeka ka dawo ba a ɗaura aure kawai a huta. Zuwa wani satin ta tare ɗakinta taje tai haƙuri tamkar kowa. Hakan yama Dr Mahmud daɗi, hakama su Baffah da suka kai kuɗin. Nanko take aka zarge igiya uku tsakanin Sa'adatu Sulaiman Danya da Dr Mahmud Dawood. Zokaga baki wajen ango. Aiko AK ya dinga masa sherin kurame yana ramawa shima kamar yanda yay masa. Dan bazai fito kai tsaye yay maganaba sai dai yayi a fisge ya tsuke baki cikin basarwa tamkar bashine yayi ba. Cike da farin ciki suka dawo kano da wannan labari, Zinneerah kam tafi kowa murnar wannan al'amari dan har kukan daɗi tayi. Cikin amincin ALLAH sati na zagayowa akai tariyar Sa'a. sai dai Zinneerah bataje Danya ba dan batajin daɗin jikinta kam, Khalipha ma tasa amaryar ta tare a nasa gida da aka kammala. Yanzu kam sai dai mu cigaba dabin kowa da fatan alkairi. Tun bayan tariyar Sa'a komai ya sake lafawa, Khalipha ya koma London shi kaɗai domin karasa karatunsa. Zinneerah ma cikin ƙarfin hali AK ya sata zana exam na November/December. Tasha wahala saboda laulayin dake damunta, amma babu laifi tayi ƙoƙari Alhmdllh, sai fata da addu'ar fitowar ƙyaƙyƙyawan result. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Zinneerah na rainon cikinta dake ƙara fitowa yana wahal da ita, duk ta rame sai haske data ƙara kam masha ALLAH. Yanda wahalar tai mata yawa ne ga aikin gida ga little ya fara makaranta, dan yanzu yafi zama anan fiye da ko ina, yawonsa sai weekend, ga gida shiru ita kaɗai yasa Hajiya iya cemasa ya maidota nan gidan sai ta haihu. Babu wani ɓoye-ɓoye ya ɓata ransa. Dan shi dai yafison su cigaba da lallaɓawa a hakan har ALLAH ya sauketa lafiya. Tunda dai bawai kwance take rijif ba. Aikin gida da lalurarsa girki da sauransu duk tanayi. Fitace kawai bata cika sonyi ba dan wahala take sha sosai koda kuwa zuwa gidan su Granny ne kawai tayi ko gidan mmn sadiq. Shiyyasama ta tattara kowanne yawo ta ajiye. “Ikon ALLAH, wai ka cika baki da iska! Bazaka maidotan bane komi kake nufi moddibo?”. Shiru yay mata kamar bazai tanka ba, sai da yaja wasu sakanni ya dubeta yana ajiye wayar hannunsa. “Granny ki fahimta mana dan ALLAH, taya yarinya na gidan mijinta ace ta taso ta baro. Wazai kula damu ni da Abdul-Mutallab to?”. “Owoo, sai ta zauna zaman kula da ku ita kuma ta kashe kanta. Kana ganin yanda duk jikinta ya koma ko abincin kirki bataci sai yame-yame”. “Granny duk nasan da waɗanan matsalolin kuma suna damuna wlhy nima, ina kuma yin iya bakin ƙoƙarina na ganin na bata kulawa nima, kuma Alhmdllh jikin natama ya fara sauƙi. Kawai dai idan kin yarda a samo wata ta zauna da ita ni ko nawane zan biya. Kokuma ke ki koma can dan ALLAH ”. “Wa? Kama kanka. Kawai sai naje ƙososo na zauna muku a gida raba kanka malam”. Murmushi yayi a ransa yana faɗin, ‘Ai wlhy ke zan lallaɓa kije madam, nasan maganinki ai’. A fili kam sai yay mata shiru, daga ƙarshe ma ya miƙe yana faɗin, “Bara naje na ɗauka Abdul-Mutallab a makaranta”. “ALLAH ya kiyaye ka gaishesu”. Zinneerah na falon farko na sashenta a kwance cikin kujera barci ya ɗan fara figarta daga charting dasu Meenal suka shigo. Kamar yanda Little ya saba duk da kuwa yanzu ya ƙara girma da wayo ga shegen miskilanci kamar sunyi kaki sun ajiye ya nufeta da gudu. Yana ƙoƙarin faɗa mata a jiki AK ya ɗagashi sama dan yanayinta ya nuna masa batajin daɗin jikin. Kuma lafiya lau ya fita ya barta. Itama ajiyar zuciya ta sauke ganin ya hana little ɗin faɗa mata a jiki. Ta yunƙura ta tashi zaune tana musu sannu da zuwa. Amsawa yay idonsa a kanta yana kaiwa zaune kusa da ita little a jikinsa. “Jikin ne kuma?”. Fuska Zinneerah taɗan yamutse tana kamo hannun little ɗin. “Kawai dai banajin ƙarfi ne amma babu inda kemin ciwo, garama tashin zuciya daketa damuna tun cin kifin nan na jiya da naci”. Tausayintane ya sake kamashi, musamman daya tuna yanda taita damunsa da maganar kifin. harma ya dawo gida jiya da nufin bazai sake fitaba ta takura sai da ya fita kusan goma na dare ya nemo mata kifin, gashi kuma taci ta kasa zaman lafiya. “Sannu ALLAH yay miki albarka ya saukeki lafiya. Bara na taɓa Mahmud naji kozaki iya shan wani abu dazai baki nutsuwa”. “Yayanmu kama barshi zai bari dan kansa. Dan nayi waya da Yaya gajeje tace na samu ɗan kanwa kaɗan nasa a ruwa na sha zai faɗa min”. Kafin yace wani abu little da yay kamar ba saurarensu yakeba yace, “Aunty sorry, idan kika haifa mana babynmu zan kaiki makka”. Dariya zancen nasa ya basu, dan haka suka murmusa AK na shafa kansa. “ALLAH ya tabbatar ɗan albarka.

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182